← Book details Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 41

Sashe 1

Mukaddari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal Default Paragraph Font Table Normal No List "Kurfi! Kurfi!!" Ihun da sauran dalibai ke yi kenan suna k'ara fasawa 'yar budurwar kai yayinda ta ke kokarin jefa kwallon a ragar (basketball). Hatta da su kansu malaman hankalinsu ya karkata kaf a wajenta, kwarewarta a iya wasan har mamaki yake ba da yawa daga malamai. A sanadin hakan tayi suna, ta zama cikin manyan daliban da ake ji da su. Ba su yi aune ba, suka ga ta buga wani uban tsalle ta jefa cikin ragar bayan kaucewa abokan wasanta da dama. Hakan ya yi daidai da busa wusir da referee din ya yi. Zo ka ji ihu daga dalibai, wadanda ke tare da dayan team din kuwa, suka yi jugum rai ba dadi, yayinda abokan wasan Kurfi suka rukunkumeta suna murna har sai da suka kai ta k'asa. Sai da aka yi dagaske kafin su saketa, ta mike tana kakka6e jikinta yayinda take fidda numfashi a wahalce. Nan kuwa aka basu kofi, mai makarantar kansa sai da ya ba Kurfi kyauta ta musamman bisa wannan kokari da tayi, ko babu komai ba'a zo wasa makarantarsu an cinyesu ba. Da kunyar da zasu ji ba kad'an ba. Karfe hudu daidai aka tashi daga makarantar, tuni ta sauya kaya zuwa na makaranta, ash ne wandon sai farin riga mai tsaga a gefe-gefe sannan karamin hijab wanda ko kirjin bai gama rufewa ba. 'Yar uwarta Zeenat Kurfi ta dubeta da dariya. "Da kin bari kin je gida haka da kayan." Kurfi ta zaro ido. "Ni shegiya ko? Tab, ban shirya amsa tambayoyin iyayennan namu ba, wai ni, Allah ma kada Ya ba waninsu ikon ganina da wannan 6ingilallen wandon na basketball. Don ta Abbana banda matsala, amman Baba Mudassir da Yaya Khalid? Hum um!" Suka dara. "Da ba ke kadai ba, har ni gidanmu za'a ci wallahi." Kurfi ta ta6e baki sadda take kokarin rufe zip din jakarta bayan kammala sanya ledar kayan a ciki. "Atoh, duka ne kadai Baba Mudassir basu yi mana ba akan wasan nan, kema kin sani." Murmushi Zeenat tayi daga haka suka rankaya zuwa filin makaranta don jiran a zo daukarsu. Suna fitowa kuwa ga mamakinsu, Bala direban Abban suka gani. Suka karasa, Kurfi ce ta soma tambaya. "Tare da Abba kuke?" Ya amsa a sake. "Aa, yanzu dai zamu biya a daukoshi." Bayan sun shiga motar, Zeenat ta kara jefamasa tambaya. "Toh ina Yakubu?" "Motarsa ce ta samu matsala, yana tare da su Jawad. Amman yanzu ya barta hannun mai gyara, sun tafi a motar haya shi ne Alhaji ya ce na zo na taho da ku kawai." Daga haka suka ja bakinsu suka yi shiru. Kurfi ta kunna wayarta ta sanya earpiece tana sauraron wak'a yayinda Zeenat ta shagala wurin kallon titi. Mintoci kadan ya kawosu Bompai inda anan kamfanin iyayennasu yake. Aka budemusu gate da sauri ganin motar, suka kutsa zuwa ciki. Bayan ya faka suka fito suka nufi ciki. Duk inda suka ketare kallo ake binsu da shi, wasu har gaishesu suke ganin kama muraran da Zuri'ar Kurfi. Ko ba'a fadamusu ba sun gane jinin Ogansu ne. Kurfi taku take tamkar bata so, yayinda tuni Zeenat ta yi gaba har ta kai kofar da zata sadata da ofishin Abban. "Excuse me Ma." Ta ji muryar secretary dinsa, ta juya gareta. Suka gaisa a mutunce, nan take sanar da ita cewa Oga na meeting room, Zeenat ta ce ba matsala zasu jira. Daga nan ta bude ta shige, ita kuwa uwar karambanin jin hakan yasa ta dubi matar ta tambayeta inda Meeting Room din yake. Ba musu ta nunamata ta kara da cewar tayi hakuri ba zata samu shiga ba sai sun kammala sun fito. Hararar Kurfi ta watsamata gami da jan guntun tsaki, bata kara sauraronta ba tayi gaba, Zeenat wacce ta shige, sai gatanan ta fito a dan tsorace ta shiga kwalamata kira amman ko juyowa bata yi ba ballantana ta ji za ta fasa zuwan. Kwankwasa kofar ta soma kokarin yi ta ji an rike hannun, ta juya da niyyar ihu jin irin azabar rik'on sai dai tuni aka sanya hannu aka rufemata bakin. Wanda ta gani yasa ta ji kamar ta saki fitsari a wando. Jikinta ya soma rawa nan take, to wai ma yaushe ya iso garin? A murtuke take fuskar kamar koyaushe, ta kasa cewa komai gareshi banda le66anta da ke rawa. Janta ya shiga yi har suka koma cikin ofishin Abba. Ya rufe ya dubeta a hasale. "Ke wace iriyar marar kunya ce? Don ba ki da mutunci an ce su na meeting amman ba za ki fasa shiga ba? Da ma na barki kin shiga ki fito sannan na 6a66alaki! Stupid kawai! Nemi wuri ki zauna tun ban kai hannu jikinki ba." Kafin ma ya karasa ta d'osana duwawunta a kusa da na Zeenat wacce itama ta yi shiru abinta tana wasa da yatsu. "Dama da waya kike zuwa makarantar? Waye ma ya siyamaki? Bance sai kun gama secondary ba sannan za ku rik'e?" 'Na shiga uku.' Ta furta a zuci. Ya dakamata tsawa. "Tambayarki nake!" A gigice ta dago kai. "Yaya Hassan na tambaya, ka yi hakuri." Ya watsamata harara. "Ok, shi ke dauremaku ku ke abinda kuka ga dama ko? Ke har kinsan ki rok'i abu? Toh ba zan lamunta ba. Bani wayar." A duniya Kurfi na masifar son chatting, watannin da tayi da waya a hannu ta saba har bata kaunar motsawa nan da can idan har ta rik'eta. Amman ya za ta yi? Babu mai ja da bala'in Yayansu Khalid Ta mik'amasa wayar idanunta cike da ruwan hawaye, ji take komai ma ya ce ta ba shi za ta bayar matukar zai barta da wayar. Masoyanta ta tuno, gaskiya za ta yi kewa ba kadan ba, ga wani sabo da tayi kwanannan, Barrister guda ne wanda ke zaune a Kaduna. Yanzu shikenan Khalid ya nesanta ta da su. Tana kallo ya sanya a aljihun wandonsa . Gum kawai tayi amman a cike take, jefi-jefi take dauke ruwan hawaye. Zeenat ta saci kallonta, sai ta bata tausayi, ta san yanda take mutuwar son chatting, yau kam karshenta ya zo tunda ta kuskure har Yaya Khalid ya gani. Shi kam baima san suna yi ba, wayarsa yake hankali kwance, yanda yake bada girma ga mai shi din yasa suka fahimci wani babban ne a wurin aikinsu. Karshe ma sai ya mik'e gaba daya ya kashe wayar bayan gama sauraro. Dubansu ya yi yana mai tattara gira wuri guda. "Idan Abba ya fito ku ce masa na zo amman an kirani na wuce." Daga nan bai saurari toh dinsu ba ya wuce da sassarfa ya bar wurin. Yana fita Kurfi ta ja wawan tsaki. "Allah kuwa ban yafe ba!" Ta furta hade da zubar hawaye, Zeenat abin sai san nan ya bata dariya. Harara Kurfi ta watsamata ta kauda kai. "Jimin baiwar Allah, wai ba ki yafe ba, to ya za ki yi? Kema dai kinsan ganganci ne ki ka yi tun farko da kika nemi a siyamaki waya. Atoh, ki godewa Allah ma da maganar bata kai ga Baba Mudassir ba, Yaya Khalid ma kin ci sa'a da bai 6allaki ba." Kurfi ta turo baki tana kallon inda ya matsemata a hannu. Murzawa ta ke yi tun dazun. "To mene marabar wannan abin da yay min da 6allawar? Ai ya yi niyya, Allah ne bai bashi iko ba. Dama kaf cikin Babban gida ba wanda ya tsana kamar ni." Tana kaiwa nan ta hau shesshekar kuka, Zeenat ta sha jinin jikinta ganin dagaske ran Kurfi ya 6aci. Dama kuma kuka ba wuya yakemata ba, bata kaunar abinda zai ta6a lafiyar jikinta sam. Dakyar ta rarrasheta ta hanyar ban baki da kwa6arta kada Abba ya zo ya risketa domin idan ya ji ita zai ba laifin ma. Aikuwa anan ta samu Kurfin ta mike ta fada toilet ta wanko fuska ta goge da toilet paper san nan ta fito, amman fa kuncin nan yana nan damk'am a zuciyarta. Shikenan dan nishadin da take ji na samarwa makarantarsu nasara a Basketball Competition ta nemeshi ta rasa. Tana kallon Zeenat ta dauro alwala ta yi sallah, abincin ma da Saktariyar ta kawomusu ko kallo bai isheta ba sai Zeenat din ce ta ci abinta tayi nak. Ba jimawa sai ga Abba ya shigo da hanzari, dubansu ya yi cike da kulawa. "Kuyi hakuri 'yanmatana, na barku da jira ko?" Murmushi Zeenat tayi. "Bakomai Abba." Ya kai duba ga Kurfi wacce fuskarta ba walwala, cike da zolaya ya ce. "A'ah, manyan yanmata yau kuma mulkin ne ya motsa?" Ta dan turo bakin, ta dubeshi amman ba ta ce komai ba. Hakan yasa shi duban Zeenat, tun bai tambaya ba Zeenat ta hau bashi labarin Yaya Khalid sai dai ta 6oye batun waya. Abba ya yi murmushi. "Ki ce ke da yayannaku ne, toh ai sai kiyi hakuri tunda nima Abbannaki tsoron yayannaku nake." Wannan yasa ta dariyar da bata shirya ba, suma suka tayata. Mikewa tayi ta karasa ga Abbanta, hannu ta dora saman kafadarsa cikin shagwa6a ta soma nunamasa hannunta da Khalid ya matse. "Kaga fa Abba, ji yanda ya barmin tabo. Allah kuwa Yaya Khalid ya tsaneni, so ya yi ma ya karyamin hannun. Ni sai na fad'awa Daddy." Sai kuka ya hanata karasawa, Abba ya rike hannun ya dawo da ita ta gabansa. "Kayya, bai kyauta ba amma tunda za ki fadawa Daddy abin ya yi zafi. Hannunnan ma zai hanaki abubuwa da yawa yanzu, shikenan ma na fasa siyamaku Laptop din, wannan ai ba hannun da za ki dan..." Tuni ta rufemasa baki tana ihun murna. "Aa Abba, zan iya wallahi, kaga ya daina ciwo ma." Ta fadi tana mai yarfa hannuwan. Dariya sosai Abba ya shiga yi suma su na tayashi. A duniya yana son d'iyartasa kasancewarta ita daya a wajensa. Komai da yake samu bai wuce don ganin ya kyautatamata ba a rayuwa. Haka suka dunguma zuwa gida, Kurfi ta sake sosai babu sauran k'unci a tattare da ita. Gidansu babban estate ne guda na zuri'ar ALHAJI KHALID KHALIL KURFI. Bala yana shiga ya hau kan babban titin ya soma tafiya har sai da ya dangana da gate din gidan Abba. Hon biyu, ana uku Maigadinsu ya
Chapter 1 · 0% Book details