← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 42

Sashe 32

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin Yusuf ya shigo yana bin su da kallo ita da Amira cikin zallar bacin rai sai kuwa Asiya ta tashe da kuka ita da Maimiuna tana cewa, "Yaya sai da nace kar mu shigo Umma ma bata kyale ba balle ke, Gashi daga gaisawa ta dake ki nima ta dake ni. Ki tashi mu tafi bana son tashin hankali. Mu muka kawo kan mu ko me tayi mata mu muka jawo.”

Maimuna tace, "Nayi tunanin dan na shigo mun gaisa ba wani abun bane dan Umma tace abinda ya faru ya wuce kar mu canja mata. kiyi hak’uri Ameena basai kin kai ga dukana ba laifina ne da na shigo gidan nan, ban d’auka hakan zata faru ba da banzo ba.” Yusuf da yake tsaye baiyi wani tunani ba ya k’arasa inda Ameena take a fusace yace, “wanne irin hauka ne wannan wai Ameena? Yaushe kika koma wannan banzayen halayen. Dan Malama ki basu hak’uri Yanzun nan.”

Ta girgiza kai tana kuka tana kallon su duka biyun kawai ta wuce sama yabi bayan ta a guje su kuma sukayi dariya a tare suka tafa suka mik’e tsaye suna hararar Amira Maimuna tace, "Yau sai Kun bar gidan nan, duk Bala’in ku gidan Yusuf na Asiya ne ita kad’ai” tana fad'ar hakan ta fice tana hararar falon Amira ta zauna a wajan tana kuka sosai.

Magana yake yana bin Ameena tana tafiya tayi masa banza yana zuwa kusa da ita ya cinkota ya d’aga hannu zai mare sai ya fasa yace, "Ina yi miki magana kina tafiya? Abubuwan da kike yi a gidan nan Ina kyale ki har ya kai haka?. Yayar matata kika saka hannu kika daka dan baki da mutunci? Kishin naki har yakai haka?.” Bata ce komai ba sai kallon sa da take yi yace, "kin sace min gold, kina d’aukar min kudi, kin zagi babar ta, kin zage ta, ki kore ta daga motar ki, yanzu kuma kin daki yayar ta. Da yake ke mara hankali wacce bata san abinda take yi ba nace ki bata hak’uri sai ki tawo nan dan ki nuna musu ban isa dake ba?.”

"Kaine mara hankali ba ni ba, in ma hauka ne kaine kake yin haukan bani ba....." Marin ta yayi tare da hankad'ata baya ta fad’i ta buge da kujera yana kallon ta yace, "Ni kike fad’awa haka?."
"Na fad’a maka, na fada, nan gaba ka sake dukana ma wallahi sai na rama na gaji ba saboda haka aka kawo maka ni ba. In ka gaji da zama dani ka sake ni mana ai baa dole. Me na tare maka?.”

Da mamaki yake kallon ta ransa ya b’aci sosai yace, “ni kike fad’awa haka?.”
“Nace na fad’a maka d’in, zuciya ce a kirjin ka nima itace a kirjina. Na daina lamuntar abubuwan da kake yi min, dan kana ganin kamar ina jin tsoron ka shiyasa kake taka ni yadda kake so. Yanzu komai ya k’are yadda baka sona nima bana sonka, ka sake ni in ka gaji da zama dani.”

"Daman ai bani na kawo ki ba Ameena Ammah ce kuma zaman ta kike yi, Ammah ita ta ganki tace na aure ki bani da zab’i na amince nata saboda tana sonki ba dan ni ina so ba, duk soyayyar da na nuna miki anyi ne saboda Ammah yanzu ne na samo zab’in raina kuma wallahi baki isa kiyi mata wani abun ba na kyale ki dan ta fiki a wajena. Dole ki karb’i hukunci in kika aikata ba daidai ba.”

Duk da halin da take ciki sai da gaban ta ya fad’ita mike tsaye tana kallon sa jikin ta duk a sanyaye da abinda yace tace, "Da gaske baka sona?."
"Eh bana son ki, bani na ganki nace Ina so ba Ammah ce ta saka na auro ki Ina zaune dake ne kawai saboda ita badan so ba. Banda abin ki in badan Ammah ba taya zan zauna da b’arauniya kamar ki?. Taya zan zauna dake kina fad’a min magana ina kyale ki?, kallona kika yi kika ce na sake dukan ki sai kin rama, ba dan Ammah ba da Yanzu kin jima bakya gidan nan domin kuwa bazan zauna dake ba!.”
Sai kuwa ta fusata tace, “in baka sona ka sake ni mana, ka sake ni in da gaske baka sona ai babu Wanda yayi mama dole sai ka zauna Dani.”
Yusuf ya wara idanun sa kanta yace, “Saboda Amma kike zaune a nan in badan haka ba da yanzu bakya cikin gidan nan, bazan zauna da mai sata ba ke kin San da haka, badan Ammah da yanzu na manta da shafin rayuwar ki gabad’aya.”

"Tunda kana so ka manta da shafin rayuwar ta zaka manta Yusuf, Tabbas baza ka zauna da barauniya ba Yusuf, yau alfarma da take ci saboda Ammah ta k’are Yusuf, zaman hak’urin da kake da ita duk ya k’are daga yanzun nan. yau b’arauniya zata bar gidan ka sai ka zauna da wacce kake so!." Jin muryar wanda basu yi tunani ba duk suka juya suna kallon inda suka ji maganar ba kamar Yusuf da ya wara idanu yana kallon wajan zuciyar sa har harbawa take yi.

#Nana Haleema
#Mai Daki
#Book2
#Paid
#500
#09030398006.

Book2
021

Dukkan su a tare suka kalli wajan Ameena ta ware idanu waje cikin mamaki da murna da kuma tsoro, babu wanda bai ji tsoro ba ganin wanda basu yi tunani ba a tsaye yana kallon Yusuf da b’acin rai a kan fuskar sa har wuci yake saboda b’ari ran da yake ciki, fuskar sa a murtuk’e daman shi ba gwanin fara’a ba, yadda yake bin Yusuf da kallo ma abin tsoro ne saboda kana ganin kallo kasan babu sassauci a cikin sa.

Ameena a guje ta k’arasa kusa dashi ta rungume shi tana kuka sosai a jikin sa ya rik’e ta shima yana kallon Yusuf zuciyar sa wuya ji yake kamar yayi masa dukan tsiya yace, “Ko baka ce ba yau Ameena zata bar gidan nan Yusuf, Tunda b’arauniya ce ba sonta kake ba ina tabbatar maka daga yau zaman ta ya k’are.” Ya kalli Amira da yake tsaye yace, “Shiga d’akin ta ki d’auko mata mayafi da duk abinda kika san zata yi amfani dashi yanzu ku fito mu tafi.”

Yusuf ya kasa ko motsin kirki sai kallon Yaya Adam da yake yi dan yasan tunda yace sai ta tafi wallahi sai ta tafi, zuciyar sa bugawa take yi sosai dana sanin furucin da yayi a kanta ya mamaye masa zuciya hakan ya saka shi kasa koda d’aga ido ya kalle shi, yayi tsitt ya kasa tankawa haka yaga Amira ta wuce shi ta shiga d’akin Ameena tana jifan sa da harara.

Yaya Adam ya d’ago da Ameena daga jikin sa yana kallon ta yace, “Gatan ki ya dawo Ameena, babu wanda kuma ya isa ya sake yi miki abinda yayi miki daga rana irin ta yau indai Adam yana numfashi. Babu wanda ya isa ya kuma dukan ki matuk’ar ina da rai, rashi na kusa dake ne ya jawo hakan kar ki damu na dawo gare ki yanzu.” Kuka take yi sosai fuskar ta tayi ja ta kumbura saboda marin da ta sha a hannun sa ya kalli kumatun ta ya girgiza kai a lokacin Amira ta fito da babbar jaka da kuma tata jaka tazo ta wuce shi ta baya Ameena mayafin yace, “Jeki ki saka a mota.”

Ba musu ta wuce zata sauka ya kalli Ameena yace, “Jeki kema.” Ta rik’e hannun Zaytun zasu fita yace, “bar masa y’ar sa a nan ai ba da ita kika zo ba.” Kallon sa tayi kamar zatayi magana sai kuma ta kasa cewa komai ta saki hannun Zaytun sai kuwa ta saka kuka tana kiran Mummy tana bin bayan ta ya kalli Ameena d’in yace, “Jeki da ita ina zuwa.”

Fita sukayi daga falon ya juya ya kalle su yaga basa hango shi ya matso kusa da Yusuf bai tsaya jiran wani abu ba ya tsinke shi da mari ya nuna shi fa yatsa yace, “Na Rama mata marin da kayi mata ko na ce kake mata, sannan kar ka sake kazo inda take, koda wasa na ganka a gida na wallahi sai ranka ya b’aci fiye da tunanin ka, kar kazo inda Ameena sai da takardar saki na sake maimaita maka” yana fad’a ya juya ya fita ya tarar da Ameena jiri na k’okarin yarda da ita yayi sauri ya rik’e ta a lokacin Amira ta dawo ta sauka da Zaytun shi kuma ya rik’e Ameena suka sauka yana rik’e da ya bud’e mota ya saka Ameena Amira ta shiga gaba yaja motar suka fita daga cikin gidan.

Suna cikin tafiya ya kalli Amira yace, “Wanne asibiti kuke zuwa sun bata da lafiya?.” Amira har lokacin kuka take yi ta ja numfashi tace, “Wani private ne a nan gaba, bara na kira likitan da take zuwa wajen ta ko tana nan” ta fad’a tana bud’e wayar Ameena ta kira Dr mansura ta tabbatar mata da tana asibiti suka nufi can kai tsaye.

Da taimakon Amira suka je wajan Dr mansura tana ganin su ta mike’e aka kwantar da Ameena akan gado da yake office d’in ta ta fara suna jinin ta dan tasan dakyar in ba shine ya hau ba, suna nan tsaye suna kallo sai suka ga tayi sauri ta d’auko ruwa ta saka mata, ta dauki allura tayi mata a jijiya daga nan bacci ya kwashe Ameena cikin mintina kad’an. Bayan ta gama ta tabbatar Ameena tayi bacci Dr Mansura ta kalli Yaya Adam tace, “Dan Allah kai Yayan tane?.” Ya daga kai yace, “Eh ni Yayan tane ko nace mahaifinta, meye yake damun ta?.”
Chapter 32 · 0% Book details