← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 42

Sashe 41

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rukayya gabad’aya ba jin ta take yi ba hankalin ta ya tafi wani waje tana kuma bukatar shawara da k’awayen ta guda uku amma ta ina zata fara fad’a musu wannan maganar? Anya babu cin amana a lamarin? Anya babu yaudara a cikin wannan abun da yake k’ok’arin faruwa?. Abinda ake fad’a Ana dariya gashi yanzu yana so ya zama gaske. Tab’a ta Umma tayi hakan ya saka ta dawo daga tunanin ta kalli Umma tace, “in sha Allah Umma zanyi addu’a, ko ina alkhairi yake Allah ya had’a ni dashi.” Umma tace, “Allah yasa” ta fad’a tana tashi ta fita ta barta tana hasaso fuskar Ibrahim sai gaban ta ya yanke ya fad’i. A haka itama ta tashi ta shiga d’aki jikin ta a mace gabadaya, Umar ko Ibrahim?.

A b’angaren Yusuf tun bayan da akayi maganar a gidan su babu wanda ya sake yi masa maganar kowa ya share shi ya kuma zuba masa ido yaga iyakacin gudun ruwan sa, ko gidan yaje sai dai a gaisa kawai amma babu wani mai sakewa dashi ayi hira kowa ya d’aure masa fuska. Ammah kuwa a ciki take amsa gaisuwar sa daga nan babu wata magana da zata sake yi masa.

Yana cikin tuk’in mota yaji k’arar shigowa sak’o a wayar sa bai duba ba sai da ya shiga gida ya faka motar ya fito sannan ya dauki wayar sa yana dubawa, sunan Adam ya gani yayan Ameena nan take gaban ya fad’i ya kulle ido ya furzar da iska daga bakin sa sannan ya bud’e Idon hannun da yana rawa ya bud’eSakon yaga abinda ya rubuto kamar haka,

_Yusuf banda darajar iyayen ka da yanzu na d’auki mataki a kanka, nayi shiru kai kuma naga baka San shiru ba, to ka gaggauta kawowa Ameena takardar sakin ta in kuma ba haka ba ka kuka da kanka duk abinda nayi maka._

Yana gama karantawa ya sauke numfashi kansa ya sara yayi saurin dafewa, ya rasa meyasa yanzu inda za’a ambaci Ameena sai gaban da ya fad’i kansa kuma ya sara, ko kuma yaji kamar Ana tafasa masa jinin sa hakan ya saka baya so a ambace ta a gaban da gabadaya jinyar wucin gadi yake tafiya in hakan ta faru sai dai ya daure kawai. Cikin gidan ya shiga ya samu Asiya a falo a zaune ta d’ora k’afa kan d’aya cikin shigar da ta saba, zani da kuma riga mai karamin hannu sai kuma dankwalin da bai yi Kala da zanin jikin ta ba.

Falon kaca-kaca taci abinci ta bar kwanon a wajan ga kofi ga robar ruwa duk a wajan tana kuma zaune tana kad’a kafa ba tare da hakan ya dame ta ba. Bai zauna ba ya wuce sama kawai ganin hakan sai ta d’auki waya ta saka a kunne kafin tace, “ya shigo Yanzun nan amma baiyi min magana ba.” Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta sake cewa, “nifa so nake nayi masa tsawa kamar yadda yake min, duk abinda nake so shi nake so yayi burina bai wuce ya saki waccan matar tasa ba.”

Sake yin shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tace, “bara naje yanzu.” Katse kiran wayar tayi ta mik’e tabi bayan sa ta same shi a zaune a gefen gado ya dafe kai har ta shiga bai sani ba ta k’arasa inda yake tace, “My love me yake damun ka haka?.” D’agowa yayi ya kalle ta yace, “Meyasa in na ajjiye kud’i a dak’in nan bana ganin su? Ina suke zuwa?.”

K’are masa kallo take yi kafin tace, “kenan kana so kace sata nake maka ko me?B’arauniya ce ni?.” Jin yadda ta tambaya sai ya samu kansa da kasa bata amsa yace, “A’a ba haka ba, kawai dai ban San inda nake kai su bane shiyasa.” Murmushi tayi jin abinda yace sai ta zauna tace, “watakila baka shigowa dasu ne shiyasa. Me yake damun ka?.”

“Nima ban sani ba, amma Ina kina kamar ba ni bane.”
“Kaine, dalilin jin ka a haka saboda baka saki Ameena bane da ka sake ta shikenan an wuce wajan.” Ya sake dafe kansa yace, “ban san meyasa bana so naji sunan ta a kusa dani ba, zuciyarta tana son taji sunan amma kuka kunnena baya son yaji an ambaci sunan ta.”

Asiya tace, “kawai ka sake ta, in ka sake ta zaka daina jin abinda kake ji.” Dan ja baya yayi dan bakin ta da jikin ta gabad’aya wari yake yi amma baya so ya furta dan kar ranta ya b’aci. Tashi tayi ta d’auko ‘karamin jotter na store din sa da biro tace, “ka rubuta ka sake ta kawai ka huta.” Kallon takardar yake yi sai ya mik’e tsaye yana girgiza kai yace, “bazan iya sakin ta ba, ki kyale ni” yana fad’aya fita ya barta a tsaye a wajan tana kallon sa cikin tsoro.

Sauka yayi daga gidan gabad’aya zai shiga b’angaren Ameena yaji ana yi masa waya ganin sunan mahaifin sa sai ya d’auka ya kasa a kunne sai kuma ya fasa shiga gidan ya koma saman Asiya ya samu bata d’akin ya d’auko key din mota ya sauka ya fita shiga ya nufi gidan nasu.

A falo ya samu mahaifin nasa shida Ammah a zaune ya shiga da sallama ya zauna Abbah ya kalle shi sai ya kalli Ammah suka had’a ido ya sake kallon Yusuf din yace, “Masu karb’ar sample din nan ne suka zo, sark’ar tana nan ko kuma itace wacce kace Ameena ta sace maka?.” Yayi shiru ya runtse idanu yace, “in aka ambace ta Abbah ji nake kamar ana sara min kaina, zuciyata ta kuma ba haka nake ji ba.”

Abbah ya kalli Ammah ya sake kallon sa yace, “Saboda tsanar da kayi mata har ta kai baka son a fad’i sunan ta ko?.” Shiru yayi ya sunkuyar da kansa k’asa Abbah ya kuma cewa, “ina tambayar ka, itace sark’ar ko ba ita bace?.”
“Itace” ya furta ba tare da ya d’ago ba. Abbah yace, “Yaushe zaka kai mata takardar sakin ta? Kasan yayan ta badan mu ba da yanzu kana hannun hukuma ko?.”

Yusuf yace, “na kasa aikata hakan ne Abbah” ya fad’a a sanyaye sosai kamar zaiyi kuka har Ammah ta kalle shi sai kuma ta d’auke kanta. Abbah yace, “Baka isa ba kuwa, Tunda Baka son ta sai ka sake ta, ga takardar da biro nan yanzu ka sake ta dan in y’ata ce nima wallahi ta gama zama dakai.”

Yusuf ya kalli jotter din da Abbah ya nuna masa yaga sune a jiki shida ita ranar sunan Zaytun ya d’auke idanun sa yana sauke numfashi yace, “Abbah bazan iya sakin ta, ina ji a zuciya bazan iya hakan ma amma gangar jikina bata jin hakan. Abbah dan Allah kar kace na sake ta bazan iya ba” ya fad’a muryar sa na rawa sosai Abbah yayi murmushi yace, “Yusuf ai Baka isa ba, saki ya zamar maka dole kayi ko baka so.”

Yusuf ya kulle ido ya bud’e zafin da yake ji a zuciyar sa har a idanun sa yaji yake ji dakyar yace, “ina so na fara magana da ita sannan…..” Abbah yace, “baza ka ganta ba, ka sake ta nace yanzu nan kaje ka zauna da amaryar ka tunda ita kake so. Kayi magana da ita kace mata me? Ka sake mata daman alfarmar babar ka take ci kake zaune da ita? Ko kuma ka sake d’ora mata ciwo?.” Yusuf yayi shiru bai ce komai ba Abbah yace, “da gaggawa rubuta sakin nan dan wallahi sai ka sake ta, tunda har ka iya kyale yarinya kamar ta ba tare da kana sauke hakkin da Allah ya d’ora maka ba dole ka rabu da ita.” Yusuf ya d’auki biron ya bud’e jotted din yana so ya rubuta amma zuciyar sa hana shi aikata hakan take yi.

_Ameena fa Yusuf, Ameena ka da kake so kake qauna ita zaka saki? Ina zaka kai hakkin ta da yake kanta? Kenan kun rabu wani zata aura kenan ko me?. Zaka iya rayuwa babu ita kenan? Kana sonta fa meyasa zaka sake ta?._ Abinda Zuciyar sa take fad’a masa kenan sai yake ji kamar rad’a masa ake a kunnen sa bai san lokacin da ya runtse ido yace, “Wayyo Allah, bazan iya ba!.” sai ya ajjiye biron yace, “Abbah…..” Abbah ya dakatar dashi a fusace yace, “Tunda ka iya dukan ta, Tunda ka iya saka mata hawan jini, Tunda ka kasa sauke mata hakkin ta da yake kanka har ta kai ya kawo tana shan maganin da zata kare kanta daga fad’awa halaka, Tunda ka kira ta da b’arauniya, Tunda kace kai ba sonta kake ba Ammah ce ta saka ka auro ta wallahi sai ka sake ta Yusuf kaji kuma na rantse baza ka saka ni yin kaffara ba. In Humaira ce a matsayin ta hukuncin da zan yanke kenan itama kuma y’ata ce ya zama dole ka sake ta ko kana so ko baka so.”

Jin Abbah ya rantse ya saka Yusuf hannu yana rawa ya fara rubutu akan takardar yana kuka a zuciyar sa kafin ya gama gumi ya gama wanke masa fuska duk ya d’iga a jikin takardar kamar wanda yake rubuta jarabawa mai tsauri. Abbah ya mik’awa ya karb’a ya karanta sannan ya mik’awa Ammah ma ta duba ya karb’a ya bawa Yusuf din yace, “kaje har gida ka kaiwa Yayan ta kamar yadda yace maka, Kaga yanzu mun zama shaida koda baka kai ba mun tabbatar da ka sake ta saki d’aya.”

Shiru yayi bai magana ba bai kuma tashi ba dan ji yake in ya mik’e zai iya kifawa ga zuciyar sa da yake ji kamar zata fito daga k’irjin shiyasa ya kasa ko motsin kirki, Abbah yace, “tashi ka bani waje.” Dakyar ya tashi jiki a sanyaye ya fita kamar kazar fa kwai ya fashewa a ciki shi kad’ai yasan abinda yake ji a zuciyar sa.
Chapter 41 · 0% Book details