← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 41

Sashe 35

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sallamar ta shiga kirjinta na dukan tara-tara don ba ta san kallon da zai mata ba. Fuskarsa dai bata nuna komai ba hakan yasa ba ta gane yanayinsa ba, ta dur usa ta gaishe shi ya amsa. "Abba.." Ya dakatar da ita. "Bari nayi sallah, yanzu na tashi." Ta dubeshi a tsorace don tuni ya kalli gabas, salati kawai ta yi a asan ranta. Abbanta ne har war haka bai yi sallar Asubahi ba? Lallai kam ibadarsa ga dukkan alamu ba kamar da ba. Koda ya idar tana gani ko cikakkiyar addu'a bai yi ba ya juyo gareta. Ganin bai ce komai ba ta fahimci ya bata dama ne ta yi magana. a hannu ta yi ta ajiye mishi robar ruwan maganin a kusa da shi. "Abbana ruwa ne na zamzam da na yi amfani da shi wajen addu'a don neman kariya daga sharrin masu sharri. Don Allah Abbana ka dunga sha, ba don ina zargin komai ba sai domin nema maka kariyar Allah daga sharri." Ya yi shiru yana dubanta, a can cikin zuciyarsa akwai wani tausayi da auna da ke mamayar zuciyar sai dai kuma ya rasa me ke danne hakan yana wassafa mishi kamar tsana kamar kuma haushi haushinta. "Shi ke nan, zan duba yiwuwar shan. Tashi ki tafi." Ta ji fa uwar gaba, sai dai kuma ba ta son ta fiye naci ya i sha in gaba aya. Don haka ta ce. "To Abbana, Allah Ya karemin kai, Ya ara bu amaka daga arzikinka duniya da lahira." Daga haka ta mike tana lura da yanda ya an saki fuska ka an alamar dai ya ji da in addu'ar, sai ya bata tausayi sadda ta sa afa ta fice daga akin. Ta ci sa'a har a sannan su Hajiya basu farka ba sai dai ta ci karo da Daddy wanda ya fito sanye da jallabiya zai fita waje. Ya tsaya yans dubanta, shi kansa ya na jin kamar ya tausaya a gefe kuwa ya na jin kamar tsana gareta. Ta dur usa da sauri ta gaishe shi, ya amsa ciki-ciki sannan ya fice. Tana shiga akinsu ta zube jikin Munira wacce ke zaune saman darduma ta yi tagumi da carbi a hannunta, kuka kawai ta sanya. Munira ta shiga hawaye, babu wanda ya tambayi dalilin kukan wani a cikinsu haka suka sha kukan suka ha ura suka goge fuska. arfe biyun rana a sannan sun kammala aiki, suna zaune a baranda can nesa inda Hajiya ba lallai ta hangosu ba, Munira ke yiwa Kurfi kitson kalba a kanta. Su na hirar Tasleem da an uwan Maminta. A haka amshi ya ziyarci ofofin hancinsu. Suka kai duba ga inda amshin ke fitowa, mamaki arara ya bayyana saman fuskokinsu a lokaci guda. Hafsat ce ta yi wani mugun cika da iba, ga kayan kumatu ta ajiye. Ta cakare cikin dakakkiyar shadda koriya sharr, fatarnan ta ara murjewa ta yi kyau. Wani uban gilas da ta maka ne ya kusan sa Kurfi dariya don a ganinta sam bai dace da tsarin kwalliyar ba. Kauda kai ta yi daga kallonta sa'ilin da Munira ke fa in oyoyo. Hafsat ta araso tana wani murmushi na mugunta. Gilashin ta cire tana duban Munira. "Munis, ya kike? Ke ko eyarki ban ta a gani a gidana ba ko?" Munira ta an yi dariya don ita kam ba su da case da Hafsat har ma da Rukayya don kuwa ita in ta kowa ce asalima ba ta tare musu komai ba, abokiyar ishin ta su dama Kurfi ce. "Allah Ya baki hakuri Sister, na so zuwa sai dai Allah ne bai yi ba." Hafsat ta yamutse fuska don ba ta wani damu da yanda ta ganta ba a rame. Na Kurfi ne dai ya fi sanya ta nisha "Na miki uzuri ai, kin san ma da yake nima tafiya zamu yi Honeymoon da Sweet Huzaifa, shi ne ma dalilin zuwana yiwa su Baba sallama." Munira ta an kama baki. "Ah, lallai na tayaki murna wallahi." Sai a sannan Kurfi ta gaidata a matsayinta na wacce ke mata kallon ta girme mata. Ta amsa kuwa tana dariyar mugunta a asan ranta. "Ya Mijinki Yaya Khalid? Kuna waya? Koda dai nasan har video call ba kwa rasa yi. Lailla ta Majnun." Ta yi wata ar dariya ta rainin hankali kafin ta dubi Munira. "Kinsan ba abinda ya kai aure da i Munira, musamman ma idan auren ya zamana ba na cushe bane, ke koda na cushen ne ya kasance miji na sonka. Wannan ya fi komai da Munira murmushi kawai ta an yi don ta fahimci magana ta ya a wa Kurfi, hakan bai mata da i ba sam. Kurfi ko kallo bata ishe ta ba, a karan kanta tasan yanzu ta sauya. Wannan zafin zuciyar da rashin aukar wargi duk ta bar shi, Mami ta sha ce mata watarana zai zo da za ta yi sanyi ta tashi daga mai zafi zuwa mai sanyi, gani ta ke duk wasa ne har ta ke darawa, ashe kuwa hakan ne tunda ga zahiri, sai a ya a mata magana ta yi shiru abin ta. Don haka har Hafsat ta fice ba ta bar mamakin kanta ba, da a baya ne sai ta gasa wa Hafsat maganar da za ta jima ta na mata zafi a rai. Munira ce ta katse tunaninta. "Ki yi ha uri Kurfi." Murmushi Kurfi ta yi. "It's ok." Abinda ta fa i kenan kafin ta sanyo wata hirar don kaucewa waccan. A ranar ma sai ga Ru ayya, ita dai gaba aya ta rame ta kuma yi wani sanyi. Koda suka ha u da urfi ta gaisheta, ta amsa fuska a an sake. Daga haka suka rabu lafiya. *** Ranar Lahadi suka samu bakuncin Yaya Hassan da Yaya Hussain tare da matansu. Su kansu sama-sama su kai musu, Anti Rahma da Aisha basu ji da in yanayin da mazajen suka nuna garesu ba. Kurfi ba ta damu sosai ba kasancewar sun yi zuwa hu u bayan zuwanta ba su kula ta, farkon zuwansu ta tarbesu da murna kowannensu ya aure fuska tamau. Ranar ne ta fidda hawaye amman yanzu kam ta san su inma ba a hayyacinsu suke ba. Ta rasa mugun abin da Hajiya ta aiwatar da har ya yi tasiri har haka. Abin ya bar ba ta tsoro tun soma gayawa Allah, yanzun ta fi mamaki. Anti Rahma da Aisha lafiya lau suka sakarmusu fuska. Anan ne Kurfi ta ari wayar Rahma ta kira Adda Maijidda. Nan ta ke jin labarin cewa Hajja ta samu sau i sosai don tana iya magana, da i ya cika zuciyarta. Ta ara ba ta ha uri gami da mata nuni akan su ci gaba da addua. Nan Kurfi ke labarta mata maganin karya sihirin da su ke yi kuma su Abban na sha. "Alhamdulillah ata, kin burgeni sosai. Allah Yay miki albarka. In sha Allah mu ne da nasara." Murmushi ta yi jin abinda ta ce. Daga nan ta ce a ha a ta da Mu'azzam ta ji muryarsa. Ya kuwa shiga ifice ificensa a kan wayar tana dariyar farin ciki. Yaushe rabon da ta ji muryar aninta. Anan Adda Maijidda ke sanar mata cewa Zeenat na auke da juna biyu. Wannan abu ya yi mata da i. Babu hanyar ha uwa da Zeenat saboda tana tare da Zahraddeen a Abuja yanzun wajen aikinsa. Koda da damar ma, shigowarta gidan zai yi wuya muddin Hajiya na nan. Bayan sun yi sallama ta mika wayar ga Anti Rahma, girgiza kai Rahma ta yi tana murmushin tausayinta. Ta mike tsaye. "Ki kira duk wanda kike so Laila, akwai isassu ku in da za su isheki, bari na koma can kafin Hajiya ta riske ni." Godiya sosai Kurfi ta yi, a take ta danna kira ga Zeenat, jin muryar Kurfi sai kuka, Kurfi ta dake tana murmushi. "Hey, kar fa ki sa Yaya Zahraddeen ya au mataki a kaina na saka matarsa kuka alhalin tana auke da baby." Zeenat ta yi ar dariya. "Uhum, Kurfi na yi kewarki, na tausayawa halin da ki ke ciki. Wallahi Kurfi sau uku ina zuwa ban samu shiga ba, ranar farko Hajiya mukai karo da ita ta dawo daga unguwa za ta shiga gidan, ga mamakina ta ba wani buzu sabon maigadin da ta sanya umarnin kada ya bari na shigo. To haka na juya, rana ta biyu da Noor ina muka zo nan ma ya i, na uku na dawo ni aya ya so ya min wula anci. Daga ranar Noor ya ce na hakura da zuwan kawai. Mu ci gaba da addu'a. Ga shi ba waya hannunki, kullum kina raina wallahi. Kwanaki Noor ya ke cemin Yaya Khalid ko sunanki aka ambata kashe wayar ya ke yi bai san dalili ba. To haka ma Dawud ya ce mana." Kurfi ta danne abinda ta ke ji ya na taso mata, ta yi murmushi. "Ba komai Zeenat, komai lokaci ne. Ki bar damuwa, mu godewa Allah. Shi Ya jarabcemu, ko ba komai muna aukar darasin rayuwa." Daga nan ta banzatar da hirar ta hanyar tambayarta lafiyar baby, sai sannan ta yi dariya gami da neman sanin inda ta ji. Anan ta ke fa amata sun gaisa da Adda. Ba su wani jima su na hira ba sukai sallama. Ta kira Tasleem wacce lambarta ke zane a kwakwalwarta. Tana cewa ita ce Kurfi, nan ma kukan Tasleem ta sanya ta na tsinewa Hajiya gami da fa in karshenta ba zai kyau ba. Kurfi ba ta ce komai ba, daurewa ta ke sosai don ba ta kaunar kukan ba ta ganin amfaninsa. Ba su kai ga gaisawa ba Anti Rumaisa ta kar i wayar. Suka shiga hira sosai da Kurfin ta yi mata nasiha da kuma yi mata albishir cewa su kansu su na addu'a sosai kuma su na ji a jikinsu komai zai wuce. Ta fa amata an kawo ku in sanya ranar Tasleem amman ta rantse ba za ta yi aure ba sai Kurfin na tare da ita. Anan ne hawayen Kurfi suka kwaranya tsabar tausayin kanta da Tasleen in, sha uwarsu ba ta wasa ba ce. Daga haka ta ba Tasleem wayar suka shiga hira. Dakyar su kai sallama daidai sadda Munira ta shigo akin da sallama. Kurfi na murmushi ta
Chapter 35 · 0% Book details