← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 42

Sashe 24

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ya sauke Ajiyar zuciya a bayyane yace, “naji dad’i da ta kasance tana gidan nan da ban san ya zanyi ba.” Abie yace, “A nan ta kwana bayan anyi mata allura, har yanzu bata ce komai ba na kuma tabbatar bata so tazo nan ba. A yanayin ta ma gabadaya bata so tazo gidan an ba taso tayi nisa da kai.” Yusuf yace, “laifina ne wallahi Abie amma nayi nadama bazan sake ba.”
“Daman ai ko baka ce ba ni nasan laifin kane, in laifin tane ai baza ta bar gidan ba. Yusuf kana wasa da marainiyar Allah ko? Kana wasa da alqawarin saka d’auka ko?. Kai kasan mahimmacin alqawarin kuwa? Kai kasan waye maraya kuwa?.”

Yusuf yace, “A’a ba haka bane…..” Abie ya katse shi ta hanyar cewa, “Kai kasan in Ammah taji labarin nan sai ranka ya b’aci ko?.” Ya girgiza kai alamun eh yace, “Dan Allah kar ka sanar da ita, kuskure ne na aikata bazan sake ba in sha Allah.”
“Kai dai ka sani, ya kamata kasan ko wacce mata ka samu a yanzu baza ka samu kamar Ameena ba, kuma wallahi matuk’ar na sake jin wani abun da kayi mata ni da kaina zan hanata komawa gidan ka domin nima yayan tane in Humaira ce ai bazan so ayi mata haka ba.”

Yusuf yace, “baza’a sake bama in sha Allah.” Abie ya mike tsaye yace, “kaje ka same ta in zata bika shikenan in kuma bazata koma ba zata zauna a nan kamar gidan yayan ta, kuma wallahi indai ta zab’i zaman nan naga k’afar a gidan sai ranka ya ‘baci.” Yusuf ya tashi ya shiga inda ya nuna masa ya same ta a zaune ta jingina da gado ta rufe ido kafafun ta a mike sand’al akan gado tana sauke numfashi a hankali.

A hankali ya k’arasa ya zauna kusa da k’afar ta ya saka hannayen sa duka biyun yana matsa k’afar a hankali ta yana cewa, “Ni mai laifi ne a wajan ki Ameena dan Allah ki yafe min, nasan nayi kuskure amma bazan sake aikata hakan ba in sha Allah. Nasan banyi daidai ba bai kamata nace abinda nace ba tunda nine zan bayar da shaidar ki, dan Allah kiyi hak’uri ki yafe min bazan sake wannan kuskuren ba.” Tunda ya shigo d’akin tasan yazo saboda khamshin turaren sa nan da nan zuciyar ta ta cigaba da k’una tana ayyana inda ace gidan yayan tane ba yayan sa ba da yanzu ba’a kira shi ba, da yanzu ba’a bashi damar ganin ta ba amma da yake kamar gıdan su ne Gashi har cikin d’aki.

“Dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba.” Ko motsi batayi ba balle ta amsa yace, “Ameena!.” Bata bud’e ido ba balle tayi magana tunda suke dashi bata tab’a jin haushin sa kamar yadda take ji a lokacin ba shiyasa ko kallon sa ma bata so tayi, duk abinda yake mata bata tab’a jin haushin sa kamar na yau ba.
“Ameena dan Allah.” Sai a sannan ta bud’e ido ta kalle shi tace, “Meyasa kake bani hak’uri? Saboda ka kirani da b’arauniya?.”

Ya kulle ido ya bud’e ya kalle ta zaiyi magana tace, “Inda ace Ina sa gata Ina da inda zanje da Yusuf baka isa ka same ni a nan ba, wallahi da kai da sake ganina sai ka manta ya kalar fuskata take, amma rashin iyaye shine yake min cikas a ko yaushe. A duk sanda naso guje maka sai na rasa inda zan Kefa k’afata kafin nayi wani tunani ka riske ni. Wallahi Yusuf duk ranar da na bar gidan nayi wani wajan na barshi kenan har abada bazan sake waiwayo ka ba.”

Yayi shiru yana sauraren ta yadda maganar ta take fita zaka san ranta a ‘bace yake kuma tana fama da rashin lafiya ta sake cewa, “Ni ka cewa barauniyar kudi da sark’a bayan tarin kwanakin da muka d’auka dakai ban tab’a maka satar maka koda zare a d’akin ka ba sai yanzu zan fara dan na yiwa amaryar ka sharri, in na d’auki abin ka me zai min? Baka san na jima da daina amfani da duk wani abu da ya shafe ka ba? Akan me zan d’auka baka sani ba?. Baka San da kai da shirgin ka basa gabana ba?, wallahi Yusuf an saka ruwa an wanke min zuciya haka nake ji a kanka, kaima baka cikin zuciyata balle kuma wata banzar dukiyar ka da a in na d’suka babu abinda zata k’ara min sai azabar kabari.”

Ya sassauta murya yace, “Raina ne ya b’aci shiyasa kike wannan maganar, Kiyi hakuri kawai .”
“Ko yaushe ranka a b’ace yake a kaina ai Yusuf! Ko wanne lokaci kiris kake jira dani nayi abu ka dake ni ko kayi min abinda gwara ka dake din ma. Dan Kaga iyayena k’asa ta rufe idanun su Yayata tayi min nisa Yayana da yake sona shima yayi min nisa, amma kana mantawa da Ina da Allah kuma shi idanun sa bud’e yake yana kallon kowa bai kuma yi min nisa ba yana kusa dani a ko yaushe. Na rasa abinda nayi maka, yau in nayi laifi gobe ma sai na sake yi, amma bana so nasan abinda nayi maka domin na gaji da d’aukar damuwar ka Yusuf lokaci kad’an nake jira baza ka sake ganina ba. İn badan Ammah ba da yanzu ka jima da manta sunan Ameena a rayuwar ka wallahi. Wallahi ji nake kamar na tsinke fuskar ka da mari.”

Yadda take ambatar sunan sa ya tabbatar masa da ranta a b’ace yake sosai yayi shiru yana jin ta zuciyar sa gabadaya ta karye kamar zaiyi kuka haka yake ji dan yasan yayi mata laifi ta sake cewa, “Naga alama ganina ne kusa dakai baka so kar ka damu wallahi na kusa fita daga rayuwar ka ka huta, watakila mutuwa zanyi watakila kuma da k’afata zan bar gidan. Ina so ka sani daga ranar dana bar ka wallahi daga ranar shafin dana sani ya fara a cikin rayuwar ka, in mutuwa nayi zaka tuna in kuma ina da rai zaka ce na fad’a maka.” Da sauri ya kalle ta jin ta ambaci mutuwa yace, “Ki daina zancen mutuwa dan Allah, baza ki mutu yanzu ba sai na koma miki Yusuf din ki na baya, sai na dawo da soyayya ta a zuciyar ki Ameena.”

Murmushi tayi tace, “Soyayyar ka a zuciyar Ameena? Har abada wannan bazai sake faruwa ba, a wancan lokacin ma kuskure aka samu shiyasa kake abinda Kaga dama kaga dama kake ganin kamar bazan iya rayuwa ba sai da kai.” yace, “nidai ki yi hakuri dan Allah kuzo ku koma gida na amince da duk hukuncin da zaki min zan d’auka.”

“Kaje zan dawo da kaina amma bazan tafi dakai ba, yadda na fito ni kad’ai zan koma ni kad’ai. Amma Ina so ka sani duk ranar da na dauki k’afa na tafi Bauchi wallahi bazan dawo gidan ka Ina so ka ajjiye wannan a zuciyar ka. Kai ko ba Bauchi ba matuk’ar Ameena ta sake barin gidan ka wallahi ta barshi kenan.” Yadda take nuna shi da yatsa tana wara idanun ta a kan fuskar sa zaka tabbatar maka da haushin sa take ji shi kansa ya fahimta hakan ya saka shi yin shiru ya mik’e yace, “Na gode da jin hakan, abinda kike tunani ma bazai sake faruwa ba in sha Allah. Daga yau nayi miki alqawarin baza ki sake kuka da Yusuf ba Ameena, kuka indai ba na farin ciki ba bazan bari hawayen ki su sake zuba a k’asa ba” ya fad’a yana fita ta koma ta kwanta zuciyar ta nayi sanyi dan ko babu komai ta amayar da abinda yake zuciyar ta.

Tunda ya fita hankalin Asiya ya tashi ta d’auki waya ta kira Umma cikin tashin hankali take cewa, “Umma jiya na saka tayi yaji ta bar gidan nan amma baki ga yadda hankalin sa ya tashi da yasan ta fita ba, Umma har yanzu yana son matar nan tasa ni kuma ba haka nake so ba” ta fad’a kamar zatayi kuka dan abin ya tayar mata da hankali sosai.

Umma tace, “ki kwantar da hankalin ki mana badai har kin saka ta fita ba, wata ran ta fita bazata dawo ba tunda har ta fara fitar.”
“Umma yaushe? Bana so na cika wata d’aya a gidan nan matar sa tana nan.”
“Kin cika gaggawa Asiya komai a hankali ake bin sa yadda bazai gane ba sannan ba kuma zaiyi tunani ba, ki tsaya ki nutsu Ina sane da komai zan kuma yi maganin komai.”

Asiya tace, “Umma dan Allah a san abinda za’a yi, ko fad’a min a dalilin yajin ma baiyi ba ni so nake ko kwanciya yayi da ita ya fad’a min, ya kasance ko wanne sirri na sani Umma, ta haka ne hankalina zai kwanta.” Umma tace, “kar ki damu yadda muka fara samun arzuki dashi ai baza mu bari komai ya lalace ba, in Momi zata dawo akwai sak’o daga wajan Umman ki Sakina wanda zaki yi amfani dashi gobe in ya dawo wajan ki kenan.” Ta amsa da to daga nan suka yi sallama ta kashe wayar.

Tana wajan a zaune ya dawo ya kalle ta dan kayan da ya barta dasu har lokacin dai sune a jikin ta yace, “Bakya jin gidan nan yana wani k’arni?.” Asiya tace, “Gaskiya daga hancin kane bana ji komai nidai.”
“Okay” ya amsa a takaice tace, “My love ka samu Auntyn? Ina nan hankalina duk ya tashi Allah yasa ba wani abun bane ba ya same ta.” Yusuf yace, “Komai lafiya babu abinda ya faru.”

Ajiyar zuciya Asiya tayi tace, “Alhamdulillah naji dad’in hakan,da na tsorata wallahi. Allah ya cigaba da tsare mu baki daya.” Kallon ta yayi cikin Jin dad’i ya murmusa yace, “Amin my love. Baki wanka bane?.”
“Na kasa shiga band’akin saboda wannan maganar ai, yanzu zanyi “ ta fad’a tana tashi yace, “in Kinyi wanka anjima zamu je gidan Ammah kar ki manta.” Da to ta amsa ta hau sama shima yabi bayan ta a zuciyar sa yana yaba halayyan ta dan tana son Ameena sosai shi kuma daman haka yake so dan baya son tashin hankali a tsakanin matan nasa.

#MAI DAKI
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema.
Chapter 24 · 0% Book details