Sashe 7
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ameenatu ta girgiza kai tace, "Kiyi hakuri lokacin zai zo na tabbata Umman ta fad’i haka ne kawai amma ba yi zatayi ba."
"Wallahi zata iya, Baba ne kawai yake rarrashi na Umma da ya kamata ta dinga rarrashina itace take hantara ta, wallahi gidan mu ya ishe ni Ameena na gaji, na fara tunanin had'a kayana na gudu."
"Kar Kiyi haka ki cigaba da hak’uri Allah yana sane dake fa."
"Yanzu Umma bata tunanin watakila bani da rabon auren a duniya jiran mutuwa nake yi? Meyasa Umma bata tunanin haka Kullum sai fad’a?. Ko d'an shaye-shaye ne yazo burin Umma kawai na amince na aure shi. Ameena nima fa Ina damuwa, kune kawaye na dukkan ku kuna da yara, Ina so nayi auren nima amma jiran lokaci nake yi amma umma bata ganin haka."
Ameenatu tace, "Ki kara hak’uri a jikina nake Jin lokacin auren ki ya kusa Rukayya, Ina ma ke Yusuf ya gano ya aura." Idanu Rukayya ta goge tace, "Na gaji Ameena wallahi na gaji, Bawai zaman gidan ne ya ishe ni ba kawai abinda ke yi min ne yake sakawa naji na tsani komai, Baba ya hanani aiki, ya hanani cigaba da karatu da Yanzu nayi nisa, Kullum Ina gida ba dole su gaji da ganina ba."
Ameenatu tace, "Wallahi Umma ba tsanar ki tayi ba Ruky, kamar yadda na fad’a miki so take kiyi aure ki tashi kema kiga naki yaran, na tabbata yadda take miki addu'a ke bakya yiwa kanki, tafi kowa shiga damuwa akan wannan abun tana yin haka ne sabida itama y'ar adam ce yau da gobe sai Allah bawai dan bata son ki ba. Uwa ce fa Rukayya, duk wata magana da ake yi a kan ki ta fiki jin zafin abun dole kiga ta damu. Kefa kina da mahaifiyar ma ni kuwa bani da wacce zata yi min addu'ar ma Rukayya."
Rukayya tace, "amma fad’a da abinda ake nuna min ba shine zai saka nayi aure ba ko?."
"Kedai ko cigaba da addu'a kawai kinji? Wallahi Allah in lokacin ki yayi babu bata lokaci sai kin tafi gidan mijin ki."
"Hakan Umma ta kasa ganewa ai."
"Ta sani fa Ruky, kawai tana yin haka sabida wani dalili amma ta sani Kiyi hakuri."
Numfashi ta sauke tace, "Shiyasa gidan yayi min zafi kawai na tawo wajan ki." Murmushi tayi tace, "Muyi addu'a kawai Allah yana sane damu." Rukayya ta kallo Ameenatu tace, "yaushe kika fara Shan maganin hawan jini?." Ameenatu ta kalle ta tace, "Ba'a fi wata d'aya ba, ke kad’ai kika sani ko Yayan Bauchi bata san Ina da hawan jini ba, dan Allah kar ki fad’awa kowa."
"Haba Ameena sirrin ki ai nawa ne ke kin sani, amma ki rage sakawa kanki damuwa, damuwar ke zata cutar ba shi ba.”
"A gaban ki dai akayi komai, wannan to ba wani abun bane ba dan baki ga komai ba Ruky."
"Ni wallahi sai naji tsoron auren ma na shigata."
Tayi murmushi tace, "Kiyi addu'a kawai. Akan wacce zai aura yake min wannan fad’an kawai dan naga ana kira number babu suna dan Allah basai nayi zaton shine yake kira ko yana neman wayar ba? Na d’auka wallahi kalmar dana fad’a bata fi uku ba amma sai gashi ya zamar min tashin hankali tunda gashii ana cewa na zage ta. In yarinyar nan ta shigo gidan nan Ina jin sai na bar gidan nan, tun kafin tazo ana haka Ina ga ta shigo?. Yanzu badan ke bace in a gaban masu aikina yayi min haka da banji kunya ba?. Da ya tozarta ni tozarck na har abada kuwa.”
Rukayya tace, "bata isa ba In sha Allah, ai Allah yana tare da mai gaskiya. Ke tazo ta samu baza ta fitar dake ba in sha Allah Ameena.” Ameena ta sauke numfashi tace, "baza ki gane ba Rukayy ki taya ni da addu'a kawai, kuma dan Allah ki rik’e min sirrin nan kar ki fad’awa kowa. Wallahi ban tab’a fad’awa kowa wannan maganar ba babu wanda yasan halin da nake ciki a gidan nan, kema dan kin riska ne kuma na amince dake shiyasa na iya fad’a miki. Ina neman wanda zan fad’awa abinda yake zuciyata dan na ji dad’i.” Rukayya tace, "In sha Allah ke kin san baki da damuwa, Allah ya kawo miki mafita Ameena. Fiddausi sabida hangen ki Keda Zakiyya ta kashe auren ta."
"Hmmm bata da hankali ne ai Rukayya, inda nice ita Wallahi babu abinda zai dame ni, saboda samun ina kula daga wajan mijina me ai tayar min da hankali? Koda yake ba duka aka zama d'aya ba watakila ita ta dace da samun mai kud’in. Allah ya had’a ki da miji na gari kawai Rukayya, ba mai kudi ba mai kula dake kawai, in mai kudin ne Allah ya had’a miki duka.”
Rukayya tace, "Amin ya Allah Ameena, addu’a ta kenan Allah ya bani na gari.” Ameena ta amsa da amin suka cigaba da bawa juna shawara ko wacce tana kwantarwa da yar uwar ta hankali dan dukkan suna cikin damuwa suke.
A Daren ranar Alhaji Bello ya kai Kansa wajan k’anin mahaifin Fiddausi Kawu Sa’idu yayi masa bayanin komai tare da sanar dashi baya so a d’auki lokaci da gaggawa yake so ayi auren ya sakar masa kud’i ya tafi.
Da daddare su Fiddausi suna zaune ana cin abinci Kawu ya shigo da sallama Mama ta amsa tana fad’in, "Yau kaine a gidan?." Ya zauna akan kujera yace, "Eh wallahi, ya gıda da yaran?." Mama tace, "Alhamdulillah, ya mutanen gidan?."
"Alhamdulillah." Ya kalli Fiddausi yace, "D’azu wani Alhaji Bello sagagi yazo ya same ni wai ya ganki yana son ki kuma ya samu labari akan komai daya faru dake yasan babu idda a akanki shiyasa yazo yanzu dan da wuri yake so ayi auren ku.”
Mama ta gyara zama tace, "Wanne Alhaji Bello din?." Kawu yace, "Wanda dai kika sani shi nake nufi, da alama kuma yana sonta sosai kamar ba sabuwar had’uwa bace. A Ina kuka had’u?." Fiddausi ta gyara zama tace, "A cikin satin da ya wuce ne ya ganni naje gidan Zakiyya, yana tayi min magana sai nak’i yi masa magana shine ya tambayi Zakiyya a kaina tak’i fad’a masa daga nan ban san ya akayi ba."
Kawu yace, "Da alama ya biyo ki ya samu labarin komai, Yanzu dai ban bashi dama ba Ina tunani auren naki bai jima da mutuwa ba aga an fara zuwa wajan ki babu dad’i. Sai mutane ma suga kamar da gangan aka kashe auren naki.” Mamaa tace, "Meye rashin dadin? Ai babu idda a kanta ba shikenan in tayi auren ta huta ba?. Su maganar mutane ai ko yaushe a haka suke, in kayi daidai suyi magana in basu yi daidai ba nan ma suyi magana. Dan kawai in abu yazo kawai ayi kar ace za’a tsagaita sabida bakin mutane.”
Kawu yace, "To shikenan daman ya bani lambar sa zan kira shi sai na bashi dama yazo su gaisa kafin komai ya biyo baya." Mama tace, "Hakan yayi to Allah ya Muna mana. İn kuma zuwa goben Abban su ya dawo shikenan sai ayi maganar dashi.” Ya amsa da Amin yayi musu sallama ya tafi.
#Nana Haleema
#Mai daki book2
#F5
Book2
005
A Daren Fiddausi ta labartawa Zakiyya komai suna ta murna cikin farin ciki Fiddausi tace, "Yanzu dai na kusa zama matar Alhaji, Wayyo Allah kamar a mafarki haka nake ganin abun wallahi." Zakiyya tace, "Bari kawai, an sha gwagwarmaya kafin azo nan."
"Amma fa akwai sauran damuwa har yanzu."
"Mecece ita?."
"Abba, Wallahi babu lallai ya amince da auren nan cikin kwanakin nan."
"Ba kince yana qauye ba?." Fiddausi tace, "Yana qauye, amma kin san zai dawo ai." Zakiyya tayi shiru kafin tace, "Addu'a zamu dinga yi masa Allah yasa ya amince ayi a wuce wajan kawai."
"Sai dai addu'ar kam wallahi, Mama na kira na Ina zuwa" ta fad'a tana kashe wayar ta fita dan ta jiyo kiran da Mama take mata.
Zama tayi Mama ta kalle ta tace, "Daman batu ne akan wanda yaje wajan kawun ki neman auren ki." Fiddausi tayi shiru bata ce komai ba Mama tace, "ya akayi yasan auren ki ya mutu har kin gama idda Fiddausi?." Fiddausi tace, "Ban sani ba Mama, na tabbatar kuma nbaZakiyya ce ta fad'a masa ba dan da zata fad'a min."
Mama tace, "Abin ne da mamaki, ya akayi ya sanki har yasan gidan nan da labarin ki?. Yanayin yadda ya kawo kansa kamar da akwai sabo tsakanin ku."
Fiddausi tayi dariya tace, "To Mama a ina zan ga wannan babban mutum din har mu saba? Kuma yaushe auren nawa ya mutu da zan fara kula wani?."
"Hale ne Fiddausi, amma abin akwai daure kai fa. Dan yasan auren ki ya mutu wanna ba wani abun bane, amma ya akayi yasan cikin ki ya zube babu idda yanzu?."
"Allah ne masani" ta fad'a tana kallon wani wajan daban dan bata so maganar tayi tsaho.
Mama tace, "Shikenan Allah yasa ku daidaita." Ta amsa da amin ta tashi ta koma d'aki a ranta tana Jin tsoron dawowar Abba dan tasan sai ya maimaita mata abinda Mama ta fad'a yanzu gashi shi ba irin Mama bane da wuri yake saurin gano k'aryar mutum.
Yadda take kuka sai ka d'auka zane ta akayi ko kuma wani gaggarumin abun aka aikata mata, bil hakki kuka take irin kukan wanda aka cuta ko aka yiwa rasuwa babba take yi da iyakar karfin ta, yana zaune gefen ta gabad'aya ya damu ji yake kamar shima yayi kukan hankalin sa duk ya tashi zuciyar sa babu dad'i hakan har ya bayyana akan fuskar sa.
"My love dan Allah ki bar wannan kukan." Sai a sannan ta d'ago ta kale shi tace, "Na d'auka za muyi zaman lafiya nida matar ka ashe ita a wajan ta ba haka bane, dan Allah ka bata hak'uri kace mata ba Ina niyar auren ka dan na ci fuskar ta ba."