Sashe 29
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna cikin hira ya sake kiran ta a waya ta d’auka tana murmushi tace, "Baby." Daga can yace, "Na'am baby, daga k’arshe kin zama mallakina yanzu sai shirin tafiyar Mun New York ko?." Dad’i ya mamaye mata zuciya tayi dariya tace, "sai burina da na fad’a maka Ina son cikawa da zarar an d’aura mana aure."
"Ibrahim?."
"Eh shi baby."
"Shikenan yanzu zan saka duk inda yake a kama shi a kulle shi sai ya kwana a cell."
Tayi murmushi tace, "thanks you baby, sai na jika" ta fad'a tana kashe wayar ta kalli k’awayen sukayi dariya gabadaya aka tafa aka cigaba da tsokanar ta.
Ibrahim kuwa yana cikin masallacin d’aurin auren wani abokin sa ya kaishi masallacin a nan yaga Kawun ta kuma yaji an d’aure auren Fiddausi da sunan mahaifin ta a nan ya tabbatar auren ta akayi, sai da aka d’aura nata aka d’aura na abokin nasa. bayan an kammala ya dawo gida ya samu Hajiyar sa a falo ya zauna ya kalli Fadima yace, "Faty bani abinci Yunwa nake ji." Amir da suka shigo tare yace, "Hajiya naga Kawu a masallaci."
Ibrahim baice komai ba aka kawo masa abincin ya fara ci yana cikin ci Alhaji ya shigo da sallama duk suka amsa ya zauna yace, "Ibrahim yau babu aikin ne?." Yace, "eh yau juma'a ban cika zuwa ba daman."
"Sai kuma naji batun d’aurin auren tsohuwar matar ka, wallahi mahaifinta tun daga Saudia ya kira ya sanar dani ban samu damar zuwa ba saboda d’aurin auren yaron nan da aka bani wakilci. D’aurin auren ne duk ya koma juma’a yanzu shiyasa ban samu dama ba.” Ibrahim yace, "Eh ban ma sani ba sai a masallacin naji.”
Hajiya tace, "Au har tayi aure?." Alhaji yace, "An d’aura aure ta da Bello Sagagi d’azun nan." Hajiya ta girgiza kai tace, "Bello Sagagi...! To Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman Lafiya." Alhaji ya amsa sa amin kafin yace, "rabon auren nata da wannan din ne ya kashe na Ibrahim. Kai yaushe zaka yi auren ne?." Ibrahim yayi murmushi yace, "Wallahi Alhaji nima ban sani ba."
Hajiya tace, "nima nace ya nemo yayi auren ko dan yaron nan kaga yanzu uwar sa nisa zatayi dashi zai so wacce zata maye gurbin ta."
Alhaji yace, "Haka ne, amma ya tsaya yayi komai a nutse har Allah ya kawo lokacin." Hajiya zatayi magana aka ji ana cewa, "Asslamu alaikum!." Alhaji ya kalli kofar falon zaiyi magana Sadik ya shigo yace, "Alhaji yan sanda a waje." Ibrahim ya tashi tsaye shida Alhaji yace, "y’ann sanda kuma a k’ofar gidan nan? Ibrahim muje."
Tare suka fita suka tarar da mota a gefe ga kuma wani guda d'aya a tsaye suka gaisa da Alhaji dan sandan yace, "Alhaji kaine Ibrahim?." Ibrahim yana gefe yace, “nine Ibrahim ." Ya kalli Ibrahim yace, "Zamu je da kai station ana tuhumar ka da dukan matar aure." Ibrahim ya kalli Alhaji ya sake kallon d’an sandan yace, "Dukan matar aure? Kuma ni?." Ya girgiza kai yace, "kai fa, muje" ya fad'a yana nuna masa hanya.
Alhaji yace, "officer anya d’ana kuke nema?." Ya girgiza kai yace, "Eh alhaji, shine."
Alhaji yace, "Amma d’ana babu macen da ya daka ai."
"Shiyasa zamu je ai in ba laifin sa bane zai dawo." Ibrahim ya kalli Alhaji yace, "Alhaji ka koma bara naje na dawo." Alhaji yace, "Wanne station zaku je dan Allah?." D’an sandan yace, "Bompai" ya fad'a yana yin gaba Ibrahim ya shiga motar suka tafi zuciyar sa duk babu dad'i dan ba k’aramin tozarci bane shiga motar y’an sanda. Tunanin sa shin wacce matar aure ya daka?.
Ina fama da mura ne ayi min hakuri.🥹
#Mai daki
#Book2
#Paid
#Nana Haleema
#09030398006
Book2
019
Suna shiga station d’inn Maimakon a kai shi kan kanta kawai aka bud’e cell aka saka Ibrahim, Ibrahim yace, "Akan wanne dalili kuka kawo ni nan? Ina matar da take k'arar nawa?." D'an sandan yace, "ka yiwa mutane shiru zata zo ai." Ibrahim yayi shiru ya kalli inda aka saka shi duk wajan yayi daud'a ga wari da wajan yake yi zuciyar sa har tashi take yi.
A lokacin Alhaji ya iso shida yayyen maza suka yi wajan yan sandan bai San me suke cewa ba yaga dai suna magana shi kuma yana tsaye yana kallon su. Har la’asar suna wajan ko sauraron su ma sun k’i yi balle su bada Ibrahim beli suka dawo kusa da ibrahim Yaya yace, "Ibrahim wa ka daka ne?." Ibrahim yace, "Wallahi babu wanda na daka, to wacce macen ma zan daka koda bata da aure balle mai aure? Me zai had’a ni da ita da zan dake ta?. Ni sallah nake so nayi wajan nan bazai sallah ba sun ‘ki bani dama."
Alhaji yace, "Sun ‘ki su bamu dama ne wallahi, sun k’i fad’a mana wacece ta kawo k’arar." Ibrahim yace, "ni su barni nayi sallah ma shi nake so wallahi." Alhaji ya koma ya sake yi musu magana dakyar aka barshi ya fito yayi sallah suka mayar dashi har magriba su Alhaji suna nan ance sai D.P.O yazo amma shiru bai zo ba.
Ibrahim yace, "Alhaji ku tafi gida kawai dare yayi." Alhaji yace, "taya zamu tafi mu barka a nan bayan bamu San abinda kayi ba? Wacece tayi k’arar?.” Shiru suka sake yi suka koma gefe suka zauna suna jiran tsammani, Babban mutum ne ya shigo irin manyan nan masu kama da y’an dambe sanye da kayan security bayan sa Fiddausi ce ta saka hijjabi har k'asa bata kula dasu Alhaji ba wajan Ibrahim ta nufa tana bin sa da kallon k’ask’anci tace, "Ka gane ni ai ko?."
Baiyi magana ba sai kallon ta da yake yi domin kuwa ta jima tana zuwa zuciyar sa akan lamarin bai gasgata ba sai da ya ganta tace, "Sakamakon marina da kayi lokacin da Ina gidan ka kenan, nan gaba akace ka sake yiwa wata macen ai baza ka sake yi ba. Yanzu ka tabbatar da ni ba irin matan da zaka daka bace ka zauna lafiya ba ko?, yanzu ka tabbatar ni ba sa’ar ka bace, ka tabbatar a yanzu baka wuce driver gıdana ba. To wallahi kayi a hankali nan gaba zan iya sakawa a yi maka duk abinda nake so koda daga garin ne zan iya sakawa a b’atar da kai. yanzu ni matar manya ce ka kalli bayan ka har masu kula da lafiyata ne suke yawo dani. Darajar ka d'aya Amir wallahi sai na tura ka kurkuku kayi wata biyar dan ka sake tabbatar da wacece Fiddausi a yanzu, amma na kyale ka saboda Amir ko babu komai ni na haife shi tare da kai, a yanzun ma sai ka kwana a nan dan ka gane ikon da nake dashi a yanzu."
Kallon ta kawai yake yi itama haka ido cikin iso tana hararar sa amma baice mata komai ba sai kallon, “daman ke kika saka a kama shi Fiddausi?." Muryar Alhaji taji sai ta rufe ido ta bud’e da tasa suna wajan ai baza ta zo ba sai gobe ta jiyo ta kallo Alhaji tace, "Alhaji barka ai ban kula daku ba, sannn ku."
"Ke kika saka a kama shi Fiddausi?" Ya sake maimaita mata yana kallon ta.
"Eh Alhaji" ta amsa a takaice tana kallon wani wajan daban. Yaya yace, "Akan me kenan?."
"Saboda Marin da yayi min har bakina ya fashe, wannan shine sakamakon abinda ya aikata."
Alhaji yace, "To tunda kin d’auki mataki ba sai ki kyale shi ya tafi ba." Fiddausi ta kalli Ibrahim tace, "Sai ya bani hak’uri ko na rama marin da yayi min.”
Ibrahim yace, "Har abada, koda zaki saka a kaini lahira bazan baki hak’uri ba Fiddausi. Baki kai wannan matsayin ba ai har yanzu.”
"Zaka dawwama a wajan nan kuwa daga nan har sati d'aya." Dan sanda ne ya k’araso yana cewa, "Ranki ya dad’e ai ban san kin zo ba, ga waje ki zauna, Alhaji ya sanar mana da zuwan ki bamu san kin k’araso ba." Ta kalle su tace, "ba zama zanyi ba, kawai so nake ku saka ya bani hak’uri sai na kyale shi."
Dan sandan ya kalli Ibrahim yace, "Ka bata hak’uri a wuce wajan dan laifin da ka aikata ba ‘karami bane." Ibrahim yayi murmushi yace, "Har Allah ya tashi duniya indai hak’uri zan bata." Ta kalli dan sandan tace, "A cigaba da tsare shi har sai na bada umarnin a sake shi" ta fad’a tana niyar tafiya sai suka had’a ido da Alhaji da yake kallon ta yana mamakin wai daman haka take tace, "ku sake shi yaci albarka in mahaifin sa da nake ganin girma, amma wallahi sai na nuna masa ruwa ba sa’an kwando bane" tana fad'a ta juya ta fita wanda suka shigo tare yabi bayan ta.
Har suka koma gida babu wanda ya iya cewa wani abu a cikin su, ibrshim wanka yayi sannan yayi sallah ya samu har lokacin suna zaune ana bawa Hajiya labarin abinda ya faru. Hajiya da take kallon sa da ya shigo tace, "Yanzu Fiddausi ce ta yiwa Ibrahim haka? Itace ta saka a kama shi dan tana ganin yanzu ta auri mai kud’i a yanzu?." Yaya yace, "Ta bani mamaki sosai Hajiya, in kika ga yadda take magana baza kice ta had'a jini da Ibrahim ba wallahi. Badan Alhaji ba ko ai sai na sanar da magabanta ta wallahi domin a tsawatar mata saboda gaba."
Hajiya tace, "Ai abinda ya kamata ayi kenan, Alhaji ai mahaifinta zaka fad’awa kar nan gaba ta saka yan daba su sara shi." Alhaji sai a sannan yace, "Sai mahaifin nata ya dawo daga umra zanje na same shi dan abinda tayi ba abu bane wanda za'a kyale, badan Muna wajan ba ban San lokacin da Ibrahim zai fito ba. Kin San halin sa da taurin zuciya tace sai ya bata hak’uri ni kuma na tabbatar da ko me za'a yi Ibrahim bazai bata hak’uri ba."