Sashe 27
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har sun wuce a keke napep sai taga keken ya dawo da baya bata kalli wanda yake ciki ba dan a tsorace take sosai mai napep din yace, "Shiga muje." Ta kalle shi da mamaki tace, "Ban tsayar da kai ba ai, kuma bana shiga napep da namiji a ciki ka gane?." Ganin da fad'a take magana ya saka Ibrahim da yake baya ya murmusa yace, "Sannu Rukayya, ni nace a dawo baya saboda tun d'azu na wuce na ganki a tsaye ga dare yanayi."
Jin muryar Ibrahim ya saka ta kalle shi sai tayi murmushi tace, "lahhhh! yi hak'uri ban ma kula da kai ba, Ina wuni."
"Shigo ciki dare yayi ana neman ki a gida nasan da hakan." Kulle ido tayi ta bud'e suka had'a ido ta sauke numfashi ya fuskaci tunanin shiga take yi sai yace, "mu tafi ne?."
Da sauri ta shiga baya kusa dashi ta zauna, Allah yasa ma shi kad'ai ne akwai space sosai a tsakiya dan ba jiki ne da ita ba shima haka, a lokacin wayar ta take k'ara ta samu damar daukowa taga sunan Fiddausi yana yawo a kai a fusace ta d'auka tace, "Wai Fidy bashi kika bani ne da zaki ishe ni da waya?." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tace, "To bana gida yanzu haka Ina kan hanyar dawowa, gobe da sassafe zan shigo mayi magana. Duk kin wani d'aga hankalin ki kamar auren fari sai......." Cak maganar ta tsaya jin Ibrahim yana cewa mai napep din, "Ka fara sauke ta a Yakasai sai mu wuce."
Juyowa tayi ta kalle shi taga hankalin sa yana wajan ta gabad'aya, sam ta manta ma tare suke wallahi da bazata d'auki wayar Fiddausi ba, datse kiran tayi ta saka wayar a jaka sannan tace, "Na gode sosai." Sai a sannan ya kalle ta baice komai ba ya d'auke kansa. A haka suka isa Yakasai har kofar gida aka sauke Rukayya ta fita ta kalle shi tace, "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci."
Ya amsa da fadin, "Kar ki damu, ki gaida gida" yana fad'a mai napep din ya juya suka bar wajan ta bi napep din da kallo ita gabad'aya tausayin sa ma take ji wallahi. A haka ta juya ta shiga gida jikin ta duk ya mutu daman gashi ta gaji sosai.
Tana shiga Umma ta tashi tsaye tace, "Ina kika shiga ne haka? Ana ta kiran waya bakya d'auka yanzu da baban ku ya dawo nace masa ni na aike ki har yanzu baki dawo ba?." Jin bai dawo ba sai taji dadi ta zauna tace, "Wallahi babu abin hawa ne na jima a tsaye a kan titi, yanzu ma badan tsohon mijin Fiddausi ba ban san ya zanyi ba." Umma ta kalle ta tace, "shine ya dawo dake?."
"Eh, yana cikin napep har sun wuce ya dawo suka d'auko ni har nan aka ajjiye ni."
"A Ina ya sanki?."
Ta kalle ta tace, "Umma mijin Fiddausi fa nace miki, to ai ko babar sa ta sanni balle shi."
Umma tayi shiru tana kallon ta tace, "to ko dai sonki yake yi?." Rukayya ta juyar kai ta kalli Umman tace, "Umma tsohon mijin Fiddausi fa nace miki."
"Shi din fa, akwai aibu a hakan ne?." Rukayya ta mik'e tsaye tace, "Umma banyi sallar I'sha ba" ta fad'a tana shigewa d'aki zuciyar ta cike da mamakin wannan tunani na Umman ta.
Shima Ibrahim yana komawa gida sai da Hajiya ta tambaye shi Ina ya tsaya ya zauna yana cin abinci yace, "Yau bamu gama aikin da wuri ba kuma daman na fad'a miki na kai machine dina service a napep na dawo" Abincin yake ci Amir yazo ya zauna a cinyar sa yace, "Abba yaushe zamu koma gidan mu?." Ya kalli Amir din yana murmushi yace, "Gyara maka gidan ake yi ya zama mai kyau shiyasa kake zaune a nan da an gama zamu koma can."
Amir yace, "harda Mama na?." Ya daga masa kai alamun eh Amir yace, "Amma da naje wajan ta tace min bazata sake zama damu ba wai wani gidan zata je, kuma Abba kace min zamu kuma waye mai gaskiya?." Ibrahim ya kalli Hajiya da take kallon su ya sake kallon Amir yace, "Kana ji, kaje kayi bacci gobe juma'a zamu je masallaci tare." Sai kuwa ya mike yace, "Zaka siya min alewa?." Ibrahim yace, "eh harda chocolate ma, maza jeka kar ka makara sallah." A guje ya shiga d'aki yana murna shi kuma ya kalli abincin nan take yaji ya fita daga ransa ya ture abincin.
Hajiya da take kallon sa tace, "Ibrahim yaron nan yana son komawa gida wajan ka da babar sa, bai San babar sa tayi nisa ba amma yana bukatar wata uwar da zata kula dashi. Yana samun komai a nan amma cikin kwanakin nan yana so ya dinga ganin sa gidan su shima." Ibrahim ya kalli Hajiya yace, "Ya zanyi kenan Hajiya? Nida shi zamu koma gidan kenan?."
Ta girgiza kai alamun A'a tace, "Aure zaka yi Ibrahim, kana da dama a yanzu zaka iya yin aure dan Allah ya hore maka." Ibrahim ya gyara zaman sa yace, "Hajiya sam tunanin aure baya zuwa kaina a yanzu Allah ya sani, kwana nawa ma da rabuwar mu da Fiddausi da zanyi wani auren?."
"Kai in baka yi ba ai ita zatayi, na smau labarin auren ta za'a yi shi ne nan kusa ba jimawa."
"Ita daban ni daban Hajiya, abinda yake ranta kenan daman ni kuma yanzu ta neman halak nake yi."
Hajiya tace, "ka dai sake tunani yana da kyau kayi aure kofofin alkhairin ka zasu yi saurin bud'ewa, zama hakan ba shine mafita ba ko dan d'anka ya kamata kasan abinda zakayi" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki ya bita da kallo kafin ya mike shima ya fita zuciyar sa na ayyana masa taya zai fara tunanin aure yanzu? A Ina ma zai samo matar? Ta ina zai fara?.
Washe gari da safe Yusuf yana kwance a kan gadon Asiya dan bazai fita ba sai lokacin sallah yayi, tashi yayi ya 'karasa bak'in taga yana kallon tagar d'akin Ameena amma a kule take ya lumshe ido ya bud'e ya juya yana kallon d'akin da ya tashi, gabad'aya wani iri yake ji d'akin yana masa shi ba wari ba kuma ba khamshi ba Gashi kaca-kaca kayan ta wanda suka dawo daga saudia a jikin ta suna ajjiye a gefe a haka ma ta kwashe kayan da ta jibga a gefen gadon ta kai gidan su matsayin tsaraba.
Kasancewar su ta karshe ya tuna Shida Ameena ranar da ya mata wayo taje ta samu Ammah ya lumshe ido ya bude ya sauke numfashi a bayyane yace, "Komai nata daban yake." A lokacin Asiya ta fito daga wanka ta wuce shi ta fara shiryawa ya jiyo yana kallon ta. Kanta yake kallo gabad'aya kitson ya lalace ya tsufa yana buk'atar a gyara shi amma bai ji ma tana zance ba dan ya d'auka a jiya da taje gida zata yi komai kafin ta dawo amma sai yaga akasin hakan.
Yana tsaye ta d'auko brezia wacce ta saba sakawa zata saka sai ta kalle shi suka hada ido tace, "To ka daina kallona." Ya murmusa yace, "Ya kamata ki daina saka acuci mazan tunda kin riga kin cuci mazan ai ko?." Ta kwabe fuska tace, "me kake nufi?." Ya zauna a gefen gadon yace, "Abinda kika ji." Bata saka magana ba ta juya baya ta saka ta sake kallon sa taga ba ita yake kallon ba nan da nan t shirya ta cillar da towel din wankan da ya canja kala daga farı zuwa brown ta nufo wajan sa.
Ya kalle ta bayan ta zauna yace, "Kije a gyara miki kanki shima ki cire k'arin gashin." Tayi dariya tace, "Zanje. Yanzu me kake so Kaci?."
"Komai" ya bata amsa a takaice kafin ya sake tashi ya sake kallon window amma bai ga an bud'e ba duk da daman bata cika yawan bud'ewa ba.
Ta kalle shi ta kalli inda yake kallo tace, "Wai my love Ina motar tawa?." Bai kalle ta ba yace, "Anjima kadan za'a kawo miki." Tayi dariyar murna tace, "Na gode mijina mai sona. Na tambaye ka?."
"Ina ji."
"Wai dani da Ameena wa kafi so?." Ya juyo yana kallon ta cike da mamaki yace, "Meyasa kika tambaya?."
Tace, "Ina so na sani ne kawai." Yayi gaba ya sake zama yace, "Dukkan ku Ina son ku babu wacce nafi so a ciki." Nan da nan fuskar ta ta had'e tace, "Amma ai a baya ba haka kace min ba, kace kafi sona akan Ameena , kace dani ka aura baza ka sake wani auren ba." Kallon ta yake yi fuskar sa a dan sake a ransa yace, _a hakan kina fama da k'azantar bazan sake aure ba?._ a bayyane kuma yace, "Lokacin ma wasa nake miki."
Asiya tace, "Wasa kuma? Ai ba sau d'aya kace ba balle kace wasa kake min." Ya tashi tsaye yace, "to na fad'a ne a lokacin dan kiji dad'i kuma kin ji ai shikenan ko?." Asiya tace, "Yanzu hakan yana nufin kafi son ta dani kenan?."
"Ni bance miki ba, amma ko wacce Ina sonta."
"Amma meyasa dah ka fad'a min hakan?."
"Y'an siyasa meye basa fad'a a lokacin da suke neman mulki? In suka samu kujerar suna yi ne?."
"Shiyasa daban ai aure daban, kuma kaine ka fad'a a da meyasa yanzu ka mu sa?."
Yayi murmushi wani lokacin kuruciya tana damun yarinyar nan yaga alama hakan a tare da ita ya saka yace, "Kin tab'a ganin dan siyasar da ya cigaba da campaign bayan yaci zab'e?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "To ki saka ranki haka ne abun" ya fad'a yana fita ya barta a wajan a tsaye dan dakyar yake shak'ar numfashi saboda yarin da d'akin yake yi.
#Mai daki
#Book2
#Nana Haleema
#Paid
#500
#09030398006.
Book2
018