← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 42

Sashe 13

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ta fito sai ya mik’e da Zaytun tana ji Yaya nayi masa godiya alamun ya bata wani abun ta kalli Yayan tace, “Yaya dan Allah ki bani Amira mu tafi tunda bata zuwa makaranta, ni ki bar min ita kawai dan Allah tayi makarantar a kano.” Yaya tace, “in na bar miki ita ni kuma fa?”.

“Ba akwai Hidaya ba?, dan Allah ki bar min ita mu tafi yanzu.” Yadda tayi maganar da wata irin murya ta nuna tsantar rashin son tafiya har muryar na rawa ya saka ya kalle ta ita kuma bashi take kallo ba hakan ya saka ya kalli Yayan yace, “in da dama a bamu ita d’in Yaya.” Yaya tace, “Yanke hukunci sai mahaifin ta ya dawo, zata zo dai tayi Hutu amma badai na bar muku ita ba gaskiya.”

Yusuf yayi murmushi yace, “Hakan ma Mun gode.” Yayi hanyar fita yace, “Yaya Mun koma Allah ya saka da alkhairi.” Ta amsa da amin ya fita sai kawai hawaye ya zubowa Ameena Yaya ta dafa ta tace, “Meye na kukan kuma?.”
Ameena tace, “tsoron komawa nake kar naje wannan shine ganina dake na k’arshe Yaya, komawa ta Ina ji a jikina kamar mutuwa zanyi.”

Yaya cikin sigar kwantar da hankali tace, “Haba Ameena meye na wannan zancen kuma dan Allah?.”
“Yaya sai naga kina masa dariya bayan kin San abinda yake yi min. Yaya kin manta nice y’ar Uwar ki bashi ba? Amma sai naga kin sake dashi kamar ba abinda yake so yake yi min ba.”
“Kuka zan masa Ameena? Ko kuma na kore shi nace ya tashi ya fita Ameena?. Ya kike so nayi masa.? In bakya son ki koma ki zauna bazan hana ki ba dan basan abinda kike ji a zuciyar ki ba. Duk da zaman gıda kaddara ce amma Ameena bana son ace da auren ki kina zaune a gida da sunan yaji, ke kika fada min halayen y’an uwan mu in suka ji wacce irin darıya zasu yi mana?, mu ture batun su ma Ameena zaman gidan ki shine rufin asirin ki, amma in bakya so wallahi bazan hana ki zama ba Ameena, zan fita da kaina yanzu na fad’a masa baza ki tafi tare dashi ba.”

Ameena ta girgiza kai ta goge idanun ta tace, “Kawai bana son komawa yar gidan jiya ne, zamana a nan na samu abinda nake so amma a can…..” sai kuma tayi shiru tana goge idanun ta tace, “Dan Allah in Abban su Amiran ya amince zan turo a d’auke ta gobe, zaman ta a tare dani zai saka naji dadi sosai kamar Muna tare dake Yaya.”

“In sha Allah zan masa magana ko wasu kwanaki ne tazo tayi miki.” Ameena ta girgiza kai ta rungume yayar tata kafin ta sake ta tace, “Sai munyi waya.” Yaya ta girgiza mata kai tayi hanyar fita ta bita da kallo har ta fita sannan ta daina kallon wajan. da ace tana da yadda zatayi Ameena baza ta koma Kano ba, bata son shiga tsakanin mata da miji kar tazo taji kunya dan tafi kowa sanin son da Ameena take yiwa Yusuf har gobe kuma tana son sa, kuma ita Matsalar aure a koda yaushe sassanci ake yi ba b’ataww ba shiyasa take daurewa tana kawar da komai amma mugun haushin sa take ji a ranta amma baza ta nuna ba saboda matar sace har gobe.
Kallon kud’in da ya bata tayi ta sauke numfashi tace, “kula da yar uwata yafi min wannan kud’in Yusuf” ta maimaita kamar yadda ta fad’a a gaban sa.

Dawowar Amira ne ya tabbatar mata da sun tafi ta sauke ajiyar zuciya tace, “Allah ka bawa Ameena juriya, in ita ake cuta ka saka mata ka daidaita tsakanin su.” Amin taji Amira ta fad’a hakan ya saka ta kalle ta dan bata san a fili tayi maganar ba kafin ta shiga cikin daki.

Suna baya ita da Yusuf driver na jansu a mota, motar Ameena kuma wani yana ja daman su uku suka tawo saboda motar Ameena din. Babu Wanda yake magana suna zaune Ameena tana kallon titi kewar iyayen ta na taso mata sai hawaye take tana gogewa. Zaytun na jikin sa tana bacci ita kuma tana kallon taga kafin ta kifa kanta a cinyar ta tana kuka a hankali dan ta kasa rik’e shi.

Yana Jin ta yana kuma hankalce da ita duk abinda take yi yana gani baiyi magana ba tafiya kawai ake yi har ta gaji da kukan ta goge idonta ta jingina da kujera ta kulle idanun ta. Sai gab da La’asar suka shiga gida ta fita daga motar bata ce komai ba ta shiga gidan kai tsaye ta wuce d’aki tayi wanka tayi sallar azahar tayi la’asar tana zaune tana jan carbi bacci ne yake neman d’auke ta.

Dago kai tayi ta kalle shi jin motsin sa dan bata san ma ya shigo ba shima ita ya kalla ya zauna a gefen gadon ya hard’e hannayen sa waje d’aya yace, “Meyasa kika tafi Bauchi ba tare da izinina ba?.” Shiru tayi bata amsa ba dan ita bata yi tunanin zai damu dan taje Bauchi bai San ta tafi ba hakan ya saka ya kalle ta yaga bashi take kallo ba yace, “Baki da amsa kenan?.” Ta d’ago ta kalle shi tace, “İn zaka tuna na fad’a maka ina so zanje Bauchi.”

“Kina so kika ce min ba zaki tafi ba ko?.” Tayi shiru bata amsa ba yace, “Dan nayi miki magana akan abinda kika yiwa wacce zan aura shine kika yi yaji kika tafi kenan?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “abu nawa aka yi wanda yafi wancan banyi yaji ba sai shi?.”
“Saboda tsanar ki da aurena mana, ai ko meye a wajan ki ya biyo bayan maganar aurena. Tunda ta shigo kika canja ko abinci sai kin yi niya kike bani har ta kai ta kawo Ina miki magana kina mayar min kamar sa’an ki.”

Tayi shiru nan ma bata ce komai ba ya sake cewa, “duk abinda Ammah zata yi min fad’a a koda yaushe shi kike so saboda kinga tana sonki, abu d’aya nake so ki tuna Ameena, ni Yusuf Ammah haifa ba ke ba, ko ya ya kike min wani abun dole zata ji babu dad’i a ranta duk abinda take yi miki kara ce kawai. Yanzu da kika je Bauchin maganin ne hakan yayi miki? Ko kuma zuwa kika yi kika fad’awa Yayaar ki ai nayi miki fad’a dan kin yiwa wacce zan aura wulakanci?.”

“Daman babu abinda zai min magani ai sai Allah kuma gare shi na mik’a dukkan lamarina, in badan yanzu da ka tuna min da maganar wacce zaka aura bama wallahi ni na manta da batun ta.” Ya girgiza kai yana kallon ta ransa na suya in yaji tana mayar masa da magana in yana magana yace, “Naga alama rashin kunyar ki sake gaba take duk akan zanyi aure, kin nisanta kanki dani da duk wani abu naki yanzu kuma kin samu bakin fad’a min duk abinda kike so. Yayi kyau, kin kyauta. Ina so na sake gargad’in ki akan yin doguwar tafiya tare da yarinyata” ya fad’a yana nuna Zaytun da take bacci yace, “İn zaki yi ke kad’ai ki yi amma kar ki sake yin wannan gangancin da ita.”

Ya mik’e tsaye yana kallon ta yace, “Kar kiyi tunanin naje na dawo dake daga Bauchi saboda Ina son hakaan ba, naje na dawo dake ne saboda Amma da kuma Zaytun d’ina bada su ba da baza kiga k’afata a inda kike ba Tunda dmaan bani na kai ki na.” yana gama fad’ar hakan yayi hanyar barin d’akin tace, “Nima ban dawo dan wani ba ai, na dawo saboda darajar Ammah badan ita din ba wallahi da naje kenan, yadda ba’a damuwa da na dawo ba nima ban damu na zauna ba.” Juyowa yayi ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya fita.

Da kallo ta bishi ta girgiza kai bayan ya fita ta cigaba da jan charbin ta bata bari kalaman sa sun yi tasiri a zuciyar ta kamar yadda aka saba ba, dan ta lura maganar da tayi ce ta k’arshe ta fusata shi da a hankali yake magana amma tunda tayi maganar ya fusata, sai dai kuwa yayi tayi dan auren sa a yanzu baya gaban ta ko kad’an.

A falon ta ya tsaya yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudu ya kulle idanun sa ya bud’e yana tuna abinda ya fad’a mata da wanda ta fad’a masa, ya fad’a mata haka ne kawai dan taji haushi taji abinda yaji lokacin da ta tafi ya wayi garı bata nan bai fad’a mata dan da gasken sabida Amman yaje ba sai dan ya k’ona mata rai kamar yadda ta k’ona masa rai a ranar da ya tashi bata nan. Shi kansa yasan yana kewar ta sosai, ganin da yayi mata a gidan Yaya a Bauchi ba k’aramin dad’i yaji a zuciyar sa ba baya son nuna mata ne dan kar ta samu damar sake raina sa. D’akin ya juya ya kalla kamar zai koma sai kuma ya fasa ya fita daga falon gabad’aya.

#Nana Haleema
#Mai daki
#book2
#Paid
#500

Book2
009

Lokaci yana ta gudu biki yana sake matsowa b’angaren Amarya Asiya aka ta shirye-shirye an kawo lefe na gani a fad’a gida gida aka dinga bi ana fad’a dan azo aga lefen y’ar ta bana matsiyata bane ba. Yusuf kuwa shi kad’ai yake sabgar bikin sa babu wanda yake taya shi har gwara ma Yayyen sa maza su kan tambaye shi ya shirin biki amma ‘bangaren Amma da matan babu ruwan wani dashi.

Biki ya rage saura kwana goma a fara Ameena tsakanin ta da Yusuf sai ido kawai kamar yadda baya sakewa da ita haka itama bata sakawa dashi. Har tafi jin dad’in hakan ma tunda kwana biyu babu fad’a sai tafi Jin dad’in su zauna shiru d’in yafi mata alkhairi hankalin ta yafi kwanciya. A cikin kwanakin Amira tazo sai hakan ya sake kawar mata da tunani daga kansa ko yaushe tare da Amira suna hira.
Chapter 13 · 0% Book details