← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 41

Sashe 28

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ri o, gudun kada ta fa i itama sai ta rike kafa unsa gam. Ganin yanda ya ke jifanta da mayataccen kallo sai ta ru e, kirjinta bugu ba autawa, ta hau kokarin zamewa amman karfin ba aya ba. "Ka yi hakuri don..." "Shhh." Ya dakatar da ita ta hanyar rufe bakin da yatsansa. "Ki ka ce me? Ban iya komai ba ko?" Ta hau girgiza kai, babu inda ba ya ka awa a gangar jikinta. "Ka yi hakuri." "Noo, ba zan iya ba. Raini ne." Bai ba ta damar magana ba ya tallafo ha anta gami da ha a bakunansu wuri guda. Sa onni ne da ba za ta iya auka ba, sun fi karfin sakonnin da Ma'aruf ya aika ga Bintunsa, sun wuce wanda ta sani tsakanin Tasleem da Haris in ta. Ba zai ha u da na Faruk da Umminsa ba. Daban ta ke jinsa, a duniya ta daban da ba ta ta a shigarta ba. Ta ara narkewa a jikinsa inda ya bata kyakkyawar matsa kamar zai ha esu su zama abu guda. "Assignment, sabon karatu game da Khalid." Cak ta ji ya sake ta sai dai bai janye jiki ba, ita in ma sai a sannan ta bu e lumsassun idanunta, a hankali ta dawo duniyar Laila Kurfi da Khalid Kurfi. Da sauri ta janye jikinta, ya na dubanta sadda ya sa hannu ya au coat insa saman bookshelf inda ya an sa ala. A guje ta fice zuwa angarenta, tana shiga ta murza key. A angarensa kuwa, murmushi ya yi mai bayyana asirtaccen kyawunsa. Ya shafi sumar kansa, koya mata hankali ya yi amman kamar zuciyarsa ya horar. Ya kasa fahimtar yanayinsa, hakura ya yi da tunanin kawai ya fice zuwa akinsa. *** Ta yi kukan ba in ciki har ta ji ta oshi ta ha ura ta share. Na aya al awarinsa ga Hajiya ke sosa ranta, na biyu kuwa sanin da ta yi ba soyayya tsakaninsu, ba ya sonta amman ya ha a fatarsu wuri guda. Na uku kuwa kunyar kanta ta ke ji na biye mishi da ta yi har ta kasa watar kanta. amshin turarukansa ya addabi ofofin hancinta, ta ago da sauri tana aga wuya, babu shi a in. Sai ta fahimci amshin daga jikinta ne, ba wai tufafin ka ai ba, aa har ma da fatarta. Da saurinta kuwa ta mi e ta cire kayan ta fa a wanka. Sai da ta yi sa i uku kafin ta fito aure da tawul. Kallon kanta ta yi gaban madubi, hotunan lamarin sun kasa goguwa a birnin zuciyarta. Ta yarda 100% cewar shi expert ne a wannan angaren. Ta yi imanin da gaske ya iya tafiyar da mace. A hankali ta kai hannu gefen wuyanta ta shafa, ta tuna sadda fatar bakinsa ta ha u da wurin yana sarrafawa tamkar ya samu alawa. Da sauri ta saki wuyan ta rufe fuska da tafukan hannayenta, ita a lallai kunya da takaici ke awainiya da ita. Tun daga wannan rana su ka shiga wasan uya, ita kunya shima kunya. Bai san me ya kai shi ga hakan ba, ya dai san tabbas girma ya fa Washegari da yamma ya kira wayarta ya bata umarnin shiryawa ya kai ta gida domin a ranar zai wuce wuraren goman dare. Jiki a sanyaye ta ke ha a kayanta, bayan ta kammala ta yaye bedsheet ta ha a a wanki. Ta rufe duk wani abu da ta san zai yi ura, ha ka nan falo da angarensa. Ba inda ba ta gyara ba. Bayan ta kammala ta shirya cikin leshi kalar peach inkin riga da siket wanda ya fiddo surarta. Ta tsinci kanta da yin kwalliya sosai, a arshe ta yafa mayafinta arami s y blue da takalminta shima hakan sai aramar jakarta. "To, ka yi sauri fa mu ha u a can babban gida." Muryarsa ta tsinta ya na amsa waya daga bayanta, ta juyo tana dubansa hannunta ri e da trolley in ta. Sama da asa ya ke dubanta ya na ci gaba da amsa wayarsa. Kallon ya isheta ta kauda kai gami da aure fuska ka an. Ya araso bayan kamma a wayar. "Inyee, ke kwalliya ma ki ka yi wato?" Da mamakin furucinsa ta ago ta dubeshi. Murmushi ya ke mata. Ta rasa fa inda Yayan nata ya dosa, ta kasa gane ta amaiman abinda ke asan ransa. Za ta sunkuyar da kai ya tallafi fuskar. A hankali ya ciro handkerchief insa ya hau share mata janbakin da ta sanya. Lumshe idanu ta yi don ba za ta juri kallon da ya ke jifanta da shi ba da lumsassun idanunsa. Ba kuma ta yi aune ba ta ji harshensa na zagaye saman le anta, ta bu e ido da sauri ta ja baya. Ya dubeta yana murmushi a lokaci guda ya shafi sumarsa. "Ba fa arfina ki ke fi ba Malama, bar ganin wai ina kyaleki kina ture ni, kuma ma gulma ce kawai ke damunki amman kina so." Ta aure fuska. "Ni ka san ina girmama al awari musamman ma na uwa." Maganar ta dake shi, tana son ta dunga yi mishi tuni da wannan al awarin da ya furta ya aukarwa Hajiya ba da sanin tana saurare ba. Ya kasa tankawa kawai ya juya. "Ki taho mu je." Ta bi bayansa da kallo cikin jinjina yanayin sanyin da ya yi. Sai kuma ta yi kwafa gami da ta e baki. Ai gwara ya ji yanda ta ke ji duk sadda ta tuna da al awarin da ya auka. A mota ma babu mai kula an uwansa har suka gangara layin estate in nasu. Sai a san nan ya yi magana a kausashe. "Ina mai garga inki da ki kiyaye furtawa ko ma waye maganar da ke tsakanina da Hajiyata tun da ba ki san dalilina ba. Idan ki ka yarda wani ya ji toh wallahi ni mai ar mataki ne. Ki kula." 'Ikon Allah.' Ta furta a asan ranta, wannan fa shi ne a dake ka, a kuma hana ka kokawa. "Ko ba ki ji ba?" Ya furta ya na dubanta ta cikin ba in gilashin da ya sanya tun shigowarta motar. A an tsorace ta gya a kai. Daga nan ba wanda ya ara magana sai muryar Burna Boy ke tashi a rediyon cikin wa arsa ta On the low. Ranta gaba aya a untace, sai dai kuma ganinta a ofar gidansu sai ta ji aso 50% na damuwarta ta tafi a take. Horn ya yi maigadi ya bu e ya shiga ciki. Shigarsa ya ji kansa ya sara da arfi har sai da ya taka burki gami da ri e kan, ita kuwa ji ta yi gabanta ya yi mummunan fa uwa ta hau ambaton Allah. Bayan sun yi fakin ne, Aliyu da ke a ofar gidan tare da abokansa ya taso ya nufo Yayansa. Ta fito, ga mamakinta Aliyu ya ce. "Matar Yaya sannu da zuwa." Ta dube shi, har da wani an russuna kafa a ya na shafar sumar kansa. Ta kasa cewa uffan, za ta au akwatinta Khalid ya magantu. "No, bar shi ya auka. Sashin Hajiya za ka kai mata." A razane ta dubeshi gabanta na bugu da sauri-sauri. Bayan wucewar Aliyu ta ce. "Ban fa gane ba, ba sashin Hajja ba?" Ya girgiza kai fuskar har lokacin ba alamar wargi. "No, sashin mahaifiyata na ce. Ina da dalili, ina son ku sha u da juna." Kwalla ta cika idanun Kurfi, rai a ace ta shiga girgiza kai. "Ba zan ta a zama angaren Hajiya ba!" Ya yi shiru yana dubanta. "Wallahi ba zan zauna ba! Ai rashin uwa ba ya na nufin na zama sai yanda akai da ni bane! Ba zan zauna ba! Na gwammace na koma angaren Abbana na zauna." Sai ta fashe da kuka, ya ja tsaki. "Ko na jini za ki yi, idan har ni keda iko da ke dole ki bi tsarina, idan kuwa ba haka ba sai dai ki koma can gidanki ki zauna. Idiot!" Daga haka ya fice ya bar ta nan tsaye, tana kukan ta nufi angarensu. Babu kowa a sashin Mami don haka ta arasa ga falon Abban. Ta iskeshi zaune ya na ha a takardun da ba ta san ko na miye ba. "Abbana." Jin haka sai ya ago kai yana dubanta a hankali, ba tare da ta lura da yanayinsa ba ta fa a jikinsa sai kuka. "Abbana ka yiwa Yaya Khalid magana, ni ba zan zauna a angaren Hajiyarsa ba. Abbana ka fi kowa sanin yanda ta tsane ni." Ture ta ya yi, ya aure fuska. "Wace irin maganar banza ki ke yi Laila? Hajiya Sa'adatu ba matsayin uwa ta ke a wajenki ba? Kul! Kar na ara jin wannan zancen. Maza tashi ki je ku gaisa kar ta nemeki." Sakato ta yi tana dubansa, duba na tsantsar mamaki da firgici a lokaci guda, sai a san nan ta ke are mishi kallo. Ya sauya kafataninsa, ya yi wata rama hakanan farar fatarsa ta yi duhu ka an. Ga furfura da ta cika kansa. Ta kasa fahimtar komai, ta kasa gaskata abinda ke shiga kunnuwanta. Hakan yasa ta mi e kamar wata doluwa gami da matsowa ta dafa kafa arsa a sanyaye. "Abbana, ni ce fa Laila." Ya dubeta, a wayar idanunsa ta hangi kauna matsananciya sai dai maimakon ta ji ya ba ta amsa cikin kulawa sai ta ji ya fisge hannunta a fusace ya ce. "Yau na sanki ne Laila? Ko kin manta ni ne ubanki na tunasar da ke? Idan har na isa da ke to ki tattara ki fice daga angaren nan don ni yanzu da ki ka ganni shirye-shiryen aure nake ba kuma zai yiwu ace daga aurena ki zauna tare da Amaryata ba. Idan kuwa ban isa da ke ba toh kar ki aikata abinda na sanya ki." "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Ta furta da arfi, sai a san nan ta lura da takardun da ya ke ha awa, iv card ne na aurin aurensa. Ba wannan ne matsalarta ba, damuwarta bai wuce na sauyin da ta gani daga mutane biyu ba. Yaya Khalid da Abbanta. Ta ya ya? Ya akai su ka sauya lokaci guda? Ta ci gaba da rera kuka, a guje
Chapter 28 · 0% Book details