← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 42

Sashe 42

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ammah ta kalli Abbah tace, “Har abada bazai sake samun mata kamar Ameena ba, wannan kuma da yake yake da ita sai yayi dana sanin da bai tab’a yi ba a rayuwar sa, kokari take ta mallake shi sai taje ta mallake shi kad’ai dan ni walalhi bazan yi wani abu akan Yusuf ba, taje ga rike na bar mata” tana fad’a ta tashi ta bar wajan tana goge hawaye zuciyar ta nayi mata d’aci dan ji take kamar Humaira aka yiwa abinda aka yiwa Ameena.

Abbah yayi murmushi yasan ciwo take ji a ranta dan tana son Ameena sosai tana kuma jin zafin abinda d’anta ya aikata mata, amma ya za’a yi hakan shine mafita zaman sa da Ameena cutarwa ne gwara ya sake ta kamar yadda Yayan ta ya nema, ya zauna da wacce yake so itama ta samu wanda yake sonta zai kula da ita ta zauna dashi amma Yusuf ya gaza barin sa da Ameena babbar illa ce. A bayyane Abbah yace, “ai tunda rashin sauke hakki ya shigo cikin maganar nan ta shafe komai, domin ko a addini zaman auren su akwai cutarwa a ciki, balle ga abubuwa Mara dad’i kamar ba ni na haife shi ba” sai kuma Abbah ya mik’e tsaye yace, “Ai ka haifa ne baka haifi hali ba, Allah yasa mu dace” ya fad’a yana shiga ciki a zuciyar sa yana jin yayi daidai ya aikata abinda ko mahaifin ta yana raye abinda zaiyi kenan.

End of book2🫠
Naje Hutu🚶‍♂️

#Mai daki
#Book2
#End
#paid
#Nana Haleema
Chapter 42 · 0% Book details