← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 42

Sashe 38

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaya Adam ya sake cewa, "haka ta d’auki mota ta tafi Bauchi taje tayi kwana uku shima duk dan saboda damuwar da take ciki a gidan." Yaya Adam ya kalli Yusuf yace, “a cikin abinda na fad’a da wanda likita ta fad’a in akwai k’arya a ciki Yusuf ka musa.” Shiru yayi ko motsi ya kasa kunyar duniya ta ishe shi ko d’ago kai ya kasa yi Yaya Adam ya sauke numfashi yana kallon kowa yace, "Abinda yasa duk nayi wannan bayanin Ina so azo gab’ar da nake so ne yadda kowa zai fahimci abinda nake so kuma ina da hujja akan hakan. Tunda har baya sonta kuma ta kasance b’arauniya ce, kai ko babu wannan dalilan da likita ta fad’a iya abinda na gani zama da Yusuf ba alkhairi bane balle kuma bayanin likitan sun fi wannan d’aga hankali."

Yaya ya kalli Abbah yace, "Alhaji!." Abbah ya amsa yana kallon sa kafin yace, "matsayina na gatan Ameena kuma uba a wajan ta na yanke hukuncin bazata sake zaman aure da Yusuf ba itama ta bani goyan bayan hakan. Soyayyar da kuka nuna mata Allah ya saka muku da alkhair ya biya ku amma ku yi hak’uri Ameena ta gama zaman aure a gidan Yusuf." Abbah ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "wannan hukuncin da ka yanke shine daidai Adam, hakan da kayi shine abinda ko wanne uba ya kamata yayi, koda nine nima irin hakan zanyi akan ko waye.”

Yaya yace, “Na gode da kuka fahimce ni” ya dawo da kallon sa ga Yusuf yace, “Yusuf ina jiran takardar sakin Ameena ka kawo min ita har gida kamar yadda kazo har gida ka karb’i auren ta. Sannan ina so ka sani badan iyayen ka da nake ganin girma da daraja ba da yanzu ba kaine a wajan nan a zaune ba, dan wallahi sai nayi maka hukuncin da ko a mafarki baka d’auka za’a yi maka irin sa ba, to kodan soyayyar da suke yiwa Ameena alfarmar su dole ta shafe ka shiyasa na kyale ka. amma ka tabbatar ka kawo min takardar saki domin nayi alqawarin ta gama zama dakai tunda baka sonta kamar yadda ka fada naji da kunne na kuma na gani a aikace a bayanin Dr.”

Kowa yayi shiru babu mai magana su cikin su dan basu da bakin cewa komai hukuncin Adam daidai ne ko sune abinda zasu yi kenan. Ganin hakan ya saka Yaya Adam ya mik’e tsaye yace, "to Alhaji na barku lafiya, ni zan koma gida. Ayi hak’uri haka Allah ya kaddara auren nasu bazai yi wani tsaho sosai ba.” Abbah ne yayi k’arfin halin cewa, "Allah ya kiyaye Adam Allah ya bar zumunci. Kar ka damu abinda kayi shine daidai babu Wanda zai ga laifin ka a nan, Allah ya kiyaye.” Yayi murmushi yace, "Amin ya Allah, sai da safe" ya fad'a yana fita daga falon duk suka bishi da kallo har ya b’ace daga idanun su kafin su dawo da kallon su ga Yusuf.

#Mai daki
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema

Book2
024

Yusuf ya kasa d’ago kansa idanun sa a kulle gabad’aya kunyar had’a ido yake da kowa a ciki falon musamman ma Ammah da yake jin sautin kukan ta hakan ya saka shi kasa ko motsi ya kuma kasa kallon kowa balle ya iya magana. Kusan mintina biyar yana a haka ya kuma ji shiru babu wanda yayi magana a cikin su dan shi shirin ayi masa fad’a yake amma yaji tsittt babu wanda ya furta hakan ya saka shi d’ago kai ya kalli falon amma sai yaga babu kowa saura shi kad’ai ya rage a zaune duk basa wajan.

Numfashi ya sauke zuciyar sa na harbawa da sauri ya dafe kansa ya rasa abinda yake masa dad’i, zuciyar sa a cushe take ya rasa abinda yake damun sa, bai san lokacin da ya kwashe a wajan ba yana nan zaune sai jin muryar Mubakar k’anin sa yayi yana cewa, “Yusuf zan kulle k’ofar.” Sai a sannan ya d’ago ya kalle shi sai ya mik’e ya fita jiki a sanyaye.

Kuka Ammah take yi sosai kamar k’aramar yarinya haka Humaira ma Yayan Abuja ce kawai take daurewa tana rarrashin Ammah amma abin yaci tura kuka take yi sosai dan abinda aka fad’a a wajan ya karya mata zuciya sosai. Har take ji a zuciyar ta tamkar harda saka hannun ta wajan cutar da Ameena.

Yayan Abuja tace, “Dan girman Allah Ammah ki daina wannan kukan, Kiyi hak’uri.” Ammah tayi shiru da kukan ta kalle ta tace, “baki ji abinda akace Yusuf yana yiwa marainiyar yarinyar nan ba? Duk abinda aka fad’a Baki ji bane?.”
“Naji Ammah, amma wannan kukan ai ba shine mafita ba, ke kanki ciwo zai saka miki tunda ba magani zai miki ba.”
“Yarinya ya sakawa hawan jini, ko yaushe cikin damuwa take in ka tambaya sai tace babu komai. Ina Yusuf zai kai hakkin yarinyar nan?.”

Humaira da take gefe Tce, “Ammah harda dukan ta wai yake yi, gaskiya sai Allah ya saka mata sai yayi dana sanin da baiyi tunani ba a rayuwar sa. Ban san halin wa Yaya Yusuf yayi ba wallahi.” Ammah ta girgiza kai tace, “Bari kawai, ina tausayawa Yusuf akan hakkin yarinyar nan ganin da yake kamar wasa.”
Yaya tace, “Wallahi komai ya aikata sai yayi dana sani, kuma nima bana goyan bayan cigaba da zaman auren su tunda baya son ta ya sake ta ya zauna da wacce yake so shikenan ya huta shima.”

Ammah tace, “Dan tsabar k’arya da rashin tsoron Allah wai ni nace ya aure ta shi ba sonta yake yi, Allah kad’ai yasan abubuwan da yake k’unsawa yarinyar nan shiyasa kullum take a rame kamar ba’a cikin jin dad’in take ba. Wai ni nace yaje ya aure ta, an ina nasan Ameena in badan yazo da maganar ta gidan nan ba?.” Yaya tace, “shi ya sani kuma ai, yayi asarar da bazai tab’a mayar da ita ba har abada. Ni abinda yafi bani haushi wai sata! Yanzu Ammah dan Allah in Ameena tana sata tun auren su ai mu ma baza mu tsira ba.”

Humaira tace, “Amaryar da yake rawar kai a kanta wallahi itace mai sace-sacen, daga zuwan ta gidan nan ta zauna a d’akina ta d’auke min agogo da kuma yarin kunnen nawa.” Yaya ta wara ido tace, “Kice wallahi?.”
“Wallahi da gaske nake, a cikin jakar ta duk na d’auko da taga na gane sai ta basar kamar ba itace ta d’auka ba. Yadda ta basar din nan zaki tabbatar cikakkiyar b’arauniya ce. Wallahi Yaya Yusuf ya d’auki abinda yafi k’arfin sa.”

Ammah tayi shiru tana jin su kafin tace, “Yanzu da Ameena ta fara neman maza dan Allah me gari ya waya?.” Yaya tace, “Nima shin yafi d’aga min hankali Ammah, yarinya k’arama yana kokarin jefa ta cikin halaka. Ai wallahi Yusuf ya kikayi hakkin ta da zai bibiye shi nan gaba, ko bani da rai zaku ce masa na fad’a muku.” Shiru dukkan su sukayi kowa yana tuna abinda aka fad’a suna sake tausayin Ameena tare da jin haushin Yusuf matuk’a a zuciyar su.

A haka Yusuf ya koma gida ya shiga b’angaren Asiya ya same shi gashi nan dai kamar kullum ba gyara balle khamshi bai bi ta kai ba ya wuce sama ya shiga d’akin sa ya zauna tare da dafe kai da duka hannayen sa guda biyun.

Abubuwan da suka faru ne suka masa yawo a cikin kansa shi Kansa ganin abun yake kamar wasa kamar kuma bai faru ba, sai a sannan ya tuna da cewa tabbas Ameena zata iya cutuwa ta b’angaren k’in sauraren ta da yake yi amma a kwanakin baya bai kawo hakan ba ko kusa a zuciyar sa tunda ya neme ta tak’i zuwa shikenan ya watsar da lamarin ta a gefe. In zai iya turawa rabon sa da ita tun ranar da yayi mata yawo taje ta samu Amma akan maganar auren sa bai sake waiwayar ta ba.

A bayyane yace, “kusan wata biyar kenan ko wata hud’u?.” Ya cize baki yace, “ya salam!.” Ya sake dafe kansa cikin rashin sanin ma abinda zaiyi dan abin damun sa yake a zuciyar sa kamar mutum abu na damun sa a cikin sa haka yake jin abun na yawo a zuciyar sa . Bud’e k’ofar akayi aka shigo yasan Asiya ce hakan ya saka bai d’ago kansa ba ta zauna kusa dashi tace, “My love lafiya kake?.” Bai kula ta ba ta sake cewa, “My love magana nake fa, lafiya kake?” Ta fad’a tana dafa kafad’ar sa.

“Bana son hayaniya ki kyale ni” ya fad’a a hankali batare da ya kalle ta ba.
“Taya zan kyale ka bayan naga ba daidai kake ba?.”
“Ki kyale ni nace.”
“Nidai A’a, tun d’azu nake jiran ka ko bacci banyi ba kace kuna na kyale ka?.”
“Asiya ki kyale ni nace!” Ya fad’a da k’arfi yana janye hannun ta daga jikin sa yana nuna mata hanyar fita.

Sai da ta tsorata ganin yadda ya canja idanun sa sun yi ja hana yi mata tsawa, kallon sa take yi da mamakin tsawar da yake mata ta bi hanyar k’ofar ta fita a ranta tana tabbatar da dole ma ta sake d’aukar mataki domin ita ya kamata tayi masa tsawa ba shine zai mata tsawa ba.

Washe gari.

Yaya suna tare da Ameena ta saka ta a gaba suna karyawa tare tana jan ta da hira jefi-jefi ta kan amsa wani abun kuma sai dai tayi dariya kawai bata cewa komai ba. Yaya ta zuba mata ido bayan sun gama cin abincin tace, “Ameena Yaya yace kin bada goyan bayan Yusuf ya sake ki, da gaske ne har zuciyar ki?.”
Chapter 38 · 0% Book details