Sashe 10
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaya ta fuskance ta tace, "Yadda kika ce min ke kad’ai kika zo hakan ya tabbatar min da bai San kin tawo ba." Ameenatu ta tab'e baki tace, "Yaya ko ya sani ba damuwa zaiyi dan zan tawo ni kad’ai ba, nifa arzukin Amma nake ci da take sona da yanzu na jima a gidan nan."
"Bai dai sani din ba, in ya sani bazai barki ki tawo ba ai Kano zuwa Bauchi ba tuk'in mace bane Ameenatou. Meyasa kika yi doguwar tafiya haka mijin ki bai sani ba?."
"Ina yake da lokacina da zan fad’a masa Yaya? Na fad’a masa dai Ina Jin shekaran jiya ne yayi min banza bai amsa ba ya fita, ni kuma yau ji nayi bazan iya cigaba da zama a gidan bane gwara na tawo nan."
Yaya ta sauke numfashi tace, "Kowa ya ganki yasan kin rame Ameenatu, za’a yi tunanin kin yi rashin lafiya ne ko kuma kina da ciki ko kuma akwai damuwa a tare dake" ta rik’e hannun ta tace, "Damuwar nan da kike sakawa a ranki ba itace mafita ba Ameenatou, addu'a itace kan gaba a wajan maganin damuwar ki in kina addu'a mantawa zaki yi da komai." Idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Ina yi wallahi Yaya, ko bazan yi sallah ba na saba sai na tashi da daddare nayi lazumi nayi addu'a har gari ya waye, badan Ina addu'ar bama da ban San ya zan koma ba."
Yaya tace, "to kishin ne a zuciyar ki haka?." Ameenatou tace, "Da Ina kishi amma yanzu bana yi Yaya, wallahi Yaya na yarda da tasirin addu’a domin kamar ba’a yi kishin Yusuf a zuciyata ba yanzu, ina ji amma ba kamar baya ba. Sannan duk wani abu da kika sani nasa ya fita daga raina shiyasa wannan ba shine abinda yake damuna ba. Damuwa ta sai a kwana a tashi bai damu da ya nake ba ba balle kuma ya kika kwana jiya, in kin ganshi a inda nake to tabbas Zaytun ce babu Lafiya."
"Ameenatu kuma ba wani abun kika yi masa ba?."
"Yaya kema fa kin zo gidan kinga ya nake ciki, har kika zo tafiya bai bani damar ganin sa ba balle nace masa kinzo yana d’aki yana waya da matar da zai aura. Me nayi masa Yaya?" Ta fad’a hawaye na sakko mata tayi saurin gogewa.
Ta sake kallon Yaya tace, "Yaya asibiti a d’ora ni akan maganin hawan jini......" ta ‘karasa fad'a tana fashewa da kuka sai kuma ta cigaba da cewa, "İn na cigaba da zama da Yusuf wallahi ciwon zuciya ne zai kama ni, yau duka gobe zagi jibi fad’a akan wacce zai aura, dame zanji?. Yaya bani da kowa a kusa y’an uwan mu da muke uba d’aya kinfi kowa sanin halin su, ko wacce burin ta taji damuwar da y’ar uwar ta take ciki badan ta taya ta jimami ba sai da tayi farin ciki ta yad'a, zumuncin uwa daya uba d’aya kawai muke yi. Inda ace akwai zumunci mai k’arfi tsakanin mu Yaya bazan zo Bauchi ba a wajan su zan zauna, a dangi mama ko dangin Abba wa zanje na fad’awa damuwa ta? Yaya Adam ne gata na wanda zai tsaya min shi kuma yayi min nisa a yanzu ko a waya bana samun sa. Ke kad’ai nake da ita a duk duniya Yaya, dan Allah ki barni na zauna a anan har a gama bikin sa na koma."
Shiru Yaya tayi tana rik’e da hannun ta har lokacin ita kanta zuciyar ta ta karye amma bata son yin kukan saboda kar ta sake karyawa Ameenatu zuciya hakan ya saka ta daure tace, "Shikenan to ya isa kukan, Allah zai shiga cikin lamarin ki in sha Allah." Ameenatu ta goge idanun ta ta kalli wayar ta tace, "kin gani ki Yaya, na tabbatar yaga bana gidan amma bai kira ni yaji Ina naje ba, yasan ban saba fita ban fad’a masa ba tunda yaga bana nan yasan akwai inda naje amma bai kira ba saboda bai damu ya sani ba."
Yaya tace, "Kiyi hak’uri komai zai wuce ai Ameenatu lokaci ne zaiyi dana sanin duk abinda yayi miki. Kuma wallahi a jikina nake jin har gobe Yusuf yana sonki, wani dalili ne ya saka yake yi miki wannan abubuwan Ameena.”
“Yaya ba wani so wallahi, ba kukan canjawar da zaiyi in ma zai canja watak’ila lokacin ya kashe ni ai Yaya, duk yadda zan miki bayani baza ki gane ba Yaya. Yarinyar da zai aura fa har ta fara had'a ni fad’a dashi yazo yaci min mutunci a gaban Rukayya da daddare ya sake dawowa ya sake fad’a min maganganu marasa dad’i har na kasa jurewa na fara mayar masa, shiyasa a safiyar yau d’in na gudu nan, na gaji wallahi banza iya ba.”
Yaya tace, "Tabbas kudi ba shine kwanciyar hankali ba, ga kudin ga komai na rayuwar duniya a gidan auren ki amma kwanciyar hankali kika rasa. Mu kuma babu kud’in babu abubuwan more rayuwar amma Muna da kwanciyar hankali alhamdulillah. Kowa da yadda Allah yake tsara masa rayuwar sa Kiyi hak’uri wata rana sai labari." Shiru tayi na wani lokaci tana jan numfashi bata ce komai ba.
Yaya tace, "Allah ni da naji kina zancen ma zaki yaye Zaytun d’auka nake ciki ne ma dake." Bata san lokacin da tayi murmushi ba amma bata ce komai ba tayi shiru. Yaya tace, "Saura kwana nawa bikin nasa?."
"Wallahi ban sani ba” ta fad’a murya na yin rawa.
"Bazan bari ki zauna a nan ba Ameena in nayi hakan na zama Babbar banza ai, zaki zauna dai na kwana biyu zuwa uku sai ki koma."
Ta kalli Yayan tace, "Na koma ya kashe ni kenan?."
"Bazai kashe ki ba Ameena, ko wacce mace hak’uri take a gidan mijin ta baki San abinda yake k'unsa mata ba amma daurewa ake a kawar komai sai a zauna lafiya." Ameena tace, "Yaya dan baki San zaman da nake dashi bane shiyasa kike cewa na koma. Yaya magani fa nake sha kin manta?.”
Yaya tayi murmushi tace, “Ban manta ba Ameena, bazan tab’a mantawa ba ai Ameena. Ki dai huta na kwana biyu Ameena, Allah ya k’ara mana hak’uri baki daya" ta fad'a tana tashi tana fita tare da goge idanun ta, babu yadda zata yi ne amma da Ameena bazata koma ba, da ace akwai Wanda zai tsaya musu wallahi bazata koma gidan sa ba, to meye amfanin zaman gidan? Komai lalacewa gidan mijin ka yafi rufin asiri musamman a wajan su da basu da iyaye.
Yusuf koda ya tashi yaga babu motar ta bai bi ta kanta ba ya fita yaje gidan su suka gaisa da iyayen sa ya wuce store, saboda aikin ginin sa da wuri ya dawo ya sake ganin babu mota nan ma bai wani mayar da hankali ba ya cigaba da abinda yake gaban sa.
Fita ya sake yi bai dawo ba sai bayan i'sha ya sake ganin babu motar ta ya hau sama yayi wanka ya saka kaya lokacin karfe tara na dare ya duba compound din gidsn ta window amma babu motar ya sakko zuwa d’akin ta dan a tunanin sa ko ta kai motar gyara ne. komai na d’akin yana kashe da alama bata dawo ba taja tsaki ya hau saman ya d’auki waya nemo number ta ya kira amma is not reachable. Zai sake Kira kenan kiran love ya shigo nan ya datse kiran ya kira ta suka fara wayar da suka saba.
A haka yayi bacci ya manta ma da batun kiran Ameenatu.
Da asuba ma da ya tashi ya manta da batun bata nan bai sauka masallaci ba dan ya makara sallah yayi a d’akiki kawai ya kwanta. Kiran wayar sace ta tashe shi ya d’aga kai yaga k’arfe goma na safe ya kalli wayar yaga sunan Amma ya d’auka da sallama yace, "Amma barka da safiya." Daga can ‘bangaren tace, "Barka dai, Ina Ameenatu ne Ina kiran ta bana samu tun jiya, na aiko tun jiyan akace bata nan. Had’a ni da ita yanzu zamuyi magana."
Yusuf gaban sa ya fad’i tunawa da bai fa ganta ba jiya ya diro daga kan gadon yace, "Tana d’akin ta bara na kai mata" ya fad'a yana sakkowa k’asan bayan ka kashe wayar ya shiga d’akin Ameena. Yadda d’akin yake komai a kashe babu haske zai tabbatar maka da mutum bai kwana a ciki ba, gaban sa ya fad'i ya dafe kai yace, "Me hakan yake nufi wai?."
Da sauri ya ‘karasa ya bud’e band’aki amma babu kowa ya fito daga d’akin ya shiga na kusa dashi amma duka bata nan, ‘kasa ya sakko ya duba kitchen da ko Ina amma bata nan. "Innalillahi, Ina yarinyar nan taje ne wai?" Ya fad'a tana fita gate yana fad’in, "Baba! Baba isihu!." Baba Isihu ya k’araso da sauri yace, "Yallabai barka da safiya."
"Barka dai, nace matar gidan nan ta fita da safen nan ne?."
"Yallabai ai tun jiya da safe kamar k’arfe bakwai zuwa takwas da ta fita da mota bata dawo ba har yanzu."
"Hasbunallahu wani'mal wakil!” Ya fad’a yana dafe kansa kafin ya kalli Baba yace, “Shikenan na gode" ya fad'a yana komawa ciki nan take wayar sa ta fara ‘kara kiran Amma na shigowa.
"Na shiga uku me zan cewa Amma ne?." Hankali a tashe ya d’auka ya saka a kunne Amma tace, "Ina take ne?."
"Ammm tana bandaki ne in ta fito zan kira ki" ya fad'a a diririce. Amma ta yanke wayar ya dafe kai ya sake fita.
‘Bangaren d’akin masu aikin ta yaje suka ce masa tun safiyar jiya bata dawo ba. Hankali tashe ya koma ciki yana kiran ta amma har lokacin wayar bata tafiya yana ta zagaye a falon ya rasa abinda yake masa dad’i. Hankalin sa ya tashi dan bata tab’a aikata haka ba duk inda zata je tana fad’a masa.