Sashe 21
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammah tace, “Kar ma tazo mana Yusuf kai ka damu da ita bani ba, sai da safe ka gaishe da takwara” ta fad’a tana tashi ta shiga ciki. Abbah ya kalle shi yace, “Fushi tayi dakai shiyasa bata yi maka maganar Ameena ba, ta gaji da yi kullum abu d’aya, tun ina ganin kamar son da take yiwa yarinyar ne ya jawo hakan har na fahimci laifin kane. Na tambaye ka.” Ya kalli Abbah yace, “Ina ji Abbah.”
“Kana son yarinyar nan lokacin da ka aure ta?.” Ya kalli Abbah ya sunkuyar da kai yace, “Abbah wannan duk bai tashi ba in sha Allah baza’a sake ba.”
“Haka kake cewa ai koda yaushe, da Ina zargin ko ka fara shaye-shaye ne amma yanzu na tabbatar iskanci ne kawai.”
Shiru nan ma yayi baice komai ba kafin Abbah yace, “ka aiko min da sark’ar dana baka ajiya tare da kud’in da ka kawo anjima zasu zo a karb’i kudin.” Ya daga kai alamun to Abbah ya tashi ya d’auki jakar shima ya shiga ciki ya bashi waje. Yusuf ya jima a zaune a wajan yana tunani sannan ya tashi ya fita ya nufi gida.
B’angaren Asiya ya shiga tun daga falo k’arnin kwai ne yake tashi ya d’an yamutsa fuska ya shiga ciki sosai a nan yaji ai k’arnin daga kitchen yake fitowa. Shiga kitchen d’in yayi ya ganshi kaca-kaca anyi girki a bar komai a inda yake babu abinda aka d’auke. Yana shirin yi mata magana yaga ta sakko ya bita da kallo domin tun kayan da suka dawo ne a jikin ta bata canja ba tace, “Sallah nayi yanzu zan gyara wajan.” Baice komai ba ya huce ta ya hau saman ta bishi da kallo ta kalli kitchen din a bayyane tace, “A nan fa za’a samu matsala dani gaskiya wallahi, ba komai nake lalatawa na gyara ba. ta fad’a tana fara gyara wa zuciyar ta duk babu dadi.
Ta jima kafin ta gama a lokacin ya sakko har lokacin yana jin k’arnin amma ba kamar d’azu ba ya kalle ta yace, “Ina abincin?.”D’aukowa tayi tazo ta ajjiye a kan center table tace, “kayi hak’uri my love in sha Allah bazan sake abinda nayi ba d’azu” ta fad’a tana zubewa akan carpet tana zuba masa abincin.
Karb’a yayi data gama yace, “Zaki iya kwana ke kad’ai ne?.” Ta girgiza kai tace, “A’a Momi tazo ai ta hau sama dakina wanka take.” Kai ya girgiza kawai ya kai abincin bakin sa amma k’arni ya hana shi zubawa a cikin bakin. Ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin ta zuba masa ido hakan ya saka shi zubawa a bakin yana taunawa.
A baki akwai taste sosai amma k’arni bazai barka kaji dad’in sa yadda kake so ba, ajjiye plate din yayi yasha ruwa ya kalle ta itama shi take kallo tace, “Badai ka gama ci ba?.” Yadda tayi maganar da shagwab’a ya saka shi yin murmushi yace, “in na dawo daga tafiya bana iya cin abinci daman na karb’a ne dan naci girkin amaryata kuma sannan dan na tabbatar ta cika umarnina, Allah ya taimake ki abinci kuma yayi dadi.” Murmushi tayi cikin jin dadi ta kalle shi tace, “Har naji dad’i, da farko n d’auka bai dadi bane.”
“Yayi dadi sosai amma bai kai ki” ya fad’a yana daga mata gira d’aya.
Dariya tayi sai kuma ta had’e fuska kamar zatayi kuka ta kalle shi shima ita yake kallo yace, “Meye kuma? Taso Kizo” ya fad’a yana yafito ta da hannu ta taso ta dawo kusa dashi din tana sake narkewa.
D’an baya yayi da fuskar sa jin yanayin jikin ta khamshin sai a hankali amma ya daure bai ce komai a akai na yace mata, “Meye na kukan?.” Asiya ta kwanta a jikin sa tace, “Na saba kwana a jikin ka my love, yau sai nake ji zuciyata ta cika da kewar ka dan nasan yanzu zaka tafi wajan Aunty.”
Murmushi yayi yace, “Ni kaina zanyi kewar ki sosai.”
“Ba wani kewata da zaka yi, bayan zaka samu matar ka ni wa zan samu?.”
“Ki saka a zuciyar ki Muna tare, kuma gangar jikin mu ce bata waje d’aya amma zuciyar mu a had’e take.” Kai ta girgiza cikin gamsuwa tace, “Aunty tana da kirki sosai kaga yadda muka gaisa d’azu kamar mun saba.”
Murmushi kawai yayi bai ce komai ba tace, “zanje gobe na rok’o alfarma a bani Zaytun mu kwana tare.” Ya mata kiss a goshi yace, “Sai kinzo” ya fad’a tana tashi tsaye dan abinda jikin ta yake fitarwa san baya mata dad’i. Itama mik’ewa tayi tace, “Zanyi kewar ka my love.” Shima ya ja kumatun ta yace, “Nima zanyi kewar ki, ki kulle gidan sai da safe” ya fad’a yana fita ta biyo shi har ya shiga sannan ta koma.
Khamshi ya daki hancin sa tun daga falo a lokacin yaja numfashi cikin jin dad’i a ransa yana fad’in,_Ameena sarkin khamshi._ abinci ya tarar akan dining yana kallon abincin ya jiyo sautin sakkowar ta daga sama ya d’aga kai yana kallon ta tayi masa kyau cikin material d’inkin riga da siket rigar har guiwa kuma mai fad’i sosai. Ganin yana kallon ta sosai sai tace, “Sannu da zuwa.”
“Yauwa” ya amsa yana zama a akan dining kafin yace, “Allah yasa anyi girkin dani.” Ta k’araso wajan tace, “Bani na dafa bama Amira ce.”
Da wata irin murya ya kalle ta yace, “girkin Amira zanci?.” Ta kalle shi itama tace, “Sai na dafa maka in kana so.” Ya girgiza kai ya bud’e abincin yace, “Zuba min kawai, sun dawo ne?.” Ameena ta fara zuba masa tace, “Eh sun dawo suna sama.” Abincin da ta zuba ya fara ci ta juya zata bar wajan ya rik’o hannun ta ta kalli hannun ta kalle shi yace, “ki dawo ki zauna na gama.” Ba musu ta zauna yana cin abincin ya kalle ta yace, “Baza ki ci ba?.”
Kai ta girgiza kawai alamun A’a ya tashi daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna yace, “bud’e bakin ki na baki, zama da yunwa ne yake saka ki rama haka.” Ta kalle shi tace, “Bana jin yunwa fa.”
“Sai kin ci.” Kallon sa take taga alamun shiri yake nema sa ita, ita kuma bata shiryawa hakan ba sannan kuma ba tasan magana hakan ya saka ta bud’e baki ya fara zuba mata abincin tana ci.
Babu mai magana cikin su sai k’arar cokalin da yake ci, sau uku ya bata kawai ta girgiza kai tace, “na koshi fa.” Cigaba da ci yayi har ya cinye ya tashi har zai hau sama sai ya juyo yace, “Ina jiran ki.” Da kallo ta bishi kawai dan tasan dan yasan yayi laifi ne yake mata wannan abun wani haka kawai bazai neme ta ba. Kwashe abinda aka b’ata tayi ta kashe hasken k’asan da komai ta hau saman ta samu Amira ita kad’ai da alama ya tafi da Zaytun. Zama tayi kusa da Amira babu mai magana dan kuwa bata niyar zuwa wajan ba a wannan lokacin.
Wayar tace take k’ara ganin shine yake kira ya saka ta d’auka ta saka a kunne yace, “Zo sama yanzu.” Abinda yake kenan ya kashe ta tashi ta nufi saman a zuciyar ta ta k’udurce baza ta bashi wata damar da zai yi wani abun da ita ba
D’akin ta shiga ta samu yana dube-dube duk ya fito da abubuwan drawer yayi mata filla-filla tana shiga yace, “Ina sark’ar gold din dana ajjiye a nan?.” Wajan ta k’arasa ta kalli inda cover din da sark’ar take ciki amma babu sark’ar ta kalle shi tace, “Ban sani ba nidai nasan a nan take, ko ka canja mata waje?.”
“İn na canja mata waje taya zan tambaye ki? Ki Tuna ko kin canja mata waje.”
Ta girgiza kai tace, “ban d’auka ba tunda ka fad’a min sample ne aka kawowa Abbah ya baka ajiya ban d’auka ba.”
“To Ina taje kenan?” Ya fad’a yana kallon ta. Tace, “ban sani ba wallahi.”
“Kamar ya baki sani ba? Wa na Bari a gidan?” Ya fad’a yana d’aukar wayar sa da take kara. Abbah ne yake waya ya kalle ta yace, “Kin gani Abbah ne yake min waya kuma akan maganar gold din ne” ya fad’a yana d’aukar wayar ya saka a kunne.
Abbah yace, “Yusuf ka tab’a kudin nan ne?.” Yusuf ya kalle ta yace, “Abbah Lafiya dai?” Ya fad’a yana saka wayar a speaker. Abbah yace, “an lissafa kud’in kuma an tab’a ko wacce rafa ta kud’in a zara guda d’aya, Kaga kenan babu dala dubu goma ko wacce rafar dala an dauk’i dala dari.” Yusuf gaban sa ya fadi yace, “amma Abbah ban tab’a komai a kudin ba ba wallahi, amma bara na tambayi……” Abbah yayi saurin katse shi yace, “shikenan kar ka tambayi kowa ai ba’a taba’a samun hakan ba sai wannan karon, gobe ka fito da gold din.”
Kai ya d’aga ya katse wayar ya dawo da kallon sa ga Ameena da take kallon sa yace, “Meye hakan yake nufi? Ina kudin nan suka shiga sannan Ina sark’ar dana ajjiye?.” Ameena tace, “Wallahi ban sani ba ban d’auka ba kaima ka sani.” Ya dafe kansa ji yake kamar ya mare ta yace, “nida waye a gidan in bake ba? Waye zai d’auki kud’in nan in ba ke ba?.”
Ameena ta zaro idanu waje tana kallon sa tace, “kana so kace nice nayi maka sata?.” Ya dafe kansa yana zaga d’akin tare da bincike ko Ina ko zai ga sark’ar amma babu ya juyo yace, “Wacece a gidan in ba ke ba? Waye yake shigowa d’akin nan in ba ke ba?, in wasa kike min ki d’auko sark’ar nan Ameena ba nawa bane ta Abbah ce shima kuma sample ce.” Ameena tace, “Wallahi ban d’auka ba kaima kasan ban tab’a d’aukar duk abinda ka ajjiye ba, kuma ni bana shigowa d’akin nan sai in zan share ban San da kud’i ba amma nasan da sark’a kuma ban d’auka ba.”