← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 42

Sashe 30

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akan me zai bata hak’uri ba Alhaji? Ita bata bashi hak’uri ba shine zai bata hak’uri dan kawai ta Raina shi?" Hajiya ta fad'a tana kallon Ibrahim da yake cin abinci baice komai ba har lokacin kamar babu shi a wajan. Alhaji yace, "Tayi mana abinda ba'a tab'a yi ba, har kofar gida ta turo aka zo aka kama shi kawai dan ta ci mutuncin mu baki daya."
"Duk abinda ta aikata na tabbata wata ran sai tayi dana sani, ko babu komai ai akwai Amir zata zo da k'afar ta ne Allah ya bamu lafiya" Hajiya ta fad’a a fusace dan taji zafi sosai na abinda ya faru sosai. Shi dai baya magana amma zuciyar sa tafi ta kowa zafi a haka duk suka tashi suka tattafi gida shi kuma ya fita daga gidan ko zai samu sassaucin abinda yake ji

Bayan kwana biyu.

Amarya Fiddausi ana ta sha gyaran jiki na tarewa tayi matuk'ar kyau daka zauna kusa da ita sai khamshi fatar ta har shek'i yake saboda kyau da kyaun gani. Kamar yadda aka tsara ranar juma'a zata tare Kasancewar Abuja zata tafi Zakiyya ce kawai tazo dan Rukayya baza'a barta zuwa Abuja ba ita kuma Ameena bata samu fitowa ba.

A private get aka tafi kai Fiddausi ita da Zakiyya da kuma y’an gidan su aka kaita babban gida mai kyau madaidaici zaman mace guda d'aya, kallon gidan take yi tana sake kallo zuciyar ta fari tas burin ta ya cika ta samu abinda take so hankalin ta ya kwanta.

Lokacin da suka shiga Abuja azahar ce suna sauka suka fara sallah bayan an idar aka ci abinci mai rai da lafiya Zakiyya taja Fiddausi d’aki tana kallon dakin tace, "Yanzu ya kike jin kanki dan Allah?." Fiddausi tayi dariya tayi juyi da d’akin ta fad’a saman gado tace, "Farin cikin da ban tab'a jin sa ba, ki duba wai gidan nan nawa na fa." Zakiyya tace, "Yanzu kika zama mace da kina zaune da wani fakirin miji."

Sukayi dariya a tare Fiddausi tace, "Sai dai Ina tuna Amir dina wallahi, Ina son yarona zan kuma yi kewar sa" ta fad'a tana yin baya ta kwanta a kan gadon zuciyar ta cike da farin ciki. Zakiyya tace, "Kakar sa zata kula dashi ai, dan haka Baki da wata damuwa akan Amir."
"Wallahi Zakiyya a duniya bani da masoyi kamar ki." Zakiyya tayi dariya tace, "Ke jirgi ance zai tafi, bara naje kar a tafi a barni, sai naji feedback na first night dan nasan kayan Surayya Halin yau zasu gigita mai gidan nan" ta fad'a tana dariya tana niyar fita.

Fiddausi ta tashi ta dawo kusa da ita tace, "Sai kinji labari Ina tabbatar miki da komai ya faru ke zaki fara ji." Dariya tayi a tare Zakiyya tace, "Amarya amarya, ai yanzu zaki san asalin dad’in aure ba kwanan duhu balle zaman a cikin zafi, sai na jiki aminiyar." Har waje ta rako su suka shiga mota aka tafi airport dan dawowa Kano.

Fiddausi komawa tayi tana sake kallon gidan ko Ina sai da ta shiga ta hau sama ta sakko gani take abin kamar a mafarki wai wannan gidan tane, farin ciki take ji sosai sai da ta gaji da zagayen sanma ta dawo ta zauna aka d’ora k’afa a kan d’aya ana girgizawa ana jiran ango yazo a sha soyayya mai dad’i wacce aka jima Ana jiran zuwan ta.

Sai da akayi magariba sannan taji an bud’e gate alamun angon ta ya iso ta tashi tana kallon sa ta window ta ya fito daga mota cikin shigar alfarma yana amsa waya hannun sa rike da leda babba da k’arama. sakin laluben tagar tayi ta saka fashe jikin ta da turare tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba karya. Murmushi take yi ita kadai tana hasashen irin soyayyar da zasu kwasa a cikin daren.

Motsin sa take ji yana shigowa sai ta fito falo ta zauna ya k’araso har lokacin da ya shigo waya yake yi, suna had’a ido sai taga ya sauke wayar ya mayar aljihu ya bud’e mata hannayen sa alamun tazo, ba musu ta tashi ta isa gare shi ta shiga jikin sa ya rungume ta tsam yana fad’in, "Daga karshe ga Baby a cikin gıdana, babu abinda ya kai yau mahimmaci a gare ni. Yau ce ranar da bazan tab’a mantawa da ita ba, yau ce ranar da nake mararin zuwan ta, yaushe ranar da nake fatan na ganta, yau ce ranar da zuciya take burin gani. Gani gaki my Baby zuciya ta kasa gasgata hakan gaskiya ne.”

Fiddausi tayi dariya ta d’ago tana kallon sa ido cikin ido tace, "Daga karshe ka zama mallakina. Ni taka ce kaima nawa ne, babu abinda zai raba mu sai mutuwa. Ba mafarki kake ba Baby nice dai a gaban idanun ka kake gani.” Sakin ta yayi yana kallon ta yace, "Dole mu yiwa Allah godiya da ya nuna mana wannan ranar mai mahimmaci a rayuwar mu, muyi sallar I’sha sai muyi ta godiya ga Allah ko my Baby?.” Murmushi tayi ta daga mai gira ya cije bakin sa yace, "Zaki bada bayanin wannan daga girar sama, Allah ysa amaryar tawa ba raguwa bace dan mijin ta gwarzo ne, muje muyi sallar tukunna."

Fiddausi dai jin ta take kamar a mafarki ko kamar ba ita bace wata Fiddausin ce daban ba ita ba, domin ganin abu take kamar film take kallo wai yau itace a gidan Alhaji Bello wanda yake d’aya daga cikin masu kudi manyan y’an kasuwa na Nigeria.

A haka akayi sallah kamar yadda yace suka ci abinci tare shida ita kafin soyayyar da suke yiwa junan su ta fara bayyana a fili. Dan Fidy nuna masa qauna take kamar yadda shima yake nuna mata dan burin kowa ya tabbatar da soyayyar da d’an uwan sa yake yi masa. Fiddausi ta tabbatar da a baya ba aure tayi ba yanzu ne tayi aure tasan meye aure, yanzu tasan dad’in sa take kuma more masa.

Gabadaya haushin shekarun baya take ji zuciyar ta ta cika da d'aci da k’uncin shekarun da ta kwashe da İbrahim tana wahalar banza da wofi amma a yanzu ta san soyayya tasan madarar ta ita da mijin ta abin son ta.
Kamar yadda yayi mata alqawari washe gari jirgin bakwai na safe ya kwashe su zuwa k’asar America, farin ciki a wajan Fiddausi kamar wacce aka yiwa kyautar aljanna haka take ji, ko da yake tace ta samu aljannar duniya a gidsn Alhaji Bello.

A dai yi mu gani🫠

#Mai daki
#Book2
#Paid
#Nana Haleema
#09030398006

Book2
020

Tunda ya shiga falon nata yake bin sa da kallo gabad’aya komai ya fita daga hayyacin sa hatta kujerun falon sun fara duhu saboda basa samun kula mai kyau, wajan tv stand ya k‘arasa ya saka hannu ya shafi k'urar da take jiki ya sauke numfashi yana girgiza kai ya hau saman nata kai tsaye. Allah ya sani yak’i jinin k’azanta amma yaga alama Asiya bata son gyara ko kusa.

Kukan ta ya jiyo daga bakin k’ofa kamar zai shiga sai ya fasa ya tsaya yana jin abinda take cewa, daga cikin d’akin Asiya na zaune da waya a kunnen ta tana kuka tana fad’in, "Ni ban san ya zanyi ba Umma matar sa bata sona kuma wallahi ni tsakani da Allah nake zaune da ita, meyasa cin fuskar ta bazai tsaya iya ni ba sai ta had’a dake a ciki Umma? Daga kawai jiya kin shiga ku gaisa shikenan sai ta fara zagin ki? Bazan iya jurewa ba Umma babu wanda zai tab'a min uwa ya zauna lafiya."

Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta sake cewa, "Ban fad’a masa ba Umma bana son yawan masa magana akan matar sa kar yaga kamar da wani dalili nake masa maganar ko yaga nice bana son zaman Lafiya, bai San abinda ya faru ba bazan kuma fad’a masa ba saboda bana son haddasa fitina amma wallahi banji dad’i ba kefa ta ciwa fuska Umma, harda cewa wai kin saka na shigo gidan nan da a kore ta, inda mahaifiyarta na yiwa haka ai itama bazata ji dad’i ba. Mahaifi sunan sa mahaifi babu Wanda yafi wani.”

Yusuf da yake sauraren abinda take cewa ya sauke numfashi ya kulle idanun sa, kenan jiya da mahaifiyar Asiya tazo ta shiga dan su gaisa d- Ameena ta ci mata mutunci ko me kenan?. Tsaki yayi a bayyane yace, "Me yake damun Ameena ne? Yaushe ta koma haka?. Ameena da bata son fad’a magana ma bata dame ta ba yaushe ta zama Mara kunya wai har haka?. Na fara gajiya da halayyar Ameena bata son zaman Lafiya yanzu ko kusa ko alama" ya fad'a yana murd'a handle din d’akin ya shiga sai ta zabura ta kashe wayar tana bin sa da kallon shima ita yake kallo yana kuma kallon d’akin.

Mopper a ajjiye duk tayi daud’a ga kayan ta a jibge a gefe d’akin sai wani wari yake na musamman dan ya tabbata har da warin bandaki ma, zama yayi yana kallon ta itama ta kalle shi tace, "Ina kwana My love." Binta yake yi da kallo ganin kanta yana nan bata gyara ba kamar yadda yace yana binta da kallon tun kayan jiya da safe ne a jikin ta har yanzu alamun ko wanka ma batayi ba yace, "Ba nace kije a gyara miki kanki ba?."

Shiru tayi tare da tura baki gaba ya sake kallon ta yace, "Asiya bana son k'azanta ba kuma na zama da k'azami, kince min aikin gidan ya ayi miki yawa an kawo miki masu aiki amma duk da haka babu abinda ya canja. Kullum gidan nan kaca-kaca kema kanki babu gyara, gidan nan har wani wari yake yi in na fad’a kice ke bakya ji. Ki kula ki kuma gyara sam sam bana son k'azanta Asiya." Yadda yake mata maganar a sanyaye ya saka ta d’aga kai sama tace, "to."
"Meya faru jiya da Umma tazo? Akwai abinda Ameena tayi mata ne?."
Chapter 30 · 0% Book details