← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 42

Sashe 19

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Kinga sai na biya ki ma, duk kwana d’aya naira dubu dari._ abinda ya fad’o mata kenan ta sake kulle ido ta bud’e a bayyane tace, “Daman yasan akwai hakkina a kansa ne har yake wannan maganar? Daman duk abinda yake yi yana sane kenan tunda Gashi yanzu yazo ya tambaya da kansa da yake so yake yi.” Kasa cigaba da magana tayi ta dafe kanta kawai ba tare da ta motsa ba.
Tana ji wayar ta na neman d’auki amma bazata iya d’auka ba har ta katse aka sake kira amma bata kalle ta ba sai ma kwanciyar da tayi a kan gadon kirjin ta na sama da k’asa.

A b’angaren Yusuf koda ya fita kai tsaye b’angaren amarya ya nufa yaga takalma a bakin ‘kofa alamun tayi bak’i kafin ya jiyo muryar Yayar ta Fauziyya tana fad’in, “ai in ta kwantar da hankalin ta da zaman Lafiya kika zo gidan dan nan Asiya, ni wallahi na d’auka ma itace zata kawo muku abinci kasancewar ki ta amarya. Amma kar ki damu kedai ki girmamata abinda Umma ta seke cewa na fad’a miki kenan domin matar mijin kice gaba take dake.”

Ja yayi ya tsaya yana so yaji mai Asiyan zata ce yaji Tce, “Wallahi ni da zuciya d’aya na d’auke ta kamar Yayata ne, bana jin zan mata kallon kishiya dan duk abinda akace na my love ne bazan yi masa koda kallon banza ba balle kuma ace matar sace, itace kawai nake ganin bata son zaman Lafiya amma in sha Allah zata canja itama. Nidai daga wajena baza’a samu matsala ba in sha Allah.” Murmushi yayi jin abinda tace hakan yana daga cikin dalilin da soyayyar ta take sake ninkuwa a zuciyar sa domin ya fahimci tana son zaman Lafiya bata zo dan tashin hankali ba.

Da sallama ya shiga ganin sa sai sukayi shiru Fauziyya tace, “Ango barka da rana.” Yayi murmushi yace, “Barkan ku, ya gajiyar hidima?.” Momi tace, “Alhamdulillah duk Mun ware ai.” Baice komai ba sai murmushi ya hau saman suka Bishi da kallo.

Fauzy tayi dariya tace, “Da alama tarkon mu ya kama, tashi kije saman kiji abinda zai ce ga abinci nan ki kai masa mu kafin ki sakko mun wuce.” Tashi tsaye tayi sai kuma Fauziyya tace, “ke zan d’ibarwa Umma madarar can zan tafi da ita, in ta kama ma harda milo.” Asiya tace, “to kar ki d’iba da yawa kinga dai yau aka bud’a kar a gane.”
“In ma an gane sai me? Dan ke aka kawo ai, ni zan d’auki indomie biyu in naje gida na dafa na ci” Ta fad’a tana yin hanyar wajan madarar ita kuma ta d’auki abincin zuwa saman.

A falon ta same shi a zaune yana gano ta ya tashi ya karb’i abincin ya ajjiye ta zauna itama yace, “Meyasa bari nazo na Karb’ar miki ba?.” Zama tayi tace, “Yanzu ka dawo fa.”
“Ke kika dafa?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “Fauzy ce, badan ita ba ai ni bazan iya girki ba. Kaina ciwo yake sai da nasha magani.”

“Sannu kinji, amma Yanzu babu ciwon?.” Ta d’aga kai alamun babu tace, “Kaci to.” Bai musa ba ya fara ci d’in dan ko karyawa ma baiyi ba yace, “In na gama sai mu shirya kayan da zamu tafi, zuwa karfe biyar zamu wuce.” Nan take tayi dariya tace, “To.” Abincin yaci bayan ya gama kamar yadda yace suka shiga d’aki tare suka shirya kaya daman ya tawo da kayan sa daga b’angaren Ameena bayan sallar la’asar yace mata yana zuwa ya koma b’angaren Ameena ya samu ta kulle k’ofa ya tambayi Amira tace ai tace kar a deme ta bacci zatayi baice komai ba ya juya ya sauka suka shiga mota fita daga gidan.

Ameena duk tana kallon su tana daga tsaye a window sai a sannan taga Asiya d’in duk da bata ga fuskar ta sosai ba sai bayan ta babu laifi tana da kyau duk da bata da haske a kan idanun ta suka fita daga gidan ta dawo da baya ta zauna a gefen gado ta rasa wanne irin tunani ma zatayi.

Tun bayan da Yusuf da Asiya suka tafi bai Kira ta a waya ba itama bata neme shi ba har suka kwashe kwanaki biyar a can, ta tattara ta ajjiye shi a gefe ta kama addu’a da kuma shawarar Yayar ta da k’awayen ta a haka take komai duk da babu kuzari a tare da ita gashi ta rame amma tayi k’ok’arin ajjiye damuwar Yusuf ta sake sosai Kullum cikin hira suke da Amira bata ware kanta dan tana Gudun tunani. Ranar da suka kwana shida basa nan tana zaune a falon k’asa da daddare suna kallon dadin kowa a tv ita da Amira da Zaytun da take wasa akayi sallama aka shigo falon.

Amsawa tayi tana kallon wacce ta shigo taga Humayrah ce bayan ta kuma Amma ce ta mik’e da farin ciki tana fad’in, “Amma barka da zuwa.” Kallon ta take yi ganin ta rame sosai sai haske da ta sake yi hakan ya d’aga mata hankali sai kuma tayi tunanin ko ciki ne da ita shiyasa ta rame ya saka ta haske.

Ammah ta zauna Ameena ta zauna a kan carport tace, “Amma barka da zuwa.” Amma tace, “Barka dai Ameena, na same ki Lafiya duk da naga kin rame?.” Ameena ta murmusa tace, “Alhamdulillah, Amira kawowa Ammah ruwa.”
“A’a Amira yi zaman ki hanya ce ta biyo dani nace bara nazo na ganki, sai kuma naga kin sake ramewa Ina fatan Lafiya dai?.” Ameena tayi murmushi tace, “Lafiya lau Ammah.” Jjn hakan sai Ammah ta saka a ranta ciki ne da Ameena, Zaytun tayo wajan Ammah ta zauna a kan cinyar ta Ammah tace, “Takwara mai kika ajjiye min?.” Dariya akwai Zaytun take yi itama Amman tayi tana yi mata wasa.

Humayra tace, “Gobe Yaya Yusuf din zai dawo ko?.”
Ammah ta kalli Ameena tace, “Kwana nawa zasu yi ne?.” Ameena tace, “saati biyu dai yace min kafin su tafi, amma ban sani ba ko ya canja lokaci.” Amma jin hakan sai ta girgiza kai kafin tace, “Tunda yace miki hakan ai hakan ne, Allah ya dawo dasu Lafiya. Sai ke kadai a gidan.” Ameena tayi dariya tace, “da Amira ai Ammah shiyasa zaman baya damuna.” Ammah tace, “Haka ne, Humaira tashi mu koma” ta fad’a tana tashi tsaye.

Ameena ta mike itama tace, “Ammah da wuri haka?, ko abinci baki ci ba.” Ammah tace, “Dare yayi gwara mu koma.” Har bakin mota suka raka Ammah Humaira taja suka tafi itama ta koma ciki.

Ran a Amma a b’ace ta koma gıda tana komawa kai tsaye b’angaren mahaifin su ta wuce ta same shi a tsaye yana amsawa waya a d’aki ta zauna tana jira ya gama ta zayyane masa abinda yake bakin ta, bai jima ba ya gama ya kalle ya yace, “Ina ta kiran number Yusuf bana samu Ina so ya tawo min da turare a makka ko ya dawo ne?.” Ammah tace, “maganar sa nazo muyi, nida kai ba ce mana yayi sati d’aya zaiyi ya dawo ba?.”

Abbah ya zauna yana kallon ta kana yace, “kwana shida yace zuwa sati d’aya, to ai ma yau ko gobe ya kamata ace ya dawo saboda matar sa ta gıda.” Ammah ta girgiza kai tace, “To daman ba hakan yayi niyar yi ba, domin kuwa sati biyu ya cewa Ameena zasu yi kaga kenan daman haka yake son yi ya fad’a mana ne dan kar mu dakatar dashi.” Abbah da mamaki yace, “sati biyu? Shi yanzu dan bashi da hankali sai ya tafi yayi sati biyu uwar gidan sa fa?.”
“Saboda ya raina hakkın ta mana yana ganin ba komai bane, baka ga yadda yarinyar ta rame ta yanayin maganar ta ma zai nuna maka ko waya basa yi. Daman abinda ya kaini kenan na kuma tambaya ta fad’a min.”

Abbah baice komai ba ya fara kiran lambar Yusuf amma bata tafiya Ammah tace, “bafa zata shiga ba na tabbata da biyu yayi hakan saboda kar a same shi ayi masa fad’a, har ta WhatsApp nayi magana amma bata tafiya. İn bayan ya dawo aka yi masa fad’a ai kaga daga baya ne tunda ya riga ya aikata.”
“Anya yaron nan baya shaye-shaye?.”
“Ba wani shaye-shaye iskanci ne kawai wallahi dan yaga tana hakuri da lamarin sa, inda ace tana da iyaye ai bazai mata haka ba dan baza su kyale shi ba.”

Abbah yace, “kuma ni shaida ne yana son ta kafin ya aure ta, amma meyasa ya canja haka lokaci d’aya?. Ka yiwa yarinya kishiya kuma ka tafi ka barta kai da amarya da shirme da rashin sanin ciwon kai?.” Ammah bata iya cewa komai ba saboda takaici tayi shiru Abbah ya kuma cewa, “Laifina ne ma dana amince masa da tafiyar da sai nace masa in bazai tafi da ita ba ya hak’ura, ban San zai bani kunya har haka ba.” Ammah tace, “inda nice na hana ai sai kace wani abun gashi kai da kanka ka fad’a.”

Abbah yace, “in ya dawo zai gane kuskuren sa dan bai kyauta ba sam.” Ammah tace, “Daga baya kenan ai tunda yayi.” Abbah yace, “Wato ko anyi masa fad’an a banza kenan.” bata sake cewa komai ba ta tashi kawai ta fita dan a ganin ta kawai Yusuf ya raina su ne.

Tsahon kwana sha uku kenan su Yusuf basa nan a safiyar na sha hud’un suka sauka a Nigeria kai tsaye aka d’auko su zuwa gida, Ameena bata ma San sun dawo ba tana zaune a falo taje asibiti ta dawo bata shiga dak’i bama balle ma taji ‘karar mota. Koda ta tashi ma alwala kawai tayi tare da yin sallar azahar sai a sannan ta shiga d’akin.
Chapter 19 · 0% Book details