← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 42

Sashe 14

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar laraba da safe suna zaune ita da Amira a falo Amira tana gyarawa Zaytun farce ita kuma tana kallo suna hira sama-sama in abin maganar yazo suyi in bai zo ba kuma suyi shiru sai sautin tv kawai da yake tashi. K’wankwasa k’ofa ake yi hakan ya saka Amira ta ajjiye abinda take yi ta tashi ta bud’e, mata ta gani su biyar a tsaye ta bisu da kallo dan bata san su ba amma tace, “Sannun ku da zuwa, ku shiga” ta fad’a tana basu hanya suka shiga suna ta kallon falon ana kallon juna. Zama sukayi Ameena da take kallon su ta gyara zama tace, “Barkan ku da zuwa.”

D’aya daga cikin su ta amsa da fadin, “Yauwa barka, ya gıdan?.” Ameena da fara’a tace, “Alhamdulillah, Amira zo ki kawo musu ruwa.” Amira ta tashi ta kawo ruwa harda lemo wacce tayi magana d’azu tace, “Dangin amarya ne Asiya, Mun zo zamu yi kafi a gidan ne muka shigo a gaisa.” Sai da gaban Ameena ya fad’i amma bata nuna ba tayi murmushi tace, “Allah sarki, naji dad’in hakan na gode sosai da kuka shigo.”

Mik’ewa sukayi suka mata sallama suka fita tare da jan k’ofar kamar yadda suka ganta. Ameena ta jingina da kujera tare da rufe idanu ta kawai bata ce komai ba kafin ta mik’e ta hau sama.

Bata san lokacin da suka tafi ba tunda ta hau saman bata sakko ba sai bayan la’asar shima girki ne ya sakko da ita, kitchen din ta shiga ita da Amira suna yi suna hira sama-sama har suka kammala ta kwaso aka ajjiye akan dining table lokacin ana kiran magriba ta koma sama da niyar yin sallah.

Bayan ta idar da sallah ta dawo k’asan ta zauna ta fara cin abincin Amira da Zaytun suna sama basu sakko ba, tana cikin cin abincin yayi sallama ya shigo ta d’ago ta amsa tana kallon sa, tunda taga yanayin fuskar tasa gaban ta sai da ya fad’i a zuciyar ta tace, _To yau na shiga uku dmaan an jima ba’a yi min fad’a ba._ a bayyane sai ta amsa sallamar tare da fad’in, “Sannu da zuwa.” Ganin ita kad’ai ce a zaune ya saka ya k’araso yana zuwa kusa da ita ya k’are mata kallo yace, “Meyasa duk abinda za’a tafi dani a baki ana zagina shi kike son yi Ameena?.”

Fuskar ta ta nuna alamun me kuma nayi ta kalle shi bata amsa ba yace, “Duk wani abu da zaki aikata dan a zage ni shine fatan ki, burin ki kiga raina ya b’aci Amma tayi min fad’a ko kuma ta dole sai anga gazawa ta ko?.” Nan ma tayi shiru bata amsa ba sai kuwa ta fusata shi ya daki table d’in da take kai yace, “Ina magana da yake kin mayar dani d’an iska kin yi min banza? Sa’an kine ni?.”

Sai a sannan tace, “Ban san akan abinda kake magana ba shiyasa nayi shiru.” Runtse ido yayi ransa na mugun tafasa zuciya na fad’a masa kawai ya mare ta dan rainin nata yayi yawa dakyar ya sarrafa kansa ya hana kansa narin yace, “B’akin da suka zo d’azu uban waye ya hana ki yi musu abinci ki basu? Ko abincin naki ne da zaki ajjiye a store baza ki dafa ki basu ba, tambayar ki nake da kud’in ki na siya!?.”

Ameena ta dafe kanta da hannayen ta duka biyun kafin ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ya sake cewa, “Da suka zo ba ko kallon kirki basu samu daga wajan ki ba kika wulak’anta su ke a lallai ga matar gida. Wallahi in baki shiga hankalin ki ba zan d’auki mataki a akan ki wanda baki tab’a kawowa a zuciyar ki ba, ki fad’a min meye ya hana ki basu abinci?.”

Mik’ewa tsaye tayi ta kalle shi tace, “tsakani da Allah nasan zasu zo? Baka fad’a min ba ban san da zuwan su ba taya……” dakatar da ita yayi yace, “Da ban fad’a ba da suka zo meyasa a lokacin baza’a girka a basu ba? Akwai abinda babu a gidan ne?.”
“Ka fad’a min ana girkin ne? Akwai Wanda ya fad’a min ana yin abinci balle na sani nayi?.”

Banza kallo yayi mata na sama da k’asa yace, “Ohh baki san ma anayi ba kenan ko?.”
“Inda na sani taya zan tambaye ka, kai kanka kasan dana sani bazan kyale su haka ba dan rowa ba halayya ta bace ban bud’e ido da ita ba.”
“Ke rashin hankalin naki har ya kai sai an fad’a miki sannan zaki yi abu? Da kika ga sun zo kiyi mana lallai sai an fad’a miki?.”

Motsin Amira taji kamar zata sakko hakan ya saka ta d’aukar plate din abincin tayi niyar barin wajan bata so Amira tazo ta tarar dasu a haka shiyasa zata bar wajan, hakan da tayi ba ‘karamin sake harzuk’a shi yayi ba; bai San lokacin da ya kwace plate d’in ya cillar a kasa ba ya finciko hannun ta yace, “Ina miki magana zaki tafi ga mahaukaci ko?.” Kallon gefen ta tayi taga Amira da Zaytun a hannun ta a tsaye ta kalle shi tace, “Kayi hak’uri” tana fad’ar hakan ta bar wajan ta hau sama ba tare da ta kwashe abin da ya zubar ba.

Amira ce ta sakko wajan suka had’a ido da Amira ta d’auke kai haka kawai taji baza ta iya yi masa barka da zuwa ba idanun ta ya fara zubar da hawaye ta ajjiye Zaytun akan kujera ta d’auko tsintsiya tana share abinda aka zubar. Kwafa yayi ya fita Amira ta bishi da kallo ta gama ta d’auki Zaytun suka koma saman gabad’aya bazata iya cin abincin ba ranta ya b’aci.

Ameena Tunda ta hau saman take kuka sosai babu mai rarrshin ta, zuciyar ta tafasa take mata fiye da ko yaushe haka take ji. Babu abinda yake d’aga mata hankali kamar had’a ta fad’a da shi da gidan su amaryar suke yi, tun kafin ta shigo ana yi mata irin wannan makircin Ina ga amaryar ta shigo gidan?.

Sallar Isha ce ta saka ta tashi tayi sallah tana yi tana jan numfashi saboda kuka tana idarwa ta zauna tana cigaba da zubar da hawaye. Bud’e k’ofa akayi Amira ta shigo jiki a sanyaye ita kanta tasha kuka ta zauna kusa da ita tace, “Aunty Ameena Kiyi hak’uri ki daina kuka, komai lokaci ne kuma komai zai wuce kamar bai faru ba.” Kallon Amira tayi ganin yadda fuskar ta tayi alamun tayi kuka tace, “Kar ki damu Amira ki daina kuka kije kuci abinci, in Daddyn Zaytun din bai ci ba ki kai baya su Baba Habi su cinye kar ya lalace.”

Amira tace, “Aunty bazan iya cin komai ba bana jin yunwa” ta fad’a tana niyar yin kuka Ameena tace, “Tashi kije kici a haka kar ki kwanta da Yunwa.” badan taso ba haka ta tashi ta rik’e hannun Zaytun suka fita daga d’akin ta lumshe ido tana kallon sama. Bud’e k’ofar ta saka ji anyi an shigo tace, “Amira kije kici abinci nace ko? Kar ki kwanta haka baki ci komai ba.” shiru taji ba’a amsa ba hakan ya saka ta bud’e ido ta kalli inda take jin motsin ta ganshi a zaune yana kallon ta.

Mayar da ido tayi ta kulle ko motsi batayi ba hakan ya saka shi cewa, “Raina ne ya b’aci d’azu da naji baki basu abinci ba, ko babu komai bak’i na ne ya dalilina suka zo nan bai kamata ace sun zo har gıdana sun tafi basu ci komai ba. Komai ya wuce kiyi hak’uri” a tusashe yake maganar hakan ya saka ta sake bud’e ido ta kalle shi suka had’a ido ta seke mayar da Idon ta rufe ya sakko kusa da ita ya zauna ya rik’e hannun ta yace, “Ki bar fushi mana komai ya wuce.”

Kai ta girgiza tace, “ni ba fushi nake ba.”
“To indai haka ne ki saki ranki.” Bata ce komai ba har lokacin bata bud’e ido ba sannan bata saki ranta yace, “Indai da gaske ba fushi kike ba kizo muje dakina ki kwana a can. Kuma dan Allah gobe zasu dawo bakin a daure ko jellof ce a basu.” Sai a sannan ta bud’e ido ta kalle shi sosai sai tayi murmushi na takaici daman tasan bada hakurin nan da yazo da biyu yazo ko tace da uku ma haka kawai bazai bata hak’uri dan yayi mata fad’a ba, yake dukan ta ma bai bata hakuri ba balle wani fad’a.

“Yanzu ba wannan ba ki tashi muje saman” ya fad’a tana tashi tare da jan hannun ta. Zame hannun tayi daga cikin nasa dan taga alamun yana raina mata hankali ko yaushe yazo da niyar ya bata hak’uri sai yace wai tazo suje sama, Kenan ya mayar da ita abinda yake nufi ne zai saka ta daina fushi, tace, “basai naje saman ba nafi son kwanciya a nan.” Ya sake dawowa ya tsuguna gaban ta yace, “ni kuma a can nake so ki kwana, ki taso muje saman kar y’ay’an ki su dawo.” Ta kalle shi tace, “kayi hak’uri bazan iya tashi ba bana Jin dad’i.”
“Zan iya d’aukar ki ai ba wani nauyi ne dake ba” ya fad’a yana niyar d’aukar nata.

Da sauri tace, “Dan Allah Daddyn Zaytun ka kyale ni bacci nake ji kaina ciwo yake min, Dan Allah kaje ka kwanta basai naje ba.” Ya kalle ta yace, “Shikenan, kin sha magani?.” Kallon sa tayi ido cikin ido bata amsa ba jin wai yana tambayar ta wai tasha magani shine ya bata mamaki, sai ya d’an sosa kai yace, “Shikenan ki kwanta, da wuri zan fita gobe koda baza ki iya girkin ba please ki saka Amira tayi ko su Baba Habi.” Kai ta d’aga kawai dan bata son ma jin maganar sa ya juya ya fita ta bishi da kallon mamaki.
Chapter 14 · 0% Book details