Sashe 37
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah yace, "Zai yi mana, Mubarak shiga ciki ka kira Ammah da yayar ku ta Abuja tunda tazo har Humairah ma tazo" ya fad'a yana kallon k’anin Yusuf. Ba musu ya tashi ya shiga ciki suka dawo tare da Ammah da Yayan Abuja da kuma Humaira d’in. Ammah tana ganin sa tace, “A’a wannan kamar Adam yayan Ameena ko?” Ta fad’a zama tana kallon sa. Yayi murmushi yace, “Ni ne Hajiya, barka da dare.”
“Barka dai, an dawo lafiya?.”
“Lafiya lau, na same ku lafiya.”
“Lafiya lau, mutanen gidan lafiya.” Ya amsa da komai lafiya yana murmushi.
Abbah ya kalle shi yace, "to Adam muna jin ka, Allah yasa lafiya dai." Yaya Adam ya gyara zaman sa sannan yace, "Gaskiya Alhaji ba lafiya ba."
"To me ya faru?."
Ya kalli Yusuf ya kalli Abbah yace, "Shekaran jiya na dawo daga garin Abia sallar magriba nayi da i'sha kawai na kasa hak’uri nace sai naje naga Ameena saboda kwana biyu in muna waya sai na ji yanayin ta kamar mara lafiya in na tambaya tace babu komai, ina shiga gidan na tarar da y’ar k’anwata Amira da take wajan ta da y’arAmina din suna zaune suna kuka tare, hankalina ya tashi ma d’auka ko wani abun ne ya samu Ameena na tambaya aka tana sama na hau saman da kaina."
Yayi shiru ya sake gyara zama kafin yace, "Wato abinda na gani yafi komai d’aga min hankali, domin zuwa nayi na tarar da Yusuf yana marin Ameena har tana cewa wallahi na gaji da dukana da kake yi nan gaba nima zan rama, hakan sai ya bani tabbacin kenan ba iya ranar Yusuf ya saba dukan Ameena ba. Sai kuma naji yana ce mata b’arauniya wacce ta sace masa sark’ar gold da kuma kud’i. Ita kuma Ameena take ce masa in baya sonta ya sake ta mana yace daman shi ai ba son ta yake ba, yana zaune da iya ne saboda mahaifiyar sace ta nuna tana son ya auro ta amma badan so ba" yayi shiru yana kallon yanayin kowa a cikin su dukkan su an rasa mai motsin kirki a jikin su kowa ya sauraron sa yake yi.
Ya cigaba da cewa, "Yusuf yana cewa Ameena yanzu ya samo wacce yake so kuma ta fita a wajan sa daman ita zama da ita alfarmar Maman sa ce. Hankalina ya tashi sosai a nan take nace Ameena da Amira su tattaro kayan su mu wuce gıda tunda bayan sonta bazata zauna dashi ba, tunda a kan idanuna na gani yana dukan ta dan na jima a tsaye a wajan ina kallon su basu San naje wajan ba. Da har nace ta bar masa y’ar sa ma to ganin yarinyar na kuka ne ya saka muka tafi da ita a wannan lokacin itama kuma Ameena baza ta ji dad’i ba.”
Yaya Adam ya sake cewa, "A daren muka wuce asibiti saboda jikin ta yayi zafi sosai in ta tsaya jiri d'aukar ta yake yi tsayuwa ta gagare ta. Muka je asibitin da take ganin wata likita Dr Mansura, bayanin da likitan tayi min shine yafi komai d'aga min hankali domin kuwa abinda na gani a gidan ba komai bane akan abinda naji, dan ta tabbatar min da Ameena na cikin damuwa matuk’ata tun ba yanzu ba" sai yayi shiru ya d’auko wayar sa yace, "gata ma tana kirana zata shigo tayi miki bayanin komai, nafi so kuji komai daga bakin ta kamar yadda naji" ya fad'a yana amsa wayar aka ce ta shigo.
Da yake falon shine na farko a gidan shi zaka fara tararwa Dr mansura ta shigo da sallama suka amsa ta gaishe su Yaya Adam yace, "Dr ki yi musu irin bayanin da kika yin min akan Ameena."
Dr tace, "Sunana Dr mansura ina aiki da asibitin Aminu kano sannan ina aiki da Silver clinic wanda a nan ne Ameena ta sanni. Tun farkon auren ta ni mijin ta yake kawowa ita in bata da lafiya, abinda ya shafi cikin ta har ta haihu nice nayi komai mun saba da ita sosai ya zama bata da wata likita sai ni.”
"Ameena tana zuwa wajena da damuwa sosai, in na duba ta ina ganin jinin ta ya hau sai nak’i bata magani saboda a shekarun ta bai kamata ace an d’ora ta akan magani ba; dan shi maganin hawan jini in ka fara sha baka dainawa har abada sai dai ka rage. hakan ya saka nake bata shawara akan saka damuwa a ranta duk dan saboda bana son bata magani amma abin sai da yaci tura da kaina na d’ora ta akan magani saboda zuwa lokacin hawan jini ya kama Ameena shawara bazata yi mata aiki ba sai dai magani."
Shiru tayi ta d’auko magungunan ta nuna musu tace, "wannan shine maganin da Ameena take sha duk sati biyu take shnaye wannan kwalin sai tazo wajena na sake auna bp d’in ta na gani ko zata rage ya zama tana sha duk sati hud’u amma jinin ta bai tab'a sauka ba dole a haka zance tashs na sati biyun. Sai kuma wannan maganin" ta fad'a tana sake d’auko wani ta nuna musu tace, "kafin nace komai dan Allah a nan akwai wanda yasan magani ko yake karanta b’angaren lafiya?."
Humaira ta kalle ta tace, "I’m a pharmacists ina level three a yanzu haka." Mansura tace, "good, karb’i maganin nan ki duba min kiga meye amfanin sa a jikin maza da mata, nasan ko baki San shi ba matsayin ki na pharmacists zaki san amfanin chemical d’in da akayi amfani dasu wajan had’a shi.” Ba musu ta karb’a ta bud’e ciki ta d’auko takardar da ake sakawa tana karantawa kafin ta d’ago tace, "A yadda na fahimta magani ne kamar na kwantar da sha'awa, ana bawa wanda suka jima babu aure kuma suna fama da matsananciyar sha'awa ko abinda yayi kama da haka. Haka dai nake tunanin amfanin sa.”
Dr Mansura tace, "kin san aikin ki. Abinda kika fad’a haka ne bawai a fahimtar ki bane. Wato Ameena ta jima tana shan wannan maganin, shima tun ban bata ba in ta kira ni na bata shawara nace kar ta sha komai har ya zamana da kaina na bata saboda tsoron kar ta fad’a halaka. In na tambaye ta sai tace min mijin ta baya zaman Kano kullum baya k’asar , nace mata Ameena ki sanar a gida a d’auki mataki ko ya dinga tafiya dake ko kuma ya daina zuwa ai hakkın kine, sai tayi dariya kawai bata ce min komai. Sau da dama nakan yi tunanin zuwa gidan nan saboda Ameena, dan ban san kowa nata ba iya Yusuf na sani a tare da ita da y'an uwanta zan fad’awa dan zasu fi mayar da hankali Akan matsalar."
"A kalla Ameena tasha kwalin maganin na ya kai goma, yanzu zancen da nake muku maganin yana gab da daina yi mata aiki saboda yawan da yayi a jikin ta ko nace ma ya daina sai dai a bata wanda ya fishi k’arfi. Dalilin da yasa na amince da zuwa nan kamar yadda Yayan ta yace saboda Ina so a kawo k’arshen damuwar Ameena, tayi kankanta da d’aukar wannan condition din, in kuma ba haka ba zuciyar ta zata iya samun matsala sannan zata iya fad’awa harkar lesbian ko kuma neman maza. Babu jini da ya had’a ni da Ameena amma ina jin ta kamar k’anwata Ina tausayin ta sosai shiyasa na amince nazo nan dan ayi maganin abun kafin ya yi mata illa. A yadda suka kaita asibiti shekaran jiya tsaf zata iya kamuwa da ciwon shanyewar b’arin jiki dan jinin ta ya hau fiye da lokacin baya. Tana buk’atar kwantar da hankali da kuma da kuma rarrashi gaskiya."
Yaya Adam da yake jin ta ya yake kuma kallon ta jin taje k’arshe ya saka yace, "Dr na gode sosai da abinda kika yi min, Allah ya kiyaye hanya, zan shigo asibitin gobe." Tayi murmushi tace, “Babu komai, nima Ameena k’anwa ce a wajena zan tsaya mata a ko ina dan ganin ta samu sassaucin abinda yake zuciyar. Sai anjima” ta fad’a tana saka takalmin ta ta fita.
Yaya Adam ya bisu da kallo har lokacin an rasa mai magana yace, "Har mahaifinta ya rasu bashi da hawan jini, har mahaifiyarta ta bar duniya bata da hawan jini, ni da nake matsayin uba wajan ta a yanzu bani da hawan jini, a cikin mutanen dake wajan nan bana jin akwai mai hawan jini. Ta dalilin Yusuf Ameena ta samu hawan jini har kuma take shan maganin da zai kawo mata mafita a duk sanda take cikin bukatar mijin ta, hakan yana nufin bata samun abinda take so baya sauke hakkin ta da Allah ya d’ora masa sama da kwanaki masu yawa. Dan in muka yi duba da yawan kwalayen maganin da likita ta fad’a tasha ta jima bata samu abinda take so ba a wajan Yusuf. Da kuma ta fad’a harkar neman mata ko neman maza yace bazai zauna da fasik’a ba."
Falon yayi shiru babu wanda yake magana sai Amma da take goge idanun ta haka Humaira kuka suke yi sosai saboda tausayin Ameena basu d’auka abin har ya kai ga haka ba ya sake cewa, "An sanar dani k’arfe sha d’aya na dare ta dauki mota ta fita saboda abinda yayi mata a ranar taji bazata iya kwana a gidan ba, Allah ne kad’ai yasan me yayi mata a ranar ta bar gidan a wannan daren, rasa inda zata je da kuma damuwa ya saka ta fakawa a titi har kuka zo kuka tafi da gidan gidan ka haka ne?." Ya fad'a yana kallon Abie. Abie ya girgiza kai yace, "haka ne, tabbas anyi haka nima nayi mamakin fitowa ta a wannan lokacin. Dan washe gari da Yusuf din yazo na masa fad’a sosai yace min bazata sake faruwa ba in sha Allah.”