← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 42

Sashe 5

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon ta yake yi har ta kai karshe yace, "To meye abin damuwa a nan? Waye ya wuce tsautsayi? Ai kowa hakan zai iya faruwa dashi.”
"To ni haka za'a yi bikina babu gyaran jiki?" Ta fad'a tana kallon sa tare da turo baki gaba. Murmushi yayi yana kallon ta yace, "ni za'a yiwa gyaran fa, ai dole a biya a yi miki dan ko anyi ni zai yiwa amfani, akan me bazan biya ba?” Ya fad’a yana murmushi tare da kashe mata ido d’aya. Dariya tayi ta kulle fuska yayi dariya kadan yace, “Kar ki damu zan tura miki kudin sai ki bata."

Murmushi tayi tace, Thanks you my love." Dariya yayi kad’an yace, "Ni kin tayar min da hankali ko gida ban je nayo nan. Yadda naji maganar ki na dauk’a wani abun ne ya faru ashe kan five hundred thousand naira kike d’aga hankalin ki.” ya fad'a yana kallon wayar sa da take ta vibration. Sunan Ameena ya gani hakan ya saka ya danna power wayar ya kalli Asiya yace, "Zan koma store ana nema na."

"Ko dai Auntyna tana waya?." Kallon ta yayi kamar zai ce wani abun sai ya fasa ya canja maganar yace, "international Passport din ki ya fito yana hannuna ana gama biki sai mu wuce kiyi umrah a matsayin…” sai yayi shiru yace, “ki canka.” Farin ciki ya mamaye zuciyar Asiya ji take yi kamar tayi tsalle sabida murna amma sai tace, "ai ban san matsayin meye ba, ka fad’a min.” Ya girgiza kai yace, “sai lokacin yayi zan fad’a miki.” Tayi murmushi tace, “Allah ya kaimu." Shima yayi murmushi yace, "Amin my love.” Sai kuma yace, “Ko kuma let me tell you dan ki kasance a cikin shiri” ya fad’a yana matsowa kusa da ita ya fad’a mata suka hada ido yayi daga gira sai ta kulle ido ta fita ta shiga gıda shi kuma ya tafi yana murmushi.

A guje ta shiga gıda tana fadin, "Umma ya bani dubu dari biyar din" ta fad'a tana ihu tana tsalle a falo. Umma Sakina tayi murmushi tace, "Ke ki kalle ni kawai, duk wani abun da ya kamata na Riga na aikata miki shi tun kafin yanzu. Bayan wannan sai me?."
"Umma Sakina yace min international passport dina da muka je muka yi yana hannun sa ana daura aure zamu wuce umrah a matsayin tukwuicin first” ta fad’a tana shiga d’aki a guje cikin farin ciki Mara misaltuwa.

Umma Sakina da Umma suka tafa suna dariya Umma tace, "Sakina ke k’arshe ce wallahi." Umma Sakina tayi dariya tace, "A dai shiga gidan, wallahi sai Uwar gidan ta gwammace bata aure shi ba, baza mu fitar da ita ba amma sai taji Inama ya sake ta koma gidan su da zama."
"Daman Umma Sakina na tsane ta wallahi, ta fini kyau kuma da alama shima yana sonta har yanzu, ni dama a fitar da ita daga gidan da nafi jin dad’i” Asiya ta fad'a tana fitowa daga d’aki.
"Barni da ita, kedai ki cigaba da shiri." Cikin farin ciki ta wuce zuwa kitchen.

           Ameena kuwa hankalin ta a tashe yake jikin Zaytun yayi zafi sosai gashi ita kanta bata da Lafiya baza ta iya tuk'a mota ba balle ta kaita asibiti, hankalin ta ya tashi ta bata magani amma zazzab’in bai sauka ba, ya Kira shi bai d’auka ba bai kuma kira ta ba gabad’aya ta rasa abinda zatayi. Lokacin da ya shigo ta kwantar da Zaytun d’in akan kujera taje ta dauko ruwa da towel ta goge mata jikin ta ya shigo ya samu tana kuka.

Da sauri ya d’auke ta jin yadda jikin ta yayi zafi sosai hankalin sa ya tashi ya tab’a wuyan ta yace, “Amma ta me yake damun ki?.” A lokacin Ameena ta fito da ruwa da towel a hannun ta tana fitowa bai jira abinda zata ce ba ya fara yi mata fad’a yana cewa, "Dan rashin hankali yarinya bata da lafiya baza ki kaita asibiti ba kin zauna da ita a gida sai ta mutu? Meyasa kike yin haka ne wai?, bak’in kishin naki har Akan y’arki?." Cak ta tsaya tana kallon sa yanayin ta duk ya canja murya a sanyaye tace, "Sau nawa Ina kiran ka baka amsawa?."

"Baza Kiyi min text ki fad’a min ba? Meye amfanin motar ki da baza ki kaita da kanki ba?, meye amfanin su Sani da baza ki kira su su kai ki ba?. Na lura rashin mutuncin har Zaytun ya shafa to na rantse da Allah wani abun ya same ta sai ranki ya baci" tana fad'a ya fita da Zaytun a hannun sa ta nemi waje ta zauna akan tiles ta jingina da bango.

Bata san adadin lokacin da ta d’auka a wajan ba kiran sallar magriba ne ya saka ta ta tashi sai kuma ta tuna ba sallar ma zatayi ba ta koma kan kujera ta zauna tayi tagumi tana kallon wani wajan daban. Zazzab’i take ji sosai ga kanta yana yin shiru amma hakan bai hana ta tunani ba. Tausar zuciyar ta ta fara yi a hankali sai ta fara karanta suratul waqi'a a zuciyar ta a haka har taje k’arshe zuciyar ta nayi mata sanyi sosai cikin mintina kad’an.

Shigowar sa ta gani da Zaytun a kafad’ar sa tayi bacci hannun sa da ledar magani bai ko kalle ba ya wuce sama ya kwantar da ita akan gadon sa ya shiga band’aki.

Bata yi k’ok’adin bin sa ba tana zaune sai da ta gaji da zaman dan kanta sannan ta tashi ta hau saman itama tayi wanka da ruwan zafi ta saka kaya marasa nauyi amma masu kauri ta kwanta tayi lamoo akan gdo gabad’aya zaman gidan ya ishe ta Ina ma zai barta taje Bauchi wajan Yaya da zata fi kowa farin ciki. Tunawa da Yaya Adam sai ta mik’e zaune ta jawo wayar ta ta kira lambar sa amma bata shiga ta ajjiye wayar ta koma ta kwanta, Tabbas da Yaya Adam yana nan da gatan ta yana kusa da ita,

Bata san bacci ya kwashe ta ba sai da alarm d’in wayar ta na k’arfe ukun dare ya buga ta mik’e zaune dakyar ta kalli Agogo taga karfe uku ta tashi ta shiga band’aki. Alwala tayi tazo ta zauna kan sallaya ta kalli gabas tana karatun alkur'ani a bayyane a hankali ba tare da ta rike alqur’ani ba. Ta jima a haka kafin ta fara lazimi tana addu'a a zuciyar ta tana fad’awa Allah damuwar ta.

Har bayan asuba tana zaune tayi azhkar ta tashi kenan taji motsin sa ta juya suka had’a ido ya mik'a mata Zaytun bai ce komai ba ta karb’e ta tace, "Ina kwana."
"Lafiya lau" ya amsa yana fita daga d'akin ta tab'a jikin ta taji babu zafi, ajjiye ta tayi ta rike hannun ta zuwa band’aki tayi mata wanka tana yi mata wanka suna dariya tana yi mata surutun da ta saba yi har suka fito.

Shirya ta tayi ta shayar da ita tace, "Yaye ki ma zanyi wallahi na gaji Zaytun, da k’afar ki kina yawo ko ina ga d’an banzan baki a wajan ki kamar wacce ta shekara uku, kowa kin sani komai kin sani hutawa nima zanyi wallahi.” Zaytun din sai tayi dariya kammanin ta da baban ta ya bayyana sosai a akan fuskar ta itama Ameena sai tayi taja kumatun ta ta fara yi musu,

Bata koma bacci ba suka sauka tare Zaytun tana ta kiran Mummy da Daddy ta shiga kitchen ta d’ora tea ta dafa indomie ta gama ta juye a bowl ta had’a tea suka fito falo tana ci tana bawa Zaytun din ma tana ci tana bata labari ita kuwa mamakin surutun Zaytun take yi. Tun daga sama yake kallon su yadda suke zaune suna dariya sai ya samu kansa da yin murmushi shima sun burge shi sosai musamman ita Ameenatou da tayi kyau cikin shigar da take so doguwar riga yar kanti mara nauyi, ta gyarawa Zaytun gashin kanta yayi kyau sosai sai k’yalli yake yi tun daga nesa.

Yana k’arasowa ya ajjiye mata maganin yace, "Baki damu ki nemi maganin ta ba ko?" Yadda yayi maganar cikin sanyi a kuma tausasbe shine ya saka ta kalle shi tace, "Yanzu daman zan d’auko abinci taci." Kallon ta yake yi dan ta rame sosai yana so ya tambaya dalilin ramar amma wata zuciyar na hana shi yin hakan.

"Ina nawa abincin?." Ta d’ago ta kalle shi suka had’a ido sai ta mik’e yace, "Barshi Tunda baki yi dani ba." Tayi shiru ya matso kusa da fuskar ta yace, “Meyasa bakya yin abinci dani?.” Ta kalle shi ido cikin ido tace, “zan gyara.” Ya yamutsa fuska yace, “ya kamata.” Yayi hanyar fita tace, "Daddy!." Juyowa yayi y kalle ta da alamun tambaya a fuskar sa jin sunan da ta kira shi dashi bata bari ya samu damar magana ba tace, "Dan Allah Ina so zanje Bauchi gidan Yaya na kwana biyu a can.” Bai ce komai ba ya juya ya fita ta bishi da kallo har ya b’ace ta juyo ta cigaba da cin abincin ta.

            A gidan su Ibrahim shima ya ware sosai neman kud’in sa kawai yake ya manta da komai bai bar wani abu a zuciyar sa ba balle ya dame shi. Hankalin sa kwance yake yin komai in ba Amir ya gani bama mantawa yake da wata Fiddausi albarkacin Amir yake tunawa da ita. Da sallama ya shiga gidan su ya tarar kowa yana nan a cikin y’an uwan sa mata ana hira, tunda yaga anyi shiru da ya shiga yasan hirar Fiddausi ake yi ya murmusa yace, "Yau duka kuna gıda kenan?."

Yayar sa Hadiza tace, "Eh Muna gida, Muna mayar da zancen tsohuwar matar ka. Ashe har fita take ma baka sani ba, azo a d’auke ta a mota a fita da ita duk baka sani. Kai Allah na gode maka da ka raba mu da mugun iri tun kafin abun yayi nisa.” Murmushi yayi kawai yace, "Ni ba wannan ba, nazo muku da labari mai dadi Hajiya."
Chapter 5 · 0% Book details