Sashe 11
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ameena Ina kika je? Kina Ina ne?" Ya fad'a yana sake kiran ta amma Ina bata tafiya. WhatsApp ya shiga ya Kira ta voice call amma bata online ya Kama k'ugu yana sauke numfashi. "A Ina ta kwana dan Allah?. Ina taje?.”
"Asslaamu alaikum!." Aka fad’a ana shigowa falon.
A firgice ya juya ganin wacce ta shigo gaban sa ya sake fad’uwa tsoron sa ya bayyana k’arara a fili ya kasa amsa sallamar sai ido kawai da yake bin wacce ya shigo dashi dan yasan asirin sa ya gama tonuwa.
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema
Book2
007
Kallon sa take yi shima ita yake kallo kafin tace, “Yaya Yusuf Ina kwana.” Bai iya amsawa ba dan a rud’e yake gabad’aya da ganin hakan ya saka ta kuma cewa, “Amma ta aiko ni wajan Aunty Ameena, bara na hau saman wajan ta” ta fad’a tana nufar hanyar saman. Kasa mata magana yayi dan bai abinda zai ce mata ba har ta hau saman ba jimawa yaga ta dawo ta kalle shi yana inda ta bar shi a tsaye har lokacin tace, “Yaya bata nan, tana Ina?.”
“Taje asibiti” ya bata amsa a takaice yana fita daga falon ta bishi da kallon rashin gaskiya tace, “Anya kuwa abinda yake fad’a haka ne? Ya cewa Amma tana bandaki ni kuma yace min taje asibiti.” Fitowa tayi daga falon zuwa wajan mai gadi tace, “Baba Isihu ina kwana.”
Yayi murmushi yace, “Lafiya lau Hajiya Humaira.”
“Ina Aunty Ameena? ta fita ne?.” Baba yace, “Hajiya ai tun jiya da ta fita da safe bata dawo ba har yanzu, kafin shigar ki ma mai gidan yake tambayata na sanar dashi abinda na fad’a miki.”
Humaira ta girgiza kai tace, “Okay, bud’e min zan fita da mota” ta fad’a taba yin wajan motar da tazo da ita ta shiga Baba ya bud’e mata ‘kofa ta fita. Tunda Yusuf yaga fitar ta yasan ya shiga uku yau, gabad’aya fad’an Amma yake tsoro gashi bai San inda take ba balle in ta kira shi yace ta tafi wani wajan. Bashi da gaskiya shi kansa ya sani bai San abinda zai cewa Ammah ba shine babban tashin hankalin sa.
Fitar Humaira ba jimawa sosai Amma ta kira shi yana ganin kiran gaban sa ya fad’i ya dafe kai bai iya d’auka ba har ta katse aka sake Kira ya d’auka tace, “kazo Yanzun nan ina neman ka” tana fad’a ta yanke kiran yaja numfashi ya tashi ya hau saman dan dole ya amsa kira. wanka kawai yayi ya d’auki mota ya fita shi tsoron had’uwa da Amma yake bai San me zai ce mata ba gabadaya.
Da sallama ya shiga falon ta ya same ta a zaune ita da Humaira d’in ya Harare ta a ransa yana fad’in munafuka ya k’araso ya zauna yace, “Barka da safiya Amma.”
“Ina Ameenatu take kace min tana bandaki?” Ta tambaya ba tare da ta amsa gaisuwar ba. Ya rausayar da kai yace, “Amma taje asibiti ne.” Amma tace, “dah kace min tana bandaki, yanzu meye gaskiyar zancen a cikin abinda kace? Band’aki ko asibiti?.”
Humaira tace, “Amma Baba Isihu fa yace min tunda ta fita jiya da safe bata dawo ba har yanzu, yace min shima Yaya Yusuf din da safiyar nan ya tambaye shi inda take.” Yusuf ji yayi kamar ya kifa mata mari amma babu damar yin hakan sai harara kawai ya daure yaji Amma tace, “Ina taje Yusuf? Ina taje ta kwana kai kana gidan ka kwana a ciki baka san bata nan ba?.” Ya shafa kai yace, “Amma dana dawo na d’auka tana gidan sai bacci ya d’auke ni shi…….” A tsawace Amma ta dakatar dashi tace, “Rufe min baki ko na tsinke ka da mari.”
Ya saukar da kai k’asa yana jin wani iri wai Amma ce take cewa zata mare shi yace, “Kiyi hakuri.” Kamar hak’urin take jira ya bata sai ta sake fusata tace, “Me yake damun ka ne haka?, dan zaka yi aure ita baka da damu da lamarin ta ba kenan ko?. Yarinya kuna gida d’aya matar ka ace bata kwana a gida ba Baka sani ba sai gadi kake tambaya dan tsabar lalacew da tonawa kai asiri?. Ace mai gadi ne zai fad’a maka matar ka bata kwana a gidan ba Yusuf? Kai a wajan kaa wannan siyawa kai mutunci ne?. Ko mai aikin matar ka in da hali na gari in bata nan ai ya kamata ka sani balle kuma matar ka.”
Shiru yayi bai ce komai ba kafin ta sake cewa, “Matar ka ta aure bata kwana a gida ba dan rashin kula da rashin mutunci ace baka sani ba har safiya? Na Kira kuma kayi min karya kace tana d’aki ka sake min wata k’aryar kace min ta tafi asibiti, yanzu tana Ina?.” Ya kalli Amma yace, “Wallahi ban sani ba, bata tab’a irin haka ba tunda muke, na Kira ta bana samu.” Amma taja tsaki ta d’auki wayar ta ta kira Ameenatu cikin ikon Allah aka samu wayar ta shiga ta d’auka da sallama tace, “Amma barka da Rana.” Sai da yayi Ajiyar zuciya jin maganar ta da alama lafiya take.
Amma tace, “Barka daughter, ya takwara?.”
“Alhamdulillah Amma.”
“Kina ina ne na aika gidan akace min bakya nan?.” Daga can ‘bangaren Ameena tace, “Ina Bauchi Amma.” Kallon Yusuf tayi da yake kallon Amma din da wayar a speaker aka saka ta tace, “Bauchi kika tafi babu sallama Daughter?.”
Ameenatu tace, “Naso na sanar dake wallahi Amma sha’afa nayi na d’auka kuma ya fad’a miki.” Amma ta kalle shi tace, “Bai fad’a min ba Ameena, amma ke kika ja motar har bauchi?.” Ameenatu tace, “Eh Amma, ai ba wahala kawai dai na gaji ne amma a hankali nayi driving din.”
“Duk da haka kinyi ganganci tafiyar tafi k’arfin ki, har yaushe kika iya motar ma da zaki yi tafiya irin wannan?.”
“Kiyi hak’uri baza’a sake ba in sha Allah.”
“Ya dai kamata, in kin tashi dawowa zan turo da driver ya dawo dake. Ki gaishe da mutanen bauchin.”
“To Amma zasu ji in sha Allah, a gishe da Humairah.”
“Zata ji” ta fad’a tana yanke wayar tare da bin sa da kallo.
Kafin Amma tayi magana yace, “Wallahi Amma ta fad’a min min zata je Bauchi amma ban d’auka jiya zata tafi ba, kuma ban San ita kadai zata tafi ba wallahi da bazan barta ba.” Amma da take kallon sa tace, “To kai rantsuwar ka Abar yadda ce? K’arya kake Yusuf duk abinda zaka ce, baka san zata je Bauchi ba itama ta fad’ane dan kawai ta kare ka kamar yadda ta saba amma baka sani ba, ka fad’a min gaskiya wanne irin bacin ran ka k’unsa mata da ya saka ta tafi gidan yayar ta?.”
Yace, “Ba musu nake miki ba Amma, amma wallahi nasan da zuwa bauchi ta fad’a min kuma ni babu abinda nayi mata haka kawai ta……” kallon da Amma take masa ya saka shi kasa ‘karasawa tace, “cigaba mana Yusuf, ni nasan ba kowa ne yake iya kallona yayi min k’arya ba.”
Yusuf yayi shiru ta sake cewa, “Saboda zaka yi aure ba ta ita kake yi ba; baka san ma ta d’auki mota ta tafi Bauchi ba har aka kwana aka tashi kuma a gidan kake kwana amma baka duba ta ba balle kasan a inda take. Saboda bata da gata bata da uwa da uba a duniya balle su shiga lamarin ta” ya nuna shi da yatsa tace, “Kaga in baka yi wasa ba hakkin marainiyar nan da kake rainawa ba wallahi sai ya kai ka wuta, alqawarin da ka d’aukarwa mahaifinta a lokacin da ya rik’e hannun ka yana gargarar mutuwa yace ka kula masa da y’ar sa Ameena ka kasa cikawa, Ina so ka tuna wannan alqawarin da ka d’auka ka kasa saukewa ko shi sai ya bibiye ka balle kuma ya hakkın marainiya.”
Tayi shiru tana kallon sa kansa a ‘kasa ta kuma cewa, “ka daina ganin kamar babu abinda zai same ka fa ni na tabbatar sai kayi dana sani Yusuf, ko babu raina zaka tuna na fad’a maka zaka yi dana sani akan duk abinda kake aikatawa a yanzu. Kuma yarinyar da ka ke rawar k’afa akan zaka auro ta ba baki nake maka ba amma baza kaji dad’in zama da ita ba, ni na fad’a maka zaka kuma maimaita min wataran in akwai tsahon raina, kar ka d’auka kuma baki nayi maka akan auren kawai haka lamarin yake ne zaka kuma tabbatar da abinda nake fad’a gaskiya” ta girgiza kai tace, “Abu ne a bayyane na abinda kayi mata sai itama tayi maka:”
Yusuf ya rausayar da kai yace, “Amma ke shaida ce Ina son Ameenatu tun ba yau ba, son da nake mata ne ya saka na aure ta babu wani abinda nake mata Wanda zai cutar da ita.” Amma tace, “Da gaske? Shikenan to zamu gani ai Yusuf kai da ita waye yake cutar wani, akwai lokacin da hakan zai bayyana ina tabbatar maka da hakan, tashi ka bani waje.”
Yusuf ya mik’e a kan guiwar sa yace, “Dan Allah Amma Kiyi hak’uri na amsa nayi kuskure amma bazan sake ba in sha Allah, zanje har bauchin na dawo da ita amma wannan bakin da kika yi min a kan aurena ki janye shi kar ya tabbata Amma.” Tayi murmushi tace, “Ba baki nayi maka ba Yusuf, abu ne a rubuce a kan dutse.”
“Kiyi hak’uri!”.
“Baka yi min laifi ba, tashi kaje Allah ya bamu alkhairi.” Zai kuma magana tace, “Kaje Yusuf.” Babu yadda ya iya haka ya mik’e ya fita jikin sa a sanyaye matuk’a.
Da kallo Amma ta bishi tayi murmushi har ya b’ace tace, “Ina tausyawa ranar da Yusuf zaiyi dana sani akan abinda yake yiwa yarinyar nan, tsoro na kar lokacin yazo ita kuma a wannan lokacin tayi masa nisan da bazai sake samun ta ba.” Humayrah tayi shiru zuciyar ta cike da tausayin Aunty Ameena.
Yusuf ransa a b’ace ya kai kansa gida yana shiga gidan ya d’auki waya ya kira ta yayi sa’a ta shiga shima ta d’auka kafin tayi magana yace, “Waye ya baki izinin fita daga gidan nan har ki tafi bauchi?.” Ameena tace, “Nice na bawa kaina izini.”