Sashe 18
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya girgiza kai yace, "Eh Ammah baza mu jima ba." Abbah da yake jin su ya mik’e yace, "To Allah dawo daku lafiya, ni zan wuce Abuja sai jibi zan dawo." Yusuf ya tashi da niyar raka Abbah da nufin daga nan ya gudu yaji Ammah yace, "in ka raka shi ka dawo." Da to ya amsa badan yaso ba suka fita Abbah ya shiga mota driver yaja suka tafi shi kuma ya juyo gaban sa yana fad’uwa.
Sai bayan ya zauna tace, "Ka fad’awa Ameena maganar tafiyar?." Yace, "Eh ta sani, amma yanzu zan sake tuna mata na shiga tana bacci tun d’azu." Ammah tace, "Ka kasance mai adalci dan Allah Yusuf kar ka cutar da ko wacce a cikin su kaji?."
Jin nasiha take masa ba fad’a ba ya saka yayi murmushi hankalin sa ya kwanta yace, "in sha Allah Ammah zanyi iya bakin kokarina wajan ganin ban cutar da kowa ba." Ammah taji dad’in kalaman sa tace, "To Allah ya baka iko ya zaunar daku Lafiya." Ya amsa da amin bai jima ba ya mata sallama ya tafi gıda.
Ameena kuwa a zaune ta kwana bacci sai b'arawo sai bayan asuba bacci ya d’auke ta mai nauyi hakan ya saka ta jima tana bacci. Koda ta tashi da ciwon kai ta tashi tayi wanka ta saka doguwar Riga mara nauyi kamar yadda ta saba ta fito ta kalli gefen gadon taga babu Zaytun tasan tana wajan Amira. Wayar ta tayi ‘kara ta duba ganin sunan Yaya ya saka ta d'auka ta saka a kunne.
Yaya a tausashe tace, "Aminene ya kike tashi yau din?." Ameena tace, "Alhamdulillah Yaya, ciwon kaine kuma yanzu zan sha magani." Yaya tace, "Kin karya kuwa?."
"A'a, fitowa daga wanka kenan yanzu na tashi sallar azahar zanyi sai na sauka na ci abinci."
"Ki dai ci abinci kar ki ci rashin cin abincin ki ba shi zai hana mijin ki zama da wata ba, ki saki jikin ki kawai Allah ya kaddara matar sace babu wanda zaki yi."
Ameena tace, "Haka ne Yaya, yanzu zan ci in sha Allah." Yaya tace, "in kin gama ki kira ni." Ta amsa da to ta kashe wayar. Tashi tsaye tayi ta yaye lalube ta kalli gidan Asiya sai kuma ta rufe labulen ta saka mayafi ta tayar da sallar walha. Tana raka'ar k’arshe Amira ta shigo da tray a hannun ta ta zauna a k’asa Ameena tayi sallama Amira ta kalle ta tace, "Aunty Ina kwana."
Zaytun ce ta shigo ganin Mummyn nata a zaune ta tawo a guje ta fad’a jikin ta Ameena ta rik’e ta tana dariya tace, "Yar gidan Aunty Amira, me ta baki haka naji kin koshi?." Zaytun tace, "Abinci muka ci." Ameena ta kalli Amira tace, "Aunty Amira kin tashi lafiya?."
"Lafiya lau Mummy, ga abincin ki."
"Sannun ki da kokari.”
"Yauwa." Ameena ta d’auki tea din da ta had’a mata ta fara sha tace, "Daddyn Zaytun ya shigo?."
Amira tace, "Eh ya shigo kitchen yaga na gama soya dankali lokacin da kwai ya d’auki plate ya zuba ya fita." Ameena ta girgiza kai kawai bata ce komai ba dan bata so ma ta kawo bai neme ta ba a zuciyar ta.
A b’angaren sa yana dawowa gidan Asiya ya shiga ya tarar da ita zaune da Fauziyya suna hira suka gaisa ya wuce zuwa sama yayi alwala lokacin ana kiran sallah ya sakko ya shiga masallaci ya dawo ya shiga wajan Ameena.
Kai tsaye d’akin ta ya shiga tana cin dankali ya shiga da sallama suka amsa ita da Amira a tare, a guje Zaytun ta tashi tana fad’in, "Daddy!." Ya d’auke ta yana mata wasa yace, "ya naji kinyi nauyi, me kike ci?." Cikin maganar ta da ba'a ganewa sosai tace, "Aunty Amira tana bani abinci." Yayi dariya ya zauna yace, "Lallai Aunty Amira tana son Mamana."
Amira ta tashi ta fita Zaytun ta sauka daga jikin sa tabi bayan ta a guje ya bita da kallo yana murmushi kafin ya dawo da kallon sa ga Ameena da take zaune tana shan tea kamar bsta ganshi ba. Kallon ta yake yi sosai yaga ta rame musamman daga wuyan ta zuwa fuskar ta kafin yayi magana tace, "Ina kwana." Yace, "Lafiya lau, baki da Lafiya ne?." Ta girgiza kai tace, "Lafiya nake."
"Amma kika rame haka?. Ni sai naga ramar nan taki kamar gaba take yi.”
Ta sauke numfashi ta kalle shi tace, "na jima a haka." Ya bita da kallo na wani lokaci kafin yace, "baki tambaye ni ya amarya ba?." D’ago kai tayi ta kalle shi sai kafin tayi magana sai yace, "Magana nazo muyi." Tace, "to Allah yasa ba laifi nayi ba."
"Magana ce akan tafiyar da zamuyi nida my love anjima."
Ya gyara zama yace, "Lokacin da mukayi aure munje k'asashe kusan hudu ko biyar ma ko?." Bata amsa ba sai kallon sa da take yi daman yasan baza ce komai ba ya sake cewa, "Ko wacce k'asa Ina jin sati d'aya muka yi dan munfi sati hud’u bama Nigeria sannan muka dawo, anyi haka nasan kin sani. Nayi hakan ne saboda ke matata ce kuma Ina sonki Ina so mu samu kusanci nida ke." Nan ma shiru bata ce komai ba sai kallo kawai da take bin sa dashi tana so taji karshen maganar.
"Zamu tafi Saudia da Asiya anjima Ina so muyi sati biyu sati d'aya a makka sati d'aya a madina, hakan bazai faru ba dole sai da taimakon ki dan kinga yau ya rage kwanaki shida kwanakin amarcin ta ya ‘kare kinga kenan dole sai an shiga kwanakin ki. Ina so dai da zuwan mu da dawowar mu muyi sati biyu shine nazo wajan ki muyi magana."
Ameena da take jin sa ta sunkuyar da kai tayi murmushi ta d’ago ta kalle shi tace, "me kake so nayi yanzu? Kawai kace karshen maganar.” Yusuf yace, "sati d'aya nake so ki kara mana nida ita saboda mu samu lokacin ibada sosai, kwana shida baza mu nutsu ba in kika duba kafin ma muje madina Mun ci kwana d'aya." Ameena ta gyara zaman ta tace, "Kamar ya kake nufi ban gane ba?."
"Ina nufin ki bar min kwanakin bana so ace na cutar dake ko wani abun shiyasa nazo na same ki. Bana son shiga hakkin ki shiyasa nake tambayar ki.” Ta d'ago zatayi magana ya katse ta yace, "Ni ko siya ma zanyi, duk kwana d'aya zan baki dubu dari kinga dubu dari bakwai kenan, sai na baki naira miliyan d'aya fatana kawai ki amince."
Wani dogon numfashi taja wanda sai da ya kalle ta yaga tayi shiru kawai bata ce komai ba sai kanta da ta sunkuyar tana jin zuciyar ta na bugawa sosai. Ganin hakan ya saka yace, "Ameena banyi miki dole ba, in kinga zaki iya to in baza ki iya ba bance lallai ba kar na tafi Ammah tace in ban dawo ba sai ta tsine min. Bana son boye-boye kin sani ki fad’a min kawai."
Ta d’ago ta kalle shi kamar zatayi magana wani abun ya tokare ta a kirji sai ta kasa ta sake yin shiru bata ce komai ba, sun jima a haka kafin yace, "ke nake jira zuwa anjima zamu tafi airport." Kai take girgizawa ta kalle shi tace, "Duk abinda zakayi daman kana neman izinina ne? Ka tab’a zuwa kace min neman izinina kazo nema akan wani abun? Meyasa kazo yanzu Daddyn Zaytun? Komai kai tsaye kake yi wannan ma kawai kayi babu komai ai tunda ka Saba.” Kallon ta yayi kamar zai ce wani abun sai ya canja maganar yace, "Kenan kin amince?." Da hannu tayi masa alamar yaje kawai.
"Magana nake so kiyi min ba nuni ba."
"Ai ba sai nace ba, duk abinda kaga daidai ne kayi kawai Yusuf basai kaji ta bakina ba, komai kayi a wajan ka daidai ne dan haka kayi kawai basai nace komai ba.”
"Okay na gode, babu abinda kike so?.” Ya fad'a yana mikewa. Ta girgiza kai tace, “ka tab’a cemin akwai abinda nake so ne daman? Kawai kaje.” Har zai fita ya dawo yace, "in Ammah ta tambaye ki me zaki ce mata?."
"Ina ruwan ka da abinda zance mata? Dan girman Allah ka tafi kawai Allah ya kaiku Lafiya ba shine abinda kake so ba? Kaje kawai Yusuf kar ka damu dani kamar ko yaushe kaje kawai.” Kallon ta yake sai yaji wani iri a jikin sa, jikin sa yayi sanyi sosai haka zuciyar sa ya kasa tafiya sai kallon ta da yake yi duk da ba kuka take ba amma kana kallon ta kasan akwai damuwa sosai. kamar zai magana sai kuma y fasa ya fita zuciyar sa na sake fad’a masa kamar baiyi daidai ba wata zuciyar na fad’a masa daidai yayi ai ta amince tunda ya fad’a wannan tunanin ya koma b’angaren Asiya.
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema.
Book2
012
Sai bayan taji ya kulle ‘kofa ta kalli inda yabi ta ajjiye shayin hannun ta zuciyar ta kamar an tsagata an dasa mata dutse haka take ji a ciki saboda taurin da tayi mata. lumshe ido tayi kawai jikin ta ya d’auki zafi lokaci d’aya hawayen idanun ta sun k’afe babu su babu alamar su sai ja da idanun ta yayi.
Bata so ta dinga saka lamarin sa a zuciyar ta a lokacin amma bazata iya ba in tace bata jin zafi akan abubuwan da yake yi mata tayi k’ayar kawai tana so ta dinga kawarwa ne dashi da matar sa kar su dinga damun ta. Tashi tayi daga inda take ta koma kan gado ta zauna kalaman sa suna yi mata yawo a kanta.