Sashe 3
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye private asibitin da take ganin Dr Mansura ta wuce sai da taje bakin office din ta tsaya ta kira Dr Mansura d’in tace ta shigo tana ciki ta kuwa shiga ta same ta a zauna tana ta aikin rubutu a file. Ameena ta zauna tana fad’i, "Barka da safiya Dr." Dr mansura ta d’auki Zaytun da take kujerar kusa da Ameena tana cewa, "Barka dai Ameenatu, ya jikin naki?."
"Gani nan dai kawai Dr, ciwon kan nan yayi min yawa sosai. Ni ban tab’a ciwon kai ma kamar da ba wallahi, idanu na har daina gani suke yi.” Dr mansura ta ajjiye Zaytun akan kujera ta tashi ta fara auna bp d'in ta.
"Kai Subahanallahi! Ameena jinin ki ya hau sosai fiye da baya." Ameena ta sauke numfashi bata ce komai ba daman tasan za’ayi hakan Dr tace, "Haba Ameena meyasa kike saka damuwa a zuciyar ki har haka? Yanzu tsakani da Allah ya kyautu ace a shekarun ki jinin ki ya hau haka?. Wacce damuwa kike da ita da zaki d’auke ta ki saka a zuciyar ki har ta haifar miki da hawan jini hakan?.”Ameena tace, "Dr abubuwan ne sai a hankali kawai."
"Ko meye hak’uri ake Amina, ba ko yaushe kake zama cikin farin ciki ba hak’uri ake ana mayar da komai ba komai ba sai kiga an samu sassauci. Wallahi in kowa yace zai saka damuwa a ransa da yanzu duk duniyar Mun k’are saboda ciwo ya kashe mu baki d’aya.”
Ameena bata ce komai ba Dr ta kuma cewa, "Bana son d'ora ki akan maganin hawan jini ne dan kina fara sha shikenan kullum sai kin sha har abada, shi illar sa indai aka fara sai an gama sai dai in an auna an ga jinin ya sauka ace ki rage sha amma ba ki daina ba, shiyasa bana son ki fara sabida shekarun ki sunyi k’aranci a wanann yanayin. Amma abin naga bazai yu ba dole na baki magani kodan ki samu saukin ciwon kan" ta fad'a tana zama tare da rubuta mata magani kafin ta kuma cewa, "Kuma fa indai baza ki daina saka damuwar ba wallahi ko kin sha magani a banza, kinga tunda na fara auna jinin ki ban tab’a gani yayi k’asa ba sai dai ya hau na tabbata kuma damuwa kike sakawa zuciyar ki haka, in aka cigaba da haka wallahi wata ran za’a wayi gari wani ciwon ya kama ki wanda baki yi tunani ba. sai kinyi hak’uri sannan zaki samu Lafiya."
Ameenatu tace, "in sha Allah zanyi k’okari Dr, ki rubuta min na ciwon marar." Tsayar da rubutun tayi ta kalli Ameena tace, "Shan maganin kwantar da sha'awa ba naki bane Ameena, kina da aure mijin ki shine maganin ki meyasa baza ki sanar dashi damuwar ki ba? Kina da hakki fa in hakan ya cutar dake fa?, ke baki san yawan Shan su yana haifar da illa ba?. Ameena wai meye damuwar ki ne?.”
Ameena tayi murmushi tace, “Damuwa ta yawa ce da ita Dr.”
“Meyasa baza ki sanar da na gaba dake a shiga maganar auren ki ba?, look Ameena ba wai ina so naji sirrin ki bane, ina miki magana matsayina ta likitan ki kuma y’ar uwat ki mace. In ke kina ganin baza ki iya yiwa mijin naki magana ba ki fad’a a gida ayi masa magana.”
Numfashi Ameena ta fesar tana girgiza kanta kafin tace, "Dr bani da iyaye, duk sun jima da rasuwa. Yusuf da ya kawo ni wajan ki tun jikin Zaytun har muka Saba shine kawai dani a kusa a yanzu, dan haka ki rubuta min kawai Dr lamarin ne sai hak’uri kawai."
Dr ta tallafi hab’a tace, “Yanzu in kika fara shan maganin sha'awar ta tafi gabadaya fa?."
"Shikenan na huta ma wallahi."
Dr ta girgiza kai tace, "Da yarintar ki kike yiwa kanki wannan fatan?." Ameena tace, "Kawai kı rubuta min dan Allah, kar hakan ya jefa ni cikin wani halin na daban.” Dr ta cigaba da rubutun kafin ta mik'a mata tace, "Gashi nan ko wanne akwai dose d’in da za’a sha, shi na ciwon marar kar ki dinga sha da yawa, kar kisha yau kisha gobe da jibi, in kika sha sau d'aya a wata ya isa sauran ranakun ki jure in ba haka ba zai miki illa. Koda yake in kin siyi maganin kawai kiyi snapping ki tura min zan miki bayanin ko wanne."
Karb’a Ameenatou tayi tace, "Na gode sosai Dr."
"Babu komai kar ki damu, amma ranar da angon nan naki zai dawo kamata yayi kizo ayi miki d'inki ki dawo sabuwar amarya" ta fad’a cikin zolaya duk dan ta kwantar mata da hankali. Ameenatou ta zaro idanu tace, "Rufa min asiri." Dariya Dr tayi tace, "Allah kuwa kizo." Ameena tayi dariya itama ta mik’e ta d’auki Zaytun tace, "Ai tun na haihuwar Zaytun ma da kika min bana kin Ina buk’atar wani ma a yanzu."
Dr tace, "Kawai dai bakya so ne zaki wani wayance, ai shikenan." Dariya tayi itama sukayi sallama ta fita. Kai tsaye pharmacy ta shiga ta siyi magani ta shiga mota taja ta fita daga asibitin.
Gidan Yaya Sumayya ta wuce a can ta zauna har bayan azahar sannan ta koma gida.
Tun bayan an sallami Fiddausi take a d’aki Itada Zakiyya suna kwancewa suna sake k'ullawa akan abinda ya faru da kuma wanda zai faru nan gaba. Fiddausi tace, "Yanzu ya akayi wai akace cikina ya zube ta dalilin duka bayan nasan maganin da kika bani na sha biyar lokaci d'aya ne ya jawo min haka?.”
Zakiyya tace, "Nurse d’in na samu kawai ta canja bayanin da ta yiwa su Maman, ke in kana da kudi fa a Nigeria zance ya k’are wallahi." Fiddausi tace, "Yanzu meye abu na gaba d zamuyi?."
"Ai ban sanar dashi auren ki ya mutu ba a yanzu, so nake ki dawo hankalin ki ki mayar da jikin ki sai mu san abinda za'ayi."
"Amma Ina Jin Abba fa Zakiyya, Anya zai amince ayi auren nan nan kusa duba da abubuwan da suka faru?.”
"Zai ma amince in sha Allah, in bai amince ba sai mu bi ta hanyar Kawu Sa'idu ba shikenan ba?."
Fiddausi tayi dariya tace, "Ke wallahi kanki yana Bala'in ja, kin San kuwa Kawu sa'idu da yaga kudi shikenan magana ta kare. Amma kuma ai dole maganar taso wajan Abba ai, ni kuma na tabbata Abba bazai amince da aurena nan kusa ba.” Zakiyya tayi dariya itama tace, "Ke komai a tsari za'a yi fa ki jira kawai lokacin yayi zamu tsara plan ta yadda babu wanda zai gano akwai wani abun a k’asa.”
Mama ce ta shigo dakin sai Fiddausi ta langwab'e kamar gaske Mama tace, "Yanzu mahaifin yaron nan Ibrahim yayi waya da gaske dai anyi sakin nan tunda gashi sun fad'awa mahaifin ki, gaskiya Ibrahim bai kyauta ba abun ma har da dukan da ya zama silar zubewar ciki, badan mahaifin ku ba ai baza'a bar maganar nan ba. To shi kamar ma bai amince ba har yanzu gani yake kamar laifin naki ne.”
Zakiyya tace, "Mama ya saba kawai fad’a muku ne ba'ayi, amma dan Ibrahim yayi mata duka ai ba wani abun bane tasha zuwa wajena Ina bata baki ta hakuri ta koma. Kuma Abba yana amfani da halayyar İbrahim ta zahiri ne shiyasa baya ganin laifin sa a yanzu, amma wallahi zai tabbatar nan gaba.”
"Yanzu ai komai ya ‘kare Zakiyya, ya za'ayi da Amir?."
"Mama kawai ya rik’e shi in yaso a dinga kawo shi akai akai yana ganin ta, in aka kawo shi nan a sake d'ora miki wata wahalar ne Mama."
Mama tayi shiru alamun tunani ta sauke numfashi tace, "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" ta fad'a tana fita. A tare suka kalli juna sukayi dariya Zakiyya tace, "Allah Sarki Ibrahim an tafi kenan.”
“Har abada kuwa, ni ko a hanya ma bana so mu had’u wallahi.”
“Yanzu ya zakiyi da kayan ki na gidan?."
"Ya barwa matar da zai aura bana so, ke nifa tunda na tattara kud'ad'ena da Kayan da nake so na kai gidan ki wani abun na gidan baya gabana wallahi."
"Saura kiris dai ki zama matar Alhaji in sha Allah."
"Ai zan fad’a masa ke sarkin yaqi ce ya kamata a yi miki kyauta ta musamman bayan auren mu."
"Ina so na ganki cikin daula ne ‘kawata."
"Amma da wallahi sai na saka an kama min İbrahim, wallahi sai na saka ya fahimci ni ba kalar wacce zai daka a banza bace. Sai ya girbi abinda ya shuka a lokacin ni kuma nayi masa rata sai dai gani daga nesa.”
Zakiyya tayi dariya tace, "Kina da iko yarinya, Kiyi abinda kika ga dama ke matar manya ce wallahi." A tare suka kuma tafawa suna cigaba da tattauna yadda abubuwa zasu kasance.
A gidan su Ibrahim a safiyar bayan Alhaji ya gama waya da Abban su Fiddausi ya kalli Ibrahim da yake zaune a gefen sa yace, "Kaji jiya a asibiti ta kwana wai sila dukan da kayi mata ya saka cikin jikin ta ya zube sai da aka yi mata wankin ciki."
Ibrahim yayi murmushi, "Wallahi Alhaji k’arya take ni ban dake ta ba, duk abinda ya faru tsarawa tayi akwai abinda take son cimmawa shiyasa tayi hakan. In da na dake ta ai Yaya Sulaiman zai fad’a maka, ko kuma tana so tace tun dukan safen ne bai tashi zubar da ciki ba sai dare? Alhaji ka bar Fiddausi kawai.”
Hajiya tace, "Ni daman nasan wallahi baza ka yi mata dukan da zai saka tayi b'ari ba sai dai in akwai abinda yake zuciyar ta."
Alhaji yace, "Kenan dai yanzu ta kammala idda, daman dan me ake yin idda….? saboda a tabbatar babu shigar ciki a cikin watanin, to ita ya zube har wankin ciki ma ance anyi mata, babu damar kome yanzu sai an sake sabon d'aurin aure." Hajiya tace, "Daman ban kawo ma zai mayar da ita ba wallahi a raina, ai wanda yaso kashe ka baza ka so ka sake rab'ar sa ba, ya cigaba da neman kud’in da Allah ya bashi wacce ta fita."