← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 42

Sashe 17

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

#Mai daki
#Nana Haleema
#book2
#Paid
#500.

Book2
011

A haka ya fito daga band’akin bayan ya sake yin wanka yayi alwala, kallon ta yayi tana kwance har lokacin tana bacci ya lumshe ido tuno yanayin su na jiya tsigar jikin sa ta tashi yayi saurin kawarwa kar alwalar ta karye ya saka doguwar riga ya ‘karasa inda take kwance ya tsuguna yana bubbuga fuskar ta yace, "My love! Tashi muyi sallah lokaci ya k'ure."

Bud’e ido tayi da suka yi ja da nauyi suka had’a ido yace, "Ki tashi ki yi sallah lokaci yana tafiya" yana fad’a ya juya ya hau kan carpet ya tayar da sallah dan kar lokaci ya k’ure ita bata tashi ba shima bai tashi ba. Tana tashi zaune idanun ta kan kud’in jiya suka kai suna nan wajan kusa har lokacin ta murza idanun ta ta mik’e dak’yar jikin ta duk yayi tsami ta shiga band’aki. Ta jima a ciki sannan ta fito lokacin ya idar da sallah yana ganin fitowar ta ya tashi da sauri ya k’arasa inda take ya rik’o hannun ta ya zaunar a kan gado yace, "Sannu ki yi a hankali."

Zama yayi a gefen ta kawai sai ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a kafad’ar sa tana kuka mara sauti. Nan da nan hankalin sa ya tashi ya rud’e sosai jin masoyiyar sa tana kuka ya d’ago fuskar ta yace, "Menene kuma My love? Meye na kukan?."
"Na gaji, Kaina ne yake min ciwo, bacci nake ji sosai."
"Sorry, nasan kina Jin bacci, Kiyi sallah sai ki koma ki kwanta, zan taimaka miki da tausa" ya fad'a yana mik’ar da ita tsaye tace, "Bani da kaya."

Bai amsa ba ya fita ta sake kallon kud’in tana tunanin abinda ya kamata tayi ya sake shigowa da riga doguwa da hijjabi ta saka ta tayar da sallah, dakyar tayi sallar ana yi ana langwabewa tana idarwa ta tashi ta koma ta kwanta shima ya kwanta a gefen ta yana matsa mata jikin ta dan sam baya son abinda zai b'ata mata rai. Jin ta yake a jikin ga sosai fiye da baya haka baya son yin nisa da ita.

Sun jima suna baccin har goma na safe ta gota ta riga shi farkawa tana ganin bacci yake ta zabura ta mik’e zaune, zama tayi na wani lokaci kafin ta mik’e tsaye a hankali ta k'arasa inda kud’in yake ta kalle shi taga bacci yake sosai bama inda take yake kallo ba ta saka hannu ta d’auki rafar dubu hamsin guda biyu ta fita daga d’akin a hankali.

Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa wacce ta kama ta sosai ta dawo d’akin har lokacin bacci yake ta kwashe kayan nasa da yake wajan ta saka a cikin wardrobe ta kwashe ragowar kud’in ta zuba a cikin drawer duk dan kar yayi zargin wani abun ya saka take aikin da bata yi niya ba. A kan kujerar da take d’akin ta zauna tana zama yana bud’e ido ya tashi zaune tare da kallon gefen sa nan ya hango ta a zaune ta rufe ido tana rik’e ciki kamar bata san ya tashi ba.

Da sauri ya sakko ya k’araso yace, "My love Lafiya?." Ta kalle shi sai ta d’an gyara zama tace, "Yunwa nake ji sosai, naso kafin ka tashi nayi breakfast amma na kasa ko k'asa ban sauka ba."
"I'm sorry Ina zuwa" ya fad'a yana fita daga d’akin ta tashi ta k’arasa wajan tagatana tsaye har taga ya fita daga b’angaren ta ya shiga b’angaren Ameenatu.

Da sauri ta juya sai kuma taja ta tsaya tace, "Wayyo Allah." Sai ta cigaba da tafiya ta fara bud’e drawer ko zata ga wasu kud’in amma babu komai iya kud’in jikin sa da ya shigo dasu ne kawai. Numfashi ta sauke ta kama k'ugu tace, "Da alama kud’in dai suna b’angaren waccan kenan, lallai dole nasan abinda zanyi dan nasan bazai rasa ajjiye kud’i a gida ba,
Dole nasan abinda zanyi na shiga na samo kafin lokaci ya k’ure na tara abinda na tara.” Waya ta d’auka ta koma bakin tagar da kar ya dawo bata sani ba ta kira Yayar ta Fauzy tana d’auka Fauzy tace, "Amaryar Yusuf, kece da safe haka?."

Kafin tayi magana taji maganar Umma da alama tana wajan ta karb’i wayar daga hannun Fauziyya tce, "ke ya ake ciki komai dai yayi ko?." Asiya sai taji kunya ta kamata amma haka tace, "Eh Umma, kuma maganin yayi aiki sosai wallahi ya rud’e a kaina gabad’aya."
"Ni na amince da aikin malam ai, yanzu ya battyn wani abun me ya Baki?."
"Umma ai daman cewa yayi tukwicin first night daina Saudia zamu tafi yau kinga babu abinda zai bani."
"Ke kuma baki samo ba? Na fad’a miki naci bashi a auren nan a yanzu ya kamata ki san abin yi domin yanzu yana mararin ki komai kika yi bazai kawo ke bace."

Asiya tace, "Na samo dubu d'ari dai a safiyar nan, kinga nan sabon gida ne bazai fara ajjiye kud’i a nan ba, amma da zarar mun yi tafiya nan mhn dawo zan shiga har b’angaren nata na bincika kinga in na d’auka a can ai bazai kawo ni bace." Umma tace, "To yayi kyau, Fauziyya zata zo sai ki bata kudin ta tawo dasu kafin a fara tara min mutane a waje." Da to ta amsa tana kashe wayar tace, "Umma nima fa Ina so na tara wallahi, ba duka zan dinga bayarwa ba in na samo."

Yusuf kuwa lokacin da ya shiga b’angaren Ameena babu kowa a k’asan amma a gyara yake yana ta khamshi har zai hau sama yaji motsi a kitchen yana shiga kitchen din yaga Amira ce ta gama hada breakfast. Tana ganin sa ta jiyo tace, "Ina kwana Daddy."
"Lafiya lau Amira, abincin waye?."
"Na mu ne nida Aunty bata tashi bane har yanzu."

Ya d’an sosa kai ya bud’e abincin yaga dankali ne da Kwai ya juya ya d’auki plate ya zuba ya rage kad’an a ciki yace, "Zan kaiwa sabuwar Auntyn ki, ki samu ki sake had’a wani.” Amira kamar ta kifa masa mari haka taji amma bata ce komai ba sai to ya gama ya fita tayi tsaki tace, "Allah sai ya sakawa Auntyna."

Koda ya koma b’angaren Asiya sai da ya had'a mata tea tun a k'asa sannan ya koma saman ya same ta a zaune a inda ya barta ya k’araso yace, "Sorry my love na jima ko?." Zama yayi gefen ta ta kalle shi bayan ya bata tea din a hannun ta tace, "dafawa kayi?." Kai ya girgiza yace, "No a wajan Ameena na karb’o miki." Tayi murmushi tace, "Allah sarki Auntyna tana sona." Murmushin shima yayi dan yana kin dad’in yadda take nuna tana son Ameena dan yasan ta bangaren ta bazai samu matsala ba sai dai ya b’angaren Ameena.

Bar mata yayi ya tashi ya shiga bandaki ita kuma ta fara ci, so take tayi iyayi t rage amma Ina bazata iya ba yunwa take ji in ta rage ta cuci kanta haka ta cinye tasss ko kad’an bata bari ba lokacin da ya fito ma ta gama cinyewa. Kallon ta yayi ya murmusa yace, "Gwara da kika cinye dan ko baki cinye ba na fito sai na saka kin cinye."

Bata ce komai ba tayi shiru kanta yana ‘kasa har ya saka kaya yace, "Kayana guda d'aya ne a nan daga wannan sai wanda na cire jiya, ya kamata na d’auko daga b’angaren Ameena." Bata ce komai ba ya k’araso ya zauna kusa da ita yace, "meye kike sauke kai k'asa?." Ta girgiza kai alamun babu tace, "Ina zaka je?."
"Ina so zanje wajan Amma ne, amma yanzu zan dawo." Tayi shiru yace, "Ko Baki so naje?."

Ta wara ido tace, "ni na isa? Naga baka ci komai bane."
"Bana Jin yunwa" ya kalli Agogo yace k'arfe shida na yamma jirgin mu zai tashi, shiyasa nake so naje nayi sallama da Amma na dawo." Dad’i taji yana mamaye mata zuciya cikin farin tace, "Kwana nawa zamu yi?." Yayi shiru kafin yace, "sati d'aya dai kawai zance." Ta langwabar da kai tace, "Ba biyu baaaaa!?Har yaushe ma aka samu lokacin ibada a sati d’aya? Kaga fa ban tab'a zuwa ba."

Yace, "My love dole hakan za'a yi kin manta bake kad’ai bace ba?." Ta turo Baki gaba kamar zatayi kuka tace, "Haka ne, amma da zamu samu dama da sati biyu zamuyi kodan ibada." Yayi murmushi yace, "bana son wannan fushin naki da damuwa zan san abinda zanyi, bara naje na dawo."
"To sai ka dawo." Murmushi yayi kawai ya tashi zai fita tace, "Akwai kud’in ka da ka bari akan mirror na saka a drawer."

Ya dafe kai yace, "na manta ma, sune kawai a jikina kuma" ya fad'a yana yin hanyar wajan drawer din ya d’auki kudin ba tare da ya duba ba ya saka a aljihu ya k’araso inda take ya mata kiss a goshi ya fita.

Kamar zai shiga b’angaren Ameena sai kuma ya fasa in ya dawo ya shiga ya shiga mota zuwa gidan su. A babban falo ya samu Ammah da Abbah suna zaune ya shiga da sallama duk suka amsa ya zauna a k'asa ya gaishe su Abbah yace, "Ya kwanan amarya?." Yusuf yace, "Alhamdulillah." Abbah yace, "To Allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin su." Ya amsa da amin kafin yace, "Daman nazo na sanar daku anjima da la'asar zamu tafi Saudia nida ita."

Abbah ya gyara zama yace, "Ma sha Allah, amma ita kuma uwar gidan fa?. Gadin gidan zaku barta?.” Yusuf ya sake k’asa da murya yace, "Eh Abbah da yake kwana biyar zamuyi bada ita zamu tafi ba." Sai a sannan Ammah tace, "Ita zaku bari gadin gidan kenan?." Yusuf sai da gaban sa ya fad’i dan bai so ma tayi magana ba yace, "A'a Ammah, saboda ita ma na saka kwanakin babu yawa dan kar a shiga lokacin ta." Ammah tace, "Yau in kuka tashi sai gobe zaku shiga madina, kwana biyu zaku yi a madina kenan ku wuce makka kuyi kwana biyu sai ku dawo?."
Chapter 17 · 0% Book details