← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 42

Sashe 34

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yayi ya fita Jim kad’an ya dawo da Leda da ruwa a hannun sa ya ciro maganin da kansa ya mik’a mata ta karb’a tasha ya ajjiye a kusa da ita yace, “Gasu nan kar ki dinga fashin shan su.”
“To Yaya” ta fad’a tana Jan maganin kusa da ita shi kuma yana kallon ta har lokacin.

Yace, “Ameena!.” Ta d’ago idanun ta ta kalle shi tace, “Na’am Yaya.”
“Yusuf ya saba dukan ki?” Ya fad’a yana tsare ta da idanun sa wanda ya saka tayi shiru ba bashi amsa ba yace, “kar kuma ki yi min k’arya ki bud’e baki ki bani amsar duk abinda na tambaye ki, Yusuf ya saba dukan ki?.” Ta d’aga kai alamun eh ya girgiza kai yace, “Meyasa baki i tab’a fad’a min a waya ba?.”

“Bana son na tayar maka da hankali ne shiyasa..”
“Baki San yanzu abun yafi tayar min da hankali ba?.”
“Kayi hak’uri Yaya, ganin baka kusa ya saka bana son fad’a maka irin wannan maganar.” Ya sauke numfashi yana kallon ta yace, “abinda naga Yusuf yana yi miki ya tabbatar min da a jiyan ya fara ba ya saba yi miki Ameena, na tabbatar ya saba dukan ki haka zakila ya saba ci miki mutunci. Tunda jiya Allah yasa na gani k’arshen wulakancin da yake miki yazo k’arshe. Babu zaman jin dad’i a auren ki da Yusuf ki ba’a fad’a ba yanayin ki ya nuna hakan, kin rame kin fita daga hayyacin ki bayan da ba haka kike ba.”

Ya sake cewa, “Yaushe kika kamu da cutar hawan jini?.” Gaban ta ya fad’i ta kulle ido ta bud’e kanta a sunkuye bata ce komai ba ya girgiza kai yace, “Ameena an tabbatar min da kin jima kina shan maganin hawan jini, yanzu haka gasu nan a gaban ki na baki kin sha” ya fad’a yana kallon yaga sai raba idanu take sai yayi murmushi takaici ya sake kallon ta yace, “Ameena kalle ni.” Ba musu ta kalle shi yace, “Bazan barki ki cigaba da zama da mijin da bai San darajar ki ba kamar Yusuf, bazan barki ki cigaba da zama a inda aka bud’e baki akace alfarma kike ci ake zaune dake ba Ameena, bazan bari ki cigaba da zama a inda ake kokarin kashe ki ba. Ameena zan raba auren ku da Yusuf, ki fad’a min gaskiya kina goyan bayana ko bakya goyan bayana?.”

Shiru tayi bata amsa ba sai zuciyar ta da take bugawa ta kasa cewa komai kanta yana k’asa bata san wacce amsa zata bashi ba yace, “kar kiyi min k’arya ki fad’a min kina goyan bayan na saka ya sake ki ko kuma kina son komawa gidan sa?.” Yadda yayi maganar a kausashe ya saka ta jan numfashi ta d’aga kai alamun eh, yace, “me hakan yake nufi? Kina son koma masa Kenan?.” Tayi saurin girgiza kai alamun A’a yace , “Kiyi magana mana.” Ameena murya na rawa tace, “A raba auren.”

“kin tabbatar har zuciyar ki?.” Nan ma ta d’aga kai alamun eh ya girgiza kai ya mik’e tsaye yace, “Yusuf ka jira zuwa na gare ka, zan tabbatar maka da Ameena nada gatan da baka isa ka sake wulakanta ba, ko kana so ko baka so a sai ka sake ta. Tunda k’anwata ta samu ciwon hawan jini ta dalilin ka sai na saka kayi dana sanin da baka yi tunanin zaka yi ta a cikin rayuwar ka ba” ya fad’a yana fita daga d’akinta bishi da kallo ta koma da baya ta kwanta kawai sai hawaye ya fara sakko mata daga idanun ta ba tare da tasan dalilin zuwan su ba a wannan lokacin.

#Mai daki
#Book2
#Nana Haleema
#Paid
#500

Book2
022

Rukayya tana kwance a d’aki ita kad’ai Zuhra ta shigo da sallama ta amsa tana kallon ta tace, “Yaya kizo in ji Baba.” Da to ta amsa ta tashi ta fita ta same shi a zaune a falon Umma daga shi sai ita ta k’araso ta zauna akan carpert tace, “Baba gani.”

Baba ya kalle ta yace, “Jiya da daddare wani yazo ya same ni akan yana neman izinin zuwa wajan ki.” Gaban Rukayya yayi mugun fad’uwa cikin sacannin da basu wuce biyu zuwa uku ba farin ciki ya mamaye mata zuciyar ta ta daure ta b’oye bata nuna ba sai murmushin jin dad’i da take yi kanta yana sunkuye.

Baba ya sake cewa, “ya fad’a min a nan k’ofar nasarawa iyayen sa suke, daga jiya zuwa yau na saka an bincika min an tabbatar haka ne mahaifinsa mutumin kirki ne duk da baya duniya. Anjima da yamma zai zo dan ku gana sai dai ya sanar dani yana da aure da kuma yara guda biyu.” Umma tayi caraf tace, “Dan yana da aure ai ba wani abun bane, indai zai rik’e ta hannu biyu babu ruwan mu da matar sa wallahi, Allah ya basu zaman Lafiya shine abinda zamu ce, Allah ya daidaita su” Umma ta fad’a tana murmushin farin ciki wanda ya bayyana akan fuskar ta sosai.

Baba yace, “Amin, amma ai bai zama mijin nata ba sai ta ganshi in yayi mata sai a san abinda za’a yi, in kuma bai mata ba sai ya tafi Allah ya kawo wani.” Umma ta kalle shi tace, “Yanzu wai sai ta tsaya zab’e kake nufi? Ai a ganina da an samu a amince ba sai an tsaya wani dogon jawabi ba.”
“Sam, sai yayi mata ta amince dashi sannan za’a yi auren, in kuma bata amince ba babu wanda zai aura mata wanda bata so.”
“Kai kake zugata daman ai take koran masu zuwa wajan ta, yanzu dan Allah meye abin zab’en mijin aure a wajan Rukayya dan Allah?.”
“Saboda ita ba mace bace?.”
“Mace ce mana, amma shekarun ta sun wuce zab’ar miji a yanzu, sai dai duk wanda yazo a karb’a ayi fatan alkhairi.”
“Ko me zaki ce sai ta amince sannan za’a yi auren nan, wallahi in bai mata ba zuciyar ta bata amince dashi ba babu wanda zai tilasta mata.”
“Ai shikenan” Umma ta fad’a tana tashi ta shiga d’aki.

Baba ya kalli Rukayya yace, “Kar maganar ta ta dame ki, ki tsaya ki nutsu ki tabbatar zaki iya zama dashi in kika ji akasin haka kar ki cuci kanki. Ba maganar tace zata zauna da mijin ba kece, kinga kenan sai kin gamsu a zuciyar ko zaki iya zama dashi sannan zaki aure shi.” Rukayya ta d’aga kai jikin ta yayi sanyi da kalaman Umma fahimtar hakan ya saka Baba yace, “Babar ki ba k’in ki take ba Rukayya, so take kiyi aure kema ki zauna a gidan ki kamar yadda sa’anin ki suke. Soyayya ce take nuna miki a baibai ba wai k’iyayya ko ta gaji dake ba, kinga kece a wannan halin na zaman gida ko?, Zan iya rantse miki ta fiki shiga damuwa akan rashin auren nan naki, yadda take miki addu’a ke bakya yiwa kanki saboda ita uwa ce a gare ki. Kar ki damu da kalaman ta na yanzu ki tabbatar zuciyar ki ta amince da wanda zai zo wajan ki in baki amince ba kar ki cuci kanki dan ke zaki zauna dashi, jinkirin aure bazai saka na aurar dake ga duk wanda yazo ba tare da kin amince ba.”

Rukayya tayi murmushi tace, “İn sha Allah Baba. Allah ya saka da alkhairi.” Ya amsa da amin kafin yace, “tashi kije, Allah yayi miki albarka ya baki mijin da zaki ji dad’in zama dashi.” A zuciya ta amsa da amin dan bata iya amsawa a fili indai Baba yayi mata irin wannan addu’ar ta tashi ta koma d’aki.

Farin ciki take ji a ranta da zuciyar ta wai ita Rukayya wani namiji ya gani yana so har yazo ya samu mahaifin ta da maganar, abin kamar a mafarki take ji sa. Kenan itama zata zama cikin layin masu masoya ba wanda ake son a a had’a su ba. fuskar ta ta kasa b’oye farin cikin da take ciki dan sosai take murna da hakan ko babu komai a yanzu tasan Allah ya amshi addu’ar ta tunda ga sakamako nan ta fara gani tun ba’aje ko ina ba. Ko iya haka aka tsaya Alhamdulillah domin ta tabbatar addu’ar ta ta karb’u Allah ya amsa sai dai ta jira lokaci kawai.

Tana zaune a gefen gado Umma t shigo ta k’araso ta zauna kusa da ita tana kallon ta tace, “Rukayya!.” Ta amsa tana kallon Umman tace, “Dan girman Allah ki amince da mutumin da zai zo wajan ki, in ya sub’uce wa muke dashi da zai sake neman auren ki? Bamu da kowa sai Allah. Dan Allah ki amince tunda shi ya kawo kansa ba nemo shi akayi ba ayi auren nan a gama, kina kallo Zuhra an kawo kud’in auren ta kanwar ki ce ta biyu, ina kishin hakan a raina Rukayya, ki taimaka min ki amince dashi dan Allah. Koda bai kwanta miki a zuciyar ki ba indai mahaifin ki ya amince da nagartar sa ki amince wata rana zaki so shi Rukayya, mijin aure wahala yake a yanzu na tabbata zaki bada shaida kema da kanki, kar mu bar wannan damar ta kubce mana.”

Yadda Umma take magana a raunane ya saka Rukayya kwalla ta cika mata idanu ta sauke idanu k’asa tace, “in sha Allah Umma a wannan karon bazan yi abinda bakya so ba, amma ki taya ni addu’a Allah yasa shine na gari a wajena kuma shine alkhairin da ake jira. Ki min addu’a Allah yasa k’arshen wahalar kenan Umma.” Umma tace, “Addu’a kullum cikin yi miki ake Rukayya, in sha Allah lokacin ne yazo yanzu.” Shiru Rukayya tayi bata ce komai ba kafin Umma ta tashi ta fita ita kuma ta kwanta a kan gadon tana ji a ranta zata amince da wanda zai zo wajan ta kodan Umma.
Chapter 34 · 0% Book details