← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 42

Sashe 40

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba yayi murmushi cikin jin dad’i yace, “Wato Allah gwanin hikima ne, duk yadda ka kai ga k’aguwa akan abu baka isa kayi ba sai lokacin ka yayi, sai lokacin da ya tsara maka yayi sannan abinda ka jima kana jira zai zo ko baka shirya ba, in kuma kana addu’a sai ya baka abinda baka yi tunanin sa ba. Wato Alhaji Khasim inda zaka amince dani da nace kar ka aurawa kowa Rukayya indai ba Ibrahim ba.”

Baba yace, “Ibrahim din?.”
“Shi fa, domin kuwa in ka bari irin su Ibrahim ya sub’ucewa Rukayya kafin ta samu kamar sa Wallahi Allah za’a jima domin basu da yawa a duniya. Batun alaqar su da Fiddausi wannan ka ajjiye ta a gefe in ma lokacin da Fiddausi take gidan sa ne ai ba aibu bane dan ya aure ta balle basa tare, maganar mutuwar auren sa da Fiddausi kuma komai ya faru Fiddausi ce fa jawo wallahi, duk abinda ta fad’a mana a kansa k’arya take yi na samu labarin komai a inda bata yi zaton zan ji ba. Tun tana gidan mijin ta yake tare da wanda ta aura a yanzu yake wure mata kunne in ta fito daga gidsn mijin ta zai aure ta a haka har ta kashe auren.”

“Daman kuma Fiddausi y’ata ce amma hakan bazai hana ni fadar gaskiya ba, akwai son kudi da son rayuwar kudi wannan dalilin ya saka bata ganin alkhairin Ibrahim komai yayi ba burge ta ba. Ta kashe auren taje ta auri wanda ko cikakken bincike Kawun ta baiyi ba saboda shima irin tane ya cika masa aljihu da kud’i shi kuma ya bashi ita dan anga bana k’asar a lokacin. Ina baka shawara Alhaji Khamsin indai har Rukayya na son Ibrahim kar ka sake ya kubce maka, domin addu’ar da ka jima kana yiwa Rukayya na neman miji na gari Allah ya amsa ya bata miji nagartacce kamar Ibrahim.”

Baba yayi murmushi cikin farin cikin da ya mamaye masa zuciya yace, “amma na jima banji abinda yayi min dad’i kamar wannan ba wallahi, ni da yazo daman mamaki ne ya hana ni yin komai nace yaje zan neme shi sai naji ta bakin ka yanzu da muka tattauna ji nake an cire min duk wata fargaba a akan sa walalhi.”
“Baza kayi farin ciki bama sai ka bashi ita, mutum ne da ya da sa girman iyalan sa sosai, in kaji fad’i tashin da yake yi akan Fiddausi wallahi sai ya baka mamaki sai kaji meyasa ma ta yarda ta rabu dashi. Tunda suke ina jin auren su shekara shida ne ko biyar bai tab’a kawo min k’arar ta b wallahi, itama bata tab’a zuwa tace ga damuwar sa ba sai da aka fara wure mata kunne shaidan yana taya ta, yayyen ta Sune suke auren masu kud’i amma wallahi ta fisu kwanciyar hankali, rashin gode Allah ne irin nata ya saka ta kashe auren. Alhaji Khasim ka bashi ita indai zata iya zama dashi tana son sa zance ya k’are.”

Baba yace, “abinda nake tunani kenan nima amya zata amince ta auri tsohon mijin Fiddausi? Akwai amince tsakanin su kasan mata yanzu sai ace anci amana.” Abba yace, “Addu’a kawai zamuyi Allah yasa shine mijin ta dan alkhairin da muke nema mata fa Ibrahim ne.” Baba sosai ya gamsu da bayanin Abba yace, “na gamsu da bayanin ka sosai Alhaji, Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci.”

Abba ya amsa da Amin yace, “In komai ya daidai a sanar dani mu fara shirye-shirye abu ne tuwo na kuma mai na, wallahi abun nan yayi min dad’i fiye da tunanin ka.” Mik’ewa Baba yayi yace, “nima kalaman ka sun wanke min dukka tantama ta akan Ibrahim, badan bana son ce mata jeki ga zab’ina ba wallahi da nace jeki ga Ibrahim, to na fiso na bata zab’in ta itama.” Tare suka fito har k’ofar gida suna sake tattaunawa akan lamarin kafin Baba ya tafi yana fatan Allah yasa Rukayya ta amince da auren Ibrahim.

#Mai daki
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema.

Book2
025

Baba yana komawa gida ya samu Rukayya a tsakar gida tana wanke hijjabi ta juyawa k’ofa baya ya kalle ta da murmushi a zuciyar da yana fad’in, _in sha Allah k’arshen zaman ki a gida yazo Rukayya, kema ki tafi gidan mijin ki kije ki huta ki yi rayuwar aure kamar kowa. In sha Allah lokacin yazo abinda ake jira tsahon shekaru yazo.” juyowa Rukayya tayi taga Baba a tsaye yana kallon ta sai murmushi yake yi sai ta sha jinin jikin ta itama tayi murmushi tace, “Baba Sannu da zuwa.”

“Yauwa Rukayya, in kin shiga ciki ki kiran min Umman ku.” Ta amsa da to ta shiga ta fad’awa Umma sannan ta fito ta cigaba da abinda take yi. Tana tsaye Umma ta fito ta shiga d’akin Baba ta zauna tace, “Rukayya tace nazo.” Baba yace, “eh, abin alkhairi ne ya sake tunkaro mu.” Umma tace, “to me ya faru?.”
“Wani ne yazo ya sake samu na Tana neman auren y’ar ki.”
“Rukayya!” Ta fad’a tana wara idanu tare da dafe kirji cikin farin ciki.

Baba yayi murmushi yace, “ita fa, ga kuma Umar ya dawo da k’arfin sa zancen aure yake so ayi a wuce wajan da gaggawa.” Umma tace, “Alhamdulillah! Allah maji rok’on bawa. Rukayya ta dai itace maza biyu suka fito neman auren ta da gaske ba wasa ba?.”
“Wallahi fa, lokacin yayi ne shiyasa.”
“Waye shi na biyun da yanzu zo Alhaji?.” Baba yace, “Ai kin San shi ma, Ibrahim ne tsohon mijin k’awar ta Fiddausi.”

Sak Umma tayi tana kallon Baba da mamaki kafin tace, “Wai da gaske kake? Ibrahim dai mijin k’awar ta Fiddausi da ya saki kwanakin baya?.” Baba yace, “shifa.”
“İkon Allah! Shi kuwa ya kasa rik’e fiddausi har ya sake ta yanzu sai ya biyo yace Rukayya yake so? Kuma ya manta Rukayya da Fiddausi aminai ne sosai ko ka manta ne?.”

Baba yayi murmushi yace, “ban manta ba, hasalima ni farin ciki nake yi sosai da hakan dan wallahi in Rukayya ta aure shi zan fi kowa murna.” Umma tace, “Meyasa kake farin ciki?.”
“Bayan tafiyar shi Ibrahim din ai wajan mahaifin Fiddausin naje, ashe yarinyar Fiddausi itace ta kashe auren da kanta komai ya faru itace ta jawo ya sake ta. A takaice dai mahaifin ta ya bada goyan baya akan auren Rukayya da Ibrahim, ya tabbatar min da nagartar Ibrahim fiye da wacce naji akan Umar hakan ya saka naji na amince da auren da d’ari bisa dari, wallahi a yanzu nafi son ta aure shi akan Umar din.”

Umma ta girgiza kai tace, “Amma ni sai nake gani kamar za’a lalata zumuncin su ne, ko da yake ba mijinta bane a yanzu ai.” Baba yace, “kawai kiyi mata addu’a wanda ya kasance alkhairi a cikin su Allah ya bata, amma zuciyata a yanzu tafi son Ibrahim.” Umma tayi murmushi tace, “in ma Ibrahim din ne daman burina ta samu na gari kuma an tabbatar da dukkan su na gari ne kaga ai Alhamdulillah.”

Baba yace, “nima shine fatana a koda yaushe Gashi Allah ha amsa lokaci yana zuwa kamar wasa. Tashi kije nima zan fita yanzu.” Umma ta tashi ta fita zuwa cikin gida taga Rukayya bata tsakar gidan ta shiga d’aki a nan ta ganta tana kwashe kayan Umman tana zubawa a cikin wardrobe.

Umma ta bita da kallo tace, “Rukayya ajjiye kayan nan kizo” ta fad’a tana zama tare da kallon ta. Ajjiye kayan tayi ta tawo kusa da Umman ta zauna Umma ta kalle ta tace, “Kin San waye ya samu mahaifin ku akan yana neman auren ki?.”
Rukayya ta girgiza kai alamun A’a amma buri kawai take taji waye a zuciyar ta, Umma tace, “tsohon mijin k’awar ki Ibrahim.” Gaban Rukayya ya fad’i bata san ta mik’e tsaye ba tana kallon Umma tace, “Ibrahim kuma Umma?.”

Umma ta kalle ta tace, “dawo ki zauna.” Ba musu ta zauna umma tace, “Eh Ibrahim, sai me dan shine ya nemi auren ki?.”
“Umma Ibrahim fa mijin Fidy, yaushe ma suka rabu da Fiddausin da zai zo yace yana sona?” Ta fad’a dan son ta tabbatar dan badan Umman bace bama bazata amince ba d’auka zatayi tsokanar ta ake yi.

Umma tace, “Bai jima da barin wajan mahaifin ki ba ya kuma tabbatar da auren ki zaiyi.”
“Na shiga uku! Yanzu Umma kuma mai Baba yace masa?.” Umma ta bita da kallo tace, “meye na shiga uku a nan?.”
“Umma mijin Fiddausi fa, Fiddausi tawa dai da kika sani mijin tane fa.”
“Tsohon mijin ta dai ba mijin ta ba” Umma ta bata amsa tana karantar yanayin kan fuskar ta ta.

Rukayya ta kalli Umma kamar zatayi magana sai ta fasa amma kirjin ta bugawa yake yi cikin tsoro da mamaki had’i da al’ajabin abun. Umma tace, “Mahaifin ki ya amince dashi sosai dan zan iya ce miki yadda ya amince dashi ko da Umar din bai amince ba, kawai dai yana so ki zab’i wanda zaki zauna dashi ne da kanki amma in a a ra’ayin sane yafi son Ibrahim dan sun tattauna da mahaifin Fiddausi a d’azu.”

Rukayya bata ce komai ba tayi shiru gabad’aya jikin ta yayi sanyi tuna maganar Fiddausi kawai take yi tana tsoron kar fa bakin Fiddausi ne ya kamata har aka zo wannan gab’ar ba tare da ta shiryawa hakan ba. Umma ta sake cewa, “abinda yake gaban ki kawai addu’a ce cikin su biyun wanda ya kasance alkhairi Allah ya zab’a miki, amma a cikin su bana son kice bakya son kowa Rukayya baki tab’a samun masu nagartar Umar da Ibrahim ba dan haka dan Allah ku tsayar da hankalin ki waje d’aya ki zab’a a cikin su hankalin kowa ya kwanta.
Chapter 40 · 0% Book details