← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 42

Sashe 39

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameena tayi murmushi gaban ta ya fad’i sosai zuciyar ta na harbawa a guje amma baya nuna hakan ba tace, “Haka ne.” Yaya tace, “jiya yaje gidan su ya zayyana musu komai da yake faruwa ya kuma tabbatar da Yusuf sai ya sake ki, kin san Yaya Adam bazai sake bari ki zauna sa Yusuf ba gaskiya.”
“Nima bana fatan sake zama dashi” ta fad’a tana juya cokali a ciki shayi ba tare da ta kalli Yayan ba. Yaya daya dafa ta tace, “Nima bana goyan baya Ameena, rabuwar ki da Yusuf shine yafi alkhairi a ganina .”

Ameena tace, “shine ma alkhairi Yaya kuma hakan za’ayi” ta fad’a tana kallon Yayan tana murmushi. Kallon ta kawai take yi tana so ta gane yanayin ta amma ta gaza gane hakan a yadda take magana baza kace Ameenah da ta taso Yusuf bace ba a lokacin baya. Yaya tace, “Har zuciyar ki kuma Ameena?.” Tayi murmushi yace, “Yaya sanin baya kika yi min, duk abinda kike tunani yanzu babu shi.” Ameena ta kalli Zaytun da take ta wasan ta tace, “kayan ta sun k’are ma ba’a d’auko mata da yawa ba.”

“Ina Amira tazo yanzu na saka a kaita ta d’auko mata” Yaya Adam ya fad’a yana shigowa ciki yana kallon su. Ya sake cewa, “ba kina da mota ba?.” Ta d’aga kai alamun eh yace, “Za’a d’auko ta yanzu ai Amira tasan inda key din yake ko?.” Nan ma d’aga kai tayi yace, “Duk wani abu da kika san kina so na amfani ta dauko miki shi yanzu, sauran kayan kuma in ya kawo takardar sakin sai aje a d’auko komai da yake mallarkin ki.”

Ameena tace, “To Yaya.”
“Kin sha magani?.”
“Eh yanzu na sha.”
“Yayi kyau” ya fad’a yana juyowa ya fita. Yaya ta bishi da kallo tace, “Gatan mu gaba da baya kenan, bamu da wanda yafi Yaya Adam. Badan shi ba da yanzu ba’a san halin da kike ciki ba.” Ameena tayi murmushi tana jin dad’i a wani bangare na zuciyar ta domin kuwa ya karb’a mata y’ancin ta. Kai ta girgiza kawai bata ce komai ta kasa fassara a wanne yanayin zuciyar ta take Karb’ar sakin da ake ta ambata.

*Bayan kwana biyu.*

Rukayya tana zaune a d’aki hannun ta rik’e da waya tana dannawa Umma ta shigo ta k’araso inda take zaune tace, “ke Rukayya wai har yanzu Umar d’in bai kuma kiran ki ba?.” Rukayya tace, “Eh Umma, tun bayan nan dai bai sake kira na ba gaskiya.”

“Rukayya ko dai wani abun kika fad’a masa da ya saka ya fasa auren ki? Yaro mai hankali da Kamala ke kanki kin shaida hakan kin ce zaki iya auren sa amma ya d’auke kafa ba waya baya kuma zuwa?.”
“Wallahi Umma babu abinda nace masa ban San dalilin Hakan ba.”
“To Allah yasa ba guduwa yayi ba, ya Allah ka yanke wa yarinyar nan ta tashi ya bar gidan nan kafin azumin Ramadan ya sake dawowa, Allah kana ji kama gani” Umma ta fad’a tana d’aga hannu sama.

A zuciyar Rukayya ta asma da amin da ita kanta rashin waiwaiyar ta da Umar din ya daina yi ya dame ta sosai, da shine kiran ta a waya duk da daman bai cika waya sosai ba saboda yana da aure amma yana yi mata message wanda zai saka taji dad’i amma yanzu gabad’aya ya daina bata san dalilin hakan ba.

Umma ta sake kallon ta tace, “kuma ke kin kira shi?.” Rukayya tace, “eh na Kira Umma amma bana samun sa a waya.” Umma tayi Ajiyar zuciya kawai ta fita babban burin ta Allah yasa dai Umar ba guduwa yayi ba dan yadda Baba yake fad’ar nagartar sa tayi mata sha’awar auren sa sosai.

A bangaren Ibrahim tunda Hajiya tayi masa maganar Rukayya shikenan ya kasa cire maganar daga zuciyar sa abu kamar tsafi, ko rufe idanun sa yayi fuskar ta zai gani sai yayi da gaske yake yakice tunanin ta yayi bacci. Gabad’aya ya rasa sukuni ya rasa abinda zai yi zuciyar sa na Karb’ar abinda Hajiya tace amma shi kuma yana so ya yacike abin dan gani yake kamar bazai yu ba.
Ganin tunanin zai dame shi sai ya mik’awa Allah lamarin sa ya dinga addu’ar abinda yafi alkhairi Allah ya zaba masa amma duk da hakan bai daina tunanin Rukayya ba.

Kamar ko yaushe da daddare mahaifin sa da mahaifiyar sa suna zaune a cikin hasken kwan fitila wanda yake amfani da hasken rana guda biyu shima yana zaune yana jira mahaifin sa ya gama cin abinci ya sanar dashi abinda yazo ya fad’a masa. Kallon sa Alhaji yayi yace, “Ibrahim fad’i abinda yake bakin ka.” Ibrahim yace, “Alhaji daman akan gidan ne, an siyi nawa kamar yadda na fad’a maka wanda ya siya ya k’ara mana kud’i a akai dan so yake a bashi ya rushe ya shigar dashi cikin ginın da yake yi da gaggawa. To yau ya bani kud’in naira million takwas ya siya, kuma kamar yadda ka sani yadda aka yiwa gidan kudi bai fi miliyan shida ba.”

Ya ajjiye kudin a gaban Alhaji yace, “Akwai wani gida da akayi min talla a can gaban mu wajan Sani mainagge shi kuma miliyan shida amma bai kai nawa girma ba sai yafi nawa ginın zamani kuma location din sa yafi wancan kyau gaskiya. Mun gama magana da mak gidan nace ina so ni yake jira na saka kud’in ni kuma nace zanyi shawara da kai abinda kace shi za’a yi, amma su Yaya duk sun je dinga gidan sun ce kuma yayi a siya.”

Alhaji yace, “to ka siya mana tunda yayyen ka sun ce yayi ai kamar mace ne Ibrahim, Allah ya sanya alkhairi ya cigaba da bud’e maka kofar alkhairi a rayuwar ka.” Ya amsa da amin kafin yace, “Naira miliyan shida tana cikin banki na ita zan sakawa mai gidan, wannan kuma ragowa ne nake neman shawarar abinda za’a yi da ita.”

Alhaji yace, “kayi aure kawai Ibrahim.” Hajiya tace, “shine magana, kayi aure tunda ka samu sabon gida ka saka amarya a ciki.”
Ibrahim yayi murmushi yace, “Zanyi Alhaji, amma kafin nayi nafi a d’an juya kud’in, duba da hidimar aure a yanzu za’a dauki lokaci ayi wannan ayi wancan kafin lokacin an juya wannan kudin sun zama wani abu, in Allah ya saka albarka sai kaga da riba za’a yi hidimar auren gabad’aya. Shine nake neman shawarar abinda za’a yi dasu.”

Alhaji ya girgiza kai yace, “Wannan gaskiya ne Ibrahim, abinda zai faru ka ajjiye a hannun ka ko nace ka saka su a banki suma kafin ayi tunanin abinda za’ayi dasu. Kaima kamar mutum dah meye na tawo da kud’i tsirara haka Baka tsoron a biyo ka.” Hajiya tace, “ka kwashe kayan gidan maka ne yo?.”
“Ni bani da kaya a gidan, kayan ciki na Fiddausi ne dan abu kad’an aka d’auka a gidan sauran duk suna nan ban san me zanyi dasu ba. Amma zan saka a kwashe a kai gidan su.”

Hajiya tace, “to hakan yayi, Allah yayi albarka.” Ya amsa da amin nan yana jin dad’in albarkar nan da iyayen sa suke saka masa sosai. Alhaji yace, “ka samu wacce kake so din ne ko itama ba yanzu ba?.” Ibrahim yayi shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, “Eh na samu Alhaji.” Alhaji yayi murmushi yana kallon sa yace, “a ina take?.” D’agowa yayi ya kalli Hajiya kamar zaiyi magana sai ya fasa yace, “Hajiya zata yi maka bayanin ta Alhaji” tana fad’a ya tashi ya fita yana murmushi dan yana jiyo muryar Hajiya tana cewa, “ja’irin yaro da kace baka yi.” Sosai yake jin farin ciki a zuciyar yana ji a ransa lokacin da zai fara sabuwar rayuwa yayi.

A washe garin ranar da yamma ibrahim yaje gidan su Rukayya a matsayin me neman auren ta, mahaifinta ya nuna farin cikin sa sosai ya kuma bashi lokacin da zai dawo su gaisa da ita Rukayya din amma kafin nan yace ya bashi lokaci.

Bayan tafiyar sa bai tsaya sanya ba kai tsaye gidan su Fiddausi yaje ya nemi ganin mahaifin Fiddausi dan su tattauna a kan maganar Ibrahim. Koda aka fad’a mahaifin Fiddausi ga mahaifin Rukayya yana neman sa ai ba tsaya ya karasa abinda yake yi ba ya fito dan su gaisa. Iso ya yiwa Baba har d’aki suka zauna Abba yace, “Alhaji Khasim ya gida ya kuma iyalai?.” Baba yace, “wallahi Alhamdulillah kowa da kowa lafiya lau.” Abba yace, “ma sha Allah, amma dai Lafiya ko?.” Baba yace, “Lafiya zance, batu ne akan auren Rukayya cikin ikon Allah lokaci d’aya Allah ya fito mata da mazajen aure guda biyu.”

Abba yace, “ma sha Allah, Kaji lokacin da ake jira yazo kenan ko?. Su waye an ina suke?.”
“D’aya dai sunan sa Umar a nan k’ofar nasarawa iyayen sa suke shima a nan yake da aure, yana da mata da yara. Kwana biyu ma muka ji shi shiru mun d’auka ko ya fasa ne ashe tafiya yayi aka sace wayar sa gabad’aya shiyasa ba’a jin sa sai da ya dawo ya sake sabon layi d’azu yake sanar dani. Na yaba da hankalin sa sosai dan ban bashi damar ganin Rukayya ba sai da nayi bincike a kansa sosai ma kuwa, ta b’angaren halayya da gidan sa babu wata damuwa.”

Abbah yace, “to Alhamdulillah, wannan shine fatan da muke yi ai. Ba kud’i muke nema ba mu Jin dad’i da kwanciyar hankali, Na biyun fa?.”
“Na biyun yanzu yazo ya same ni muna rabuwa nazo wajan ka.”
“Waye shi Alhaji Khasim?.”
“Ibrahim tsohon mijin Fiddausi.”

Abba ya girgiza kai cike da mamaki yace, “Ibrahim dai wanda suka rabu da y’ar wajena Fiddausi?.” Baba yace, “shifa, ban bashi lokacin ganin ta ba ya kawo kansa ne matsayin me neman auren ta abinda ya saka ban ce ya ganta ba saboda alaqar dake tsakanin Fiddausi da Rukayya, sannan kuma meye ya raba auren sa da Fiddausi har da zai zo sake neman aure?.”
Chapter 39 · 0% Book details