Sashe 20
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana shiga d’akin taji an sake bud’e ‘kofa da sauri ta kalli wajan dan Amira da Zaytun basa nan sun je gidan Yaya Sumayya, ganin Yusuf ya saka ta kallon wajan sosai ta tabbatar shine ko kuwa dai idanun tane suke ganin sa, ita yake kallo shima ganin kamar an canja ta tayi masa fresh a ido sosai ya kawar da abinda yazo ransa yace, “Babu Sannu da zuwa?.” Sai tayi dariya kadan tace, “Sannu da zuwa.” Yayi murmushi yace, “Kizo kuzo ku gaisa da Asiya tana falo.” Kai kawai ta d’aga ya juya ya fita Ita kuma ta biyo bayan sa a ranta tana fad’in sai yau aka ga damar kawo ta wajena kenan.
A falon ta da ta bari ta ganta a zaune ya d’or k’afa kan d’aya tana kad’awa ganin fıtowar ta sai da gaban Asiya ya fad’i a zuciyar ya tace, _tabdjim, taya zan bar wannan matar haka kawai ai da wuri zata kora ni. Na bar wannan ai sai ta kora ni_ a zahiri kuma sai tayi murmushi tace, “Barka da fitowa Mummyn Zaytun.” Ameena tayi murmushi tace, “ke za’a yiwa barka saboda Kun sha hanya.”
Asiya cikin iyayi tace, “An sha hanya kam, ga gajiya sai da nayi bacci na tashi naji dad’i. A can din ma kullum a gajiye ake ba samun bacci muke ba Ameena tayi murmushi tace, “Allah Sarki, ai kin san zaman Saudia da banbanci da zama a Nigeria, ba sosai ake samun bacci ba daman. Allah ya anyi umrah a sa’a.” Ta amsa da amin kafin tace, “bama wai rashin bacci na garin ba, kin san abin ka da amarya, Ai mun gode na cewa my love ma yayi miki godiya ka fad’a mata?” Ta fad’a tana kallon sa.
“Me kenan?” Ya fad’a yana zama a kujera mai mutum d’aya tace, “da ta bamu lokaci mana, kai kanka kace fa…..” da Sauri ya katse ta yace, “Asiya ba abinda nazo yi nan ba kenan, na kawo ki nan dan ki ganta itama ta ganki bana son surutun banza” ya fad’a yana hararar ta. Asiya tayi dariya tace, “Sai kace wata bak’uwa sai ka kawo ni? Ai in naga dama sai nace yau a nan zan kwana ko Mummyn Zaytun?.”
Ameena ta d’aga kai alamun eh kafin ya kalli Ameena yace, “Ina Zaytun ne?.”
“Sun fita da Amira yanzu zasu dawo.” Baice komai ba Asiya tace, “My love ka nuna min gidan nan na gani, Ina son hawa can saman gidan naje?.” Ya kalle ta yace, “Bamu yi maganar da ta tara mu ba ai ko?.”
“To ai ba bak’i bane nida ita kawai abinda ka yanke yayi. Ni bara naje” ta fad’a tana tashi kawai ta fita.
Ameena ta bita da kallon mamaki tayi dariya kafin ta dawo da kallon ta ga wani wajan daban, ya jima a haka yana kallon ta ya kasa magana shi kasan bai San me zaice mata ba kafin ya daure yace, “Kina Lafiya?.” wani iri taji a zuciyar ta ba tare da ya d’ago ba ta daga kai alamun eh kafin tace, “Ai ka gani a zahiri Lafiya nake.” yace, “Amma kin rame sosai, Kinyi haske kuma, ko kin yi rashin lafiya a kwanakin da bana nan?.” Nan ma girgiza kai tayi alamun a’a ya sake cewa, “To ramar ta meye?.” Ta kalle shi tace, “ta jin dad’i ce.”
“Jin dad’i na saka rama ne daman?.”
Ta wara ido tace, “au baka sani ba? Kaima kasan ai in ba jin dadin zaman gidan nan ba ai babu abinda zai saka ni rama.”
Jin maganar ta kamar da biyu take yi sai yace, “kiyi hak’uri wayata ce ta fad’i ban samu na kira ki ba.” Murmushi tayi ta kalle shi ido cikin ido tace, “Allah sarki, da wayar aro nake ganin story a Ig kenan?.”
Shiru yayi yana kallon ta ya kasa bata amsa sai yaga ta sake yin murmushi tace, “na fahimta ara kayi kar ka damu.” Shi dai kallon ta yake da yanayin ta da kalaman ta gabadaya sun canja masa kafin yace, “Na yanke hukuncin kwanaki biyu ga ko waccen ku, hakan ya miki?.” Tayi k’aramar dariya tace, “Abinda ka yanke kai da Asiya ai shine daidai, ina ruwan Ameenatu baiwar Allah.” Kallon ta yake yi ganin tana yi masa komai da biyu zaiyi magana kenan Asiya ta dawo falon ta zauna tace, “Naga ko Ina yayi kyau, I’m sorry Ameena na shiga d’akin My love na sama babu izinin ki.” Ameena tace, “kema mijin kine ai.”
Shiru ne ya biyo baya baice komai ba itama haka kafin Asiya tace, “My love muje ko?.” Ya kalli Ameena yace, “Ina zuwa” ya fad’a yana fita shida ita bata ma sake kallon inda suka bi ba ta tashi ta tashi ta bar falon.
Suna komawa b’angaren Asiya ya kalle yace, “Kiyi mana girki yunwa nake ji ban ci komai ba.” Ta bishi da kallon sama da k’asa, “Yau nasan b’angaren Ameena zaka tafi a can zaka kwana kuma kace nayi maka abinci? Kenan ita da miji nida girki? Kaima kasan bazai yu ba” Ta fad’a tana kallon sa shima kuma ita yake kallo cike da mamakin kalaman ta.
#Mai daki
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema
Book2
013
Cak ya tsaya yana kallon ta da mamaki da tsoro ganin ido cikin ido take fad’a masa ko kunya da nauyi bata ji ba bazata iya yin abinda ya sakata ba yace, “Ni kike cewa baza ki yi ba?.” Sai tayi sanyi tace, “Kayi hak’uri ba nufina kenan ba.” Kai ya girgiza kafin yaja baya yace, “Kafin na dawo ki tabbatar kin yi abinda nace, in ba haka ba ranki ne zai b’aci fiye da tunanin ki” yana fad’a ya fita ita kuma kamar za tayi kuka dan Allah ya sani babu ta yadda zatayi abinci yaci kuma yaje ya kwana da wata ba bazata iya ba.
Maimakon tayi abinda yace kawai sai ta d’auki waya ta shiga kitchen d’in ta kira lambar Umma, Umma ta d’auka da sallama ba tare da ta amsa ba tace, “Umma daga dawowar mu yau sati biyu da auren mu har ya fara min fad’a yana saka ni aiki, taya za’a ce matar sa yau zai kwana wajan ta yace ni zanyi abinci? Nidai gaskiya bazan iya ba.” Umma taja tsaki ta kashe wayar Asiya ta tsaya tana kallon wayar cikin rashin sanin abin yi.
K’arar shigowar sak’o taji ta duba taga da lambar Umman aka turo tayi saurin bud’ewa taga abinda aka rubuta; _Baki da hankali Asiya gabad’aya ban San me yake damun ki ba, a cikin gidan ki ko wanne lokaci mijin ki zai iya shigowa kike wannan maganar sai ya jiki?. Dan yace ki yi abinci ki dafa mana ai a haka zaki samu ki sake kama shi, kar ki manta Saudia kawai kika je ko mota bai siya miki ba, tun a yanzu zaki fara nuna masa halin rashin tarbiyayar ta ki sai ya fara gajiya dake ya fasa yi miki abinda yayi niya?, ki nutsu Malama in zaki makircin naki kar ki bari ya gane cewa bakya son matar sa ne, ki yi abu a nutse ki yi aiki da ilimi yadda koda kece da laifi ita zai zarga bake ba. Anjima Momi zata zo taya ki kwana in ta tashi tawo wa ki tabbatar an samu wata dubu d’arin ko sama da haka._
Karanta abinda tace sai tayi ajiyar zuciya tabbas fa kuma haka ne abinda Umma tace gaskiya ne, nan da nan ta saki rai ta fara dafa lafıyayyen abinci ba tare da wata damuwar komai ba. Ba jimawa ta kammala abinta ta barshi a kitchen din ta hau sama.
Shi kuwa Yusuf gidan Ameena ya shiga ya hau zuwa d’akin sa kai tsaye wata k’aramar cover ya bud’e ya d’auki wata jaka ya sauka ya shiga mota ya tafi zuwa gida. Kasancewar Anyi sallah ya tarar da mahaifin sa yana cin abinci ya shiga da jakar a hannun sa ya ajjiye ya gaida iyayen nasa duk suka amsa har Ammah da baiyi tunanin hakan ba.
Abbah ya mik’awa jakar yace, “Abbah ga sak’on da kace na tawo dashi.” Karb’a yayi yace, “Ashe d’azu ka dawo sati d’ayan kenan ko Yusuf?.” Yusuf ya sauke kai k’asa zaiyi magana Abbah yace, “Komai zaka fad’a k’arya kake Yusuf, daman abinda kayi niya kenan kuma shi kayi, ka kyauta ka nuna mana bamu isa ba ka nuna mana matar ka ba komai bace a wajan ka. Abinda nake so ka sani duk abinda ka ke yi ina sane da kai kar kaga bana magana mahaifiyar kace take magana ka d’auka ai ban sani ba ko ban damu ba, Ina sane wallahi tara ka nake duk ranar da na fusata daga ranar yarinyar ta gama zama dakai har abada. Nima uba ne bazan so a yiwa y’ata abinda kake yi mata ba. Ka bar yarinya ba kula babu abinda ya dame ka, rashin ka in ya jawo ta fad’a neman mata ko neman mazan kazo kace ai baza ka iya cigaba da zama da ita ba ga halayyar ta, to tun ba’a je nan ba zan yiwa tufkar hanci tunda kayi amarya baza ka iya cigaba da kula da ita ba sai ta matsa ta baka waje.”
Yusuf kansa yana ‘kasa har Abbah ya gama magana bai ce komai ba sai da yaji yaje k’arshe ya d’ago zai yi magana ya dakatar dashi yace, “Duk wata k’arya da ka shirya fad’a min bana son ji, abinda na fad’a shi zanyi kawai.” Ya kalli Ammah da bata da biyar magana ganin sun had’a ido sai tace, “ai amaryar ma yar gwal ce ko kawo amare da ake yi gidsn iyayen miji bisa al’ada ita ba’a kawo ta ba, bazata iya zuwa ta gaishe da iyayen ka ba kenan?.” Ido ya runtse Allah ya sani yaso hakan tare yaso suzo amma ta b’ata masa rai d’in da tayi ne ya saka ya manta shaf bai neme ta ba sai yace, “Gobe zamu zo in sha Allah, kanta ne yake ciwo shiyasa.”