Sashe 12
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf da mamaki yace, “me kika ce?.” Ameena tace, “Abinda kaji.” Ya girgiza kai yace, “Okay rashin mutuncin naki har yazo nan kenan ko? Ke a duniya in baki had’a ni da mahaifiyata ba bakya Jin dad’i, babban burin ki a duniya kiga Amma tana yi min fad’a saboda kawai tana sonki ko?. To wallahi in ma wani abun kika yi mata take son ki haka wallahi Nafi k’arfin ki a ta ko wanne b’angare. Yadda kika saka raina ya b’aci akan lamarin nan kema sai naki ya b’aci wallahi sai kin ji abinda naji, ki kuma shirya gobe zan aiko a dawo dake, kuma wallahi ciwon kai Zaytun tayi ta dalilin tafiyar ki da dawowar ki a kanki zan d’ora alhakin Hakan.”
Ameena tace, “Ban shirya dawowa gobe ba gaskiya kamar yadda na tafi zan dawo da kaina” tana gama fad’a ta yanke wayar yabi wayar da kallo yana ji kamar ya jawo ta yayi mata dukan tsiya ta wayar. A fusace ya hau saman ransa yana suya ya bud’e fridge dinsa ya d’auko giya ya kafa kai yana sha ko zai ji dadin suyar da zuciyar sa take masa. (A ganin sa amma fa).
Sabon machine ne fil ko ledar sa ba’a cire ba ibrahim yake shigowa dashi tsakar gidan su a lokacin Alhaji yana niyar fita Hajiya da Fadima da Amir suna zaune. Duk tsayawa sukayi suna kallon sa daman yasan za’a yi hakan yayi murmushi ya k’araso yace, “kunyi mamaki ko?.”
Alhaji yace, “Ka barmu baki sake muna kallon ka ai, k’arin bayani muke so an Ina ka samo wannan?.” Ibrahim yace, “Wallahi Alhaji Ogan mu da na fara aiki a company sane ashe mu uku ya d’auka amma nine kawai a b’angaren mu sauran a wata unguwar suke, shine ya bamu kyautar baburan nan saboda an fad’a masa muna jajircewa a wajan aiki sannan ba’a tab’a bamu kud’i mun b’atar da naira biyar ba, Jin dad’in hakan ya saka yayi mana wannan kyautar yanzu.”
Alhaji da Hajiya suka fad’a baki wajan kabbara Alhaji yace, “Kai na taya ka murna Ibrahim, Allah ya rik’e yasa mabud’in arzuki kenan, Allah ya kare ya kawar da idanun makiya. Ni nasan biyayyar da kake mana bazata tashi a banza ba, duk wani abu da yake faruwa da kai na lokaci ne gashi yanzu ya fara wucewa kana ganin ribar abinda kake aikatawa, ka cigaba da rik’e gaskiya a duk Ina kake baza kayi dana sani ba.” Ibrahim ya amsa da Amin yana Jin dadin addu’ar nan da iyayen sa suke masa Alhaji ya fita shi kuma ya zauna.
Fadima tace, “Yaya Ibrahim Allah ya tsare ya kawar da idanun makiy.” Ya amsa da amin yana murmushi ya kalli Hajiya yace, “Baki ce komai ba.”
Tace, “Dad’i ya hana ni magana Ibrahim , Allah ya sanya alkhairi ya kare ya kuma kiyaye hanya kaji?.” Ya amsa da amin ta kuma cewa, “Allhairi kamar jira ake wani abun ya fita daga rayuwar ka gashi sai b’ulb’ulowa yake yi, me zamu ce da Allah in ba godiya ba.”
Murmushi yayi kawai bai ce komai ba dan yasan maganar ta da Fiddausi take Hajiya tace, “Sai ka fara shirye-shiryen aure kuma ko?.” Ya wara ido waje yana dariya yace, “Aure kuma hajiya?.”
“Eh Aure Ibrahim, me zaka jira kana da sana’a da abin hawa ga gidan kan ka me za’a tsaya jira?.”
Yayi murmushi yace, “Ba yanzu ba Hajiya, zan mayar da hankalina akan neman kud’i nan gaba sai ayi wannan maganar Hajiya.” Hajiya tace, “Allah ya nuna mana, ka zab’o mai tarbiyya ba irin waccan da ta fita ba.” Yayi murmushi yace, “A cigaba da taya ni da addu’a kawai.” Hajiya tace, “Addu’a Kullum cikin yi maka ita ake in sha Allah kuma za’a ga abinda Allah zaiyi, Allah ya baka ta gari wacce zata kula min da kai.” Ya amsa da amin ya tashi tsaye ya fita yana dariya itama haka farin ciki yana shiga ranta domin Tunda ya rabu da Fiddausi walwalar sa ta dawo kamar dah, babu damuwa a kan fuskar sa ko kad’an Kullum cikin nishad’i yake kamar yadda yake a baya.
Book2
008
Ameenatu tana sauke wayar daga kunnen ta Yaya da take kallon ta tunda aka fara wayar tace, “Yusuf ne ko?” Ta fad’a tana kallon ta. Ameenatu ta girgiza kai kawai bata ce komai ba dan bata son ma maganar sa. Yaya tayi murmushi tace, “Yaushe yace ki koma?.”
“Baice ba, koda yace ma bazan koma a yanzu ba sai dai in da kan sa yazo, in kuwa bai zo ba a nan zan ta zama sai lokaci dana ga damar komawa. Ni wallahi bana so ma yazo gabad’aya haushi yake bani.”
Yaya tayi murmushi tace, “Kina tunanin bazai zo ba?.” Ta kalli Yaya tace, “Bazai zo ba Yaya, zan iya rantsewa akan Yusuf bazai zo nan ba.” Yaya tace, “Kar kiyi gaggawar rantsuwa ki bari ki gani in bai zo din ba, amma ni kuma nace miki zai zo.”
“Meyasa kike tunanin zai zo Yaya?.”
“Saboda zai zo din, ki rubuta ki ajjiye ko ba yanzu ba Allah Yusuf zai zo Ameena.” Ameena tace, “Yaya harda Allah?.” Tayi murmushi tace, “ni na fad’a miki hakan zata faru” ta fad’a tana tashi ta fita ta bita da kallo dan kawai Jin ta take yi amma ita tana da tabbaci akan Yusuf bazai zo ba.
Kwanan Ameena uku a Bauchi hankalin ta ya kwanta sosai bata da wata damuwa tun ranar da sukayi waya dashi basu sauke yi ba ta tattara ta ajjiye shi a gefe ta kama addu’a ta zamar mata makamin yak’ar damuwar ta. Ranar da ta cika kwana na ukun suna zaune da safe duk su Hidaya sun tafi makaranta sai Amira kawai suka gama rubuta waec sai kuma Daddy da bai je ba, Zaytun tana hannun hannun Amira suna yin game a waya dan yadda Zaytun take yin game din mamaki yake bawa Amira. Yaya ta kalli Zaytun tace, “Zaytun dai babu ruwan ta ko neman nono bata yi. Indai akwai game zatayi zaman ta babu Rigima.”
Ameena tace, “Ai yau na yaye ta ma ni.” Yaya ta kalle ta da mamaki tace, “Kin yaye ta fa kika ce?.” Tayi dariya tace, “Eh mana, shekara biyu take fa ai ta isa yaye, kuma tana cin abinci ga magana a bakin ta, yanzu kinga duk abinda kayi a gidan nan sai ta bada labari, in tayi wani abun Wallahi kamar y’ar shekara hud’u daman kuma yau da niyar hakan na tashi.”
“To kuma haka ake yayen ko d’an rubutu na kuka ba’a yi mata ba?.”
“Basai anyi mata ba Yaya ba kukan da zatayi, na gaji wallahi shayarwar ita take sake ramar dani. Kuma dmaan tayi girma da shan nono.”
Yaya tayi dariya tace, “To Allah ya bata hak’uri da dangana.” Itama Ameena dariya tayi tace, “Sai kace wacce aka yiwa mutuwa.” Yaya tace, “Badan nisa ba ai dana karb’e ta yayen in ta kwana biyu a wajena sai ta dawo, to gari ba kusa ba kuma baban ta ma bazai bani ba.” Ameena tayi murmushi kawai bata ce komai ba dan tasan kuwa babu inda zai bar Zaytun taje yafi so Kullum ya dinga ganin ta a kusa dashi.
Daddy ne ya shigo a guje yana fad’in, “Aunty Ameena ga Daddyn Zaytun a waje yazo.” Gaban Ameena ya yanke ya fad’i ta kalli Yaya taga tayi murmushi alamun daman na fad’a miki Ameena ta kalli Daddy tace, “Daddy da gaske kake?.”
“Eh Aunty, yace nazo na fad’a muku ne.” Yaya ta kalle shi tace, “Jeka kace ya shigo, Amira mik’o min mayafina.” Tsam Ameena ta mik’e ta shiga d’aki ta barsu a tsakar gidan dan jin zuciyar ta take yi wani iri kamar tana farin cikin zuwan sa kamar kuma bata yi ta kasa tantance a wanne ma’auni zata saka yanayin da take ciki.
Tana Jin sallamar sa da gaisawar su da Yaya tana ji tayi banza zuciyar ta nayi mata d’aci ga bugawa da take yi da gudu.
“Ameena! Kizo fa” ta jiyo muryar Yaya tana kwala mata kira ta runtse idanu ta sauke numfashi ta tashi ta fito. Tana fitowa suka had’a ido da yake yana zaune yana facing din d’akin da ta fito dukkan su sai da zuciyar su ta buga ta d’auke kai ta ‘karasa ta zauna Zaytun na cinyar sa tace, “Barka da zuwa.” D’auke kai yayi shima daga kallon ta yace, “Barkan ki dai.”
Amira da Daddy suka shiga d’aki hakan ya saka Yusuf ya kalli Yaya yace, “Yaya ayi hak’uri da abinda ya faru in sha Allah baza’a maimaita ba, nazo a bani ita mu koma Kano.” Yaya tayi murmushi tace, “Babu komai Yusuf, zaman aure a ko yaushe zo mu zaune ne kuma zo mu sab’a. Allah ya baka ikon rike amanar da mahaifinta ya baka. Yusuf Ameena amana ce a hannun ka ni nasan kasan da hakan, koda mahaifin mu mai bata amanar ta ba kafin ya rasu ita amana ce domin daga gaban magabatan ta ka d’auke ta ka kai ta gidan ka, Yusuf hakkin kula da Ameena yana wajan ka kai Allah ya d’orawa, ko kuka Ameena tayi Allah sai ya tambaye ka, gata kuma marainiya bata da uwa bata da uba kaine uwa da uban ta. Dan Allah Yusuf ka rik’e ta hannu biyu kar ka wulak’anta Ameena. Kana sonta tana sonka dalilin da ya saka akayi auren ku kenan, dan Allah kar ku Bari wani abu yayi tasiri a cikin rayuwar auren ku.”
Yusuf yayi shiru yana jin mai take cewa kafin yace, “İn sha Allah Yaya zanyi iya bakin kokarina” ya fad’a jiki a sanyaye sosai yana kallon Ameena ta k’asan ido. Yaya ta kalli Ameena tace, “Ameena ki tashi ki shirya ku tafi.” Bata iya yiwa Yaya musu dole ta mik’e ta shiga ta tattara kayan ta dana Zaytun tana jiyo maganar sa shida Yaya ta zuba a jaka Amira ta d’auko mata jakar suka fito.