← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 42

Sashe 9

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zakiyya tace, "Wannan murmushi da kike yi ya kamata ki dinga ragewa kisan mijina ne ba alhaji ba." Fiddausi tayi dariya tace, "Dallah ba wannan ba, Abba ya hana ni kula kowa wai sai lokacin idda ta ta cika."
"Kamar ya? Ya manta babu idda akan ki ne?."
"Hmmmm! Bai manta ba wallahi kawai yace wai in aka ga na fara kula maza sai ace ma plan ne mutuwar auren nawa, dan haka ba yanzu ba sai lokaci ya cika in yaso ranar dana gama iddar ma a daure min aure."

Zakiyya tace, "Eh kuma fa da hakan wallahi, za'a yi saurin gano mune muka shirya komai gwara hakan. Allah yasa bakya nuna wata alama da za'a gane hakan." Fiddausi tace, "Ke harda rantsuwa d'azu akan karya, sai jan istigifari nake." Zakiyya tayi dariya tace, "Amma hakan fa shine daidai abinda Abba yace, bara yazo mu fad'a masa yayi hakuri ku cigaba da waya ai naga anci wata d'aya wata biyu ya rage."

Fiddausi tace, "Ke naje gidan Yaya Mama ta fad'a mata wands yazo neman aurena ta tambaye ni haka ne nace eh wallahi rashin Jin dadi karara akan fuskar ta."
"Ke wai Alhaji Bello wasa ne? Ai mai karfin imani ne in yaji zaki aure shi baiyi bak'in ciki ba wallahi." Farin ciki ya cika zuciyar Fiddausi ta koma da baya ta jingina tace, "nima lokacina yazo yanzu."
Ta sake kallon abinda Zakiyya take sha tace, "Wai me kike sha ne?."
"Maganin sanyi ne wallahi, mai shegen kyau ina fada miki."
"Kin kuwa tuna min, akwai wani maganin sanyi da kika bani wallahi dana sha ke baki ga abinda na dinga fitarwa ba kuma iya rana d'aya. Ke kin sanni babu juriyar Shan magani sai na watsar."

Zakiyya tace, "Ke waye ya fada miki kayan Surayya Halin Yau wasa ne? ai wallahi ban tab'a Shan maganin sanyin da nake jin dadin sa nake ji yana min aiki kamar maganin ta ba, kedai ki jira kawai lokacin auren ki yayi wajan ta zamu je tayi miki hadin kaza na musamman dan sai mun rikita wannan bawan Allah wallahi. Zaki yi mamaki in kika yi amfani da kayan ta."

Fiddausi tace, "Gashi na fda miki daga sha sau d'aya naga aikin sa. Ke kika had'a ta da Ameena kenan naji ta tab'a yi min maganar ta."
"Nice wallahi, ga Ameena indai ba kayan ta ba yanzu bata amfani da komai, ke har Yayar ta Bauchi a wajan ta take siyan magani a kai mata har can."

Fiddausi tayi dariya tace, "Tunda dai a kano take kawai Kiyi shiru magana ta wuce zamu je walalhi."

Wayar Fiddausi aka kira hakan ya saka ta kalle ta tace, "gashi nan yazo Ina Jin." Zakiyya tace, "Bara na shigo dashi, baza ki canja kaya ba?."
"Ke rabu dani yazo kawai." Dariya Zakiyya tayi ta fita Jim kad'an suka dawo tare da Alhaji a bayan ta yana amsa waya.

Sai da ya zauna ya gama wayar sannan ya kalli Fiddausi yace, "Fidy lafiya kika min wannan kiran? Kin sana gabana sai fad'uwa yake."
"Barka da rana." Numfashi ya fesar yace, "Barkan ki, ya kika tashi?."
"Alhamdulillah."
"Me yake damun ki?."
"Abba ya dakatar da batun zuwan ka gidan mu yau."
"Innalillahi, Allah yasa ba laifi nayi ba."
"Babu laifin komai Beb, kawai yace ba yanzu ba sai lokaci idda ta ya cika. Kuma in ka lura hakan shine daidai in ba haka ba za'a yi saurin gano komai shiryawa mukayi."

Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "Haka ne gaskiya. Hangen manya a ko yaushe yafi namu, shiyasa hausawa suke cewa abinda babba ya hango yaro ko mai zai taka bazai gani ba. Ai anci wata d'aya ko?". Kai ta daga tace, "Ashe kana sane." Murmushi yayi yace, "baza ki gane yadda nake son na mallake ki ba shiyasa kike ganin bana sane."
Fiddausi ta had'e rai tace, "Ni yanzu ba wannan ba, Ina so a kama min Ibrahim ya kwana a cell dan ya tabbatar matar baban mutum ya Mara har bakına ya fashe."

Nan da nan ya murtuke fuska yace, "Me kike so ayi masa?."
"Nidai kawai ya kwana a cell shine abinda nake so." Waya ya fito da ita Zakiyy tayi sauri taace, "A'a Alhaji a bar zancen Ibrahim a bari a daura auren afi yin komai da gadara. Kaga kai yanzu ba mijin ta bane in ka zama mijin ta kana da ikon yin komai."

Fiddausi ta turo baki gaba tace, "Eh a bari a yi auren, Nidai so nake ayi masa abinda zai sann yanzu ni ba sa'ar bace. Ya tabbatar da yayi kuskuren dukan mace kamata." Alhaji yace, "Kar ki damu wannan kamar anyi an gama ne, ko prison kike so a kai shi wallahi sai yaje koda ya bar Kano kuwa." Tayi murmushi shima haka yace, "Amma zamu dinga had'uwa a nan ko?." Ta d'aga kai alamun eh yayi murmushi yace, "Da sauki." Hira suka yi kadan ba mai tsaho ba saboda wayar da ake tayi masa ne ya saka shi yi musu sallama ya wuce.

#Nana Haleema

Book2
006

Ameenatu sai bayan azahar ta shiga cikin garin Bauchi kafad’ar ta da bayan ta sun yi bala’in gajiya bata tab’a doguwar tafiya kamar wannan ba tunda ya fara tuk'a mota a haka ma ta tsaya a wani gidan abinci taci abinci tayi sallah ta huta. A ‘kofar gidan Yaya tayi parking ta fito ta d’auki Zaytun da itama gajiya ta gama bayyana a tare da ita ta shiga cikin gidan da sallama.

Karamin gıda ne mai fallen dakuna guda uku d'aya nata mai had’e da falo da band’aki d'aya na mai gida d'aya kuma na yara, Jin sallamar ta ya saka Amira lek’owa ganin da gaske fa ita din ce sai ta saki ihuu tace, "Aunty Ameena ce wallahi!." Itama dariya tayi Amira ta karbi Zaytun Yaya ta fito tana fadin, "Wai Ameena ta ce a gidan?."
"Nice Yaya, Wayyo bayana" ta fad'a tana shiga dakin da Yayan ta fito tare da zama akan kujera ta zauna tace, "Hidaya kawo mata ruwa." Wacce ta kira da Hidaya ta fita ya kawo ruwa mai sanyi ta bawa Ameena sai kuwa ta karb’a tana sha tana sauke numfashi.

Ta kalli Amira da Zaytun take hannun ta tace, "Amira ki mata wanka inda ruwan zafi ta gaji sosai." Da to Amira ta amsa ta fita Yaya ta kalli Ameenatu tace, "Sai kawai a ganki babu labari?."
"Hmmm Yaya ni kaina a safiyar nan naji sai nazo gidan nan, da kaina fa na tuk'o nazo baki ji yadda nake jin bayana ba kamar zai b'alle."

Da mamaki da tsoro Yaya ta zaro ido tace, "Ke kadai fa kika ce Aminatou?."
"Wallahi ni kad’ai Yaya, yanzu wanka nake so nayi sai na kwanta." Jin hakan Yaya sai ta mik’e ta shiga bandakin ta da yake cikin d’akin ta dauko bokiti ta fita ta zubo mata ruwa mai zafii ta sirka dana sanyi ta wuce ta kai band'aki ta ajjiye mata sannan ta dawo tace, "Taso Kiyi wankan, dole ai ki gaji, daga Kano zuwa nan ai da nisa.”

Dak’yar ta mik’e ta kalli Amira da ta gama yiwa Zaytun wanka tace, "Dauki key din motata kije ki danna wannan remote din zaki ji tayi ‘kara sai ki bud’e ki d’auko jaka a baya kizo ki saka mata kaya, ki bata abinci" ta fad'a tana shigewa band’akin. Wankan tayi ta fito aka bata doguwar Riga a kayan ta saka ta kwanta a gadon Yaya da yake gefe nan da nan bacci ya d’auke ta.

Yaya ganin zafi zai dame ta ya saka ta d’auko k’aramar fankar ta mai chaji ta kunna mata a kusa da ita dan taji dad’in baccin sosai. Itama Zaytun tana gama cin abincin tayi bacci aka kwantar da ita a kusa da Ameena suka fita suka koma dakin yaran sabida kar a tashe su.

Sai bayan la'asar ta farka ta tashi zaune lokacin fankar ma chaji ya k'are ta kashe mata ta kuma tashi ta shiga band’aki ta wanke bakin ta t sake yin wanka da ruwan da ta gani ta fito ta saka kaya ta fito tsakar gidan a nan take Jin hayaniyar su. "Lah Aunty Ameena!" Karamin d'anta Yaya mai sunan Baba wanda suke Kira Daddy ya fad’a yana tasowa a guje ya rungume ta. Ta kalle shi tana murmushi tace, "D’azu dana zo kana makaranta."
"Aunty kin zo min da alawar kano?."
"Nazo maka da ita, Hidaya jeki ki bude’e jaka ta akwai Leda zaki ganta ki d’auko min." Ta fad'a tana zama kusa da Yaya da take kallon ta.

Yaya tace, "Sai kici abinci ko?." Yaya ta kalli Amira tace, "D’auko mata abinci taci." Amira ta tashi da Zaytun a hannun ta ta d’auko abincin a flasks ta ajjiye mata Ameenatu ta bud’e taga lafiyayyen dambu ne ta baje ciki tana ci a nutse. Ameena ta kallo Amira tace, "Ina Muhammad ne? Ban ganshi ba."
"Tare suke tafi kasuwa da Abba yanzu zaki ga sun dawo."

Ta kai Ameena ya girgiza ta cigaba da cin dambun ta kad’an ta rage Yaya ta kalle ta tace, "Zaytun dai bata Rigima kamar bata ganki bama."
"Yaye ta ma zanyi wallahi, na gaji Yaya shekara biyu ai nayi kokari.”
"Ai tana cin abinci gashi tana tafiya harda gudu ga magana tun d’azu take mana hira kamar ba y’ar shekara biyu ba, tana da wayo sosai.”

Yaya kallon Ameenatu din take yi tana shan ruwa bayan ta gama tace, "in kin gama ki same ni a dami Ameenatou" ta fad'a tana shiga d’aki. Ledar da Hidaya ta kawo mata ta bud’e ta basu cakes da ta kwaso musu da cincin da chocolate. Suka dinga murna t tashi ta shiga dakin  da Yaya ta shiga ta zauna kusa da ita.
Chapter 9 · 0% Book details