← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 42

Sashe 31

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya sai ta kalle shi suka had’a ido zatayi magana yace, "Gaskiya zaki fad’a min kawai bana son wata magana." Asiya ta sauke numfashi tace, "Banyi niyar fada maka ba My love, yanzu ma Umma da ita muka gama waya tace kar na fad’a maka ita aka yiwa kuma komai ya wuce. Amma dan Allah ka yiwa matar ka magana cin fuskar ta da cin mutuncin ta ya tsaya iya kaina ta daina saki mahaifiyata a ciki, Ina girmama ta kar ta saka nan gaba kazo ka tarar Muna dambe Kaga hakan bazai maka dad’i ba." Yusuf ya sauke numfashi yana kallon ta yace, "Kiyi hakuri, ki bawa Umman hakuri in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba."

Ya goge ido tace, "Ran umma ya b’aci sosai tana ganin tayi jika da Ameena amma baka ji cin fuskar da tayi mata ba a gabana kuma Umma ta hanani na tanka" ta dago ta kalle shi tana hawaye tace, "Laifi ne da dan Umma na tazo gidan nan a karo na farko ta shiga wajan ta su gaisa?." Ya girgiza kai alamun A'a tace, "A yadda naga ana yiwa Umma a gidan Yaya Maimuna kafin mijin ta ya rabu da ita in muka je kishiyoyin ta har wajan ta suke zuwa su gaida Umma su koma, na d’auka yadda na d’auki Ameena haka ta d’auke ni; amma naga ba haka bane zan kama kaina."

Yusuf yace, "kiyi hak’uri nace dan Allah, zan kuma saka tazo ta baki hak’uri ta kuma je har gidan ku ta bawa Umman hak’uri abinda tayi bata kyauta ba sam, ki daina kuka kinji my love?." Murmushi tayi ta goge ido tace, "ni ko bata bani hak’uri ba ta bawa Umman tunda itama kamar uwa take a wajan ta." Shima murmushin yayi yace, "kar ki damu."

Murmushi itama tayi ya sake cewa, "Tafiya ta kama ni zuwa Dubai k’arfe sha biyu na rana, zanyi sati d'aya a can akwai abinda kike so?." Ta girgiza kai alamun A'a tace, "kawai zan yi missing din ka ne." Shima murmushi yayi yace, "nima zanyi missing din ki, kafin na dawo ki gyara kanki a kuma yi miki jan lalle yana kyau a hannun ki." Kai ta d’aga tana murmushi shima haka ya mik’e tsaye ya ajjiye mata kud’i yace, "Gashi nan koda akwai abinda zai taso, in kuma yafi k’arfin kud’in sai kiyi min waya na turo miki."

"To my love Allah ya kiyaye, yanzu zaka wuce?."
"Zan je dai gidan Ammah daga nan zan wuce."
"Baza kaje dani ba?" Ta fad’a kamar zatayi kuka.
"İn zan koma dake zamu je." Tayi murmushi tace, "Allah ya kaimu" ya amsa da Amin ya sauka.

A falon Ameena ya tarar da Amira da Zaytun suna zaune Amira ta daga tana koya mata turanci ganin shigowar sa Amira tace, "Sannu da zuwa." Ya kalle ta yace, "Amira jiya mahaifiyar Asiya ta shigo gidan nan?." Amira tace, "Eh tazo." Daga nan bai sake cewa komai ba dan daman so yake ya tabbatar ta shigo d’in ya wuce sama zuciyar a sama daman haushin Ameena din yake ji.

D’akin ya ya shiga ta fito daga wanka daga ita sai k'aramin towel kanta yasha kitso k'anana gashin ta yayi bak'i sosai fatar ta sai kyalli take yi, had'a ido sukayi yayi saurin janye idanun sa gabad’aya abinda yazo dashi ya gudu yana neman fita daga hayyacin sa dan yana bukatar matar sa sosai kawai rashin jin da take yi ne ya saka yake share ta dan taji a jikin ta dan shi yana da wata matar amma yau yaji abinda ya jima bai ji ba a kanta ba kuma ya tunanin zai iya kyale ta.

Ganin bai magana ba sai ta samu waje ta zauna ya daidaita kansa yace, "Ameena misali ace Maman ki na da rai sai tazo gidan nan ta shiga wajan Asiya a ci mata mutunci zaki ji dadi?." Ta kalle shi ta tsayar da abinda take yi tace, "Haka akace maka nayi kenan ko?."
"Ai hakan ne ma, domin yadda kike ji da tashen wulakanci da rashin kunya a yanzu zaki iya aikatawa."
"To shikenan haka ne" ta fad'a a hankali ta tashi ta d’auko kaya ta ajjiye a kan gado.

Yace, "Haka ne kenan kin yi?." Ta jiyo ta kalle shi tace, "Ba kai kace kasan zanyi ba? Shiyasa nace nayi saboda kar na k’aryata ka."
"Ina so yanzu kije ki bawa Asiya hak’uri sannan ki karb’i number mahaifiyarta ki kira ki bata hak’uri yanzu ba anjima ba." Ya jiyo ta kalle shi tace, "Bazan bada hak’uri akan abinda banyi ba, ko nayi matar ka bata kai matsayin na bata hakuri ba wallahi.”

Da mamaki yake kallon ta yace, "Kenan kina nufin kin aikata kuma baza ki bada hak’uri ba?." Ameena tayi shiru tana kallon sa kafin tace, "bazan iya ba." Fusata yayi matuk’a ya zazzaro idanu waje ya matso kusa da ita yace, "ni kike cewa baza ki iya ba Ameena? Ni kike kalla nace ki yi abu kice baza ki iya ba?." Ameena tace, "bazan bada hak’uri akan abinda ban aikata ba inda na aikata zan bada hakurin amma banyi ba bazan bayar ba....." zazzafan mari ya d’auke ta dashi ta dafe kunci tana kallon sa zuciyar ta na ingizata akan kawai ta rama itama amma batayi hakan ba ta kalle shi tace, "Akan abinda baka tabbatar na aikata ba ka mare ni?."

"Na mare ko Ameena ko zaki Rama ne?" Ya fad'a yana kallon ta. Tayi murmushi tace, "Bazan rama ba, amma tabbas wata ran ana aikata hakan zan rama domin jikina ba dan duka yake zaune a gidsn nan ba” ta fad'a hawaye na sakko mata ta saka hannu ta share ya bita da kallo itama shi take kallo tana kuka. Baki ya bud’e yana kallon ta idanuna waje yace,"Ameena zaki iya marina dan na mare ki kenan?."
"Tunda har kai ka iya zan iya mana."
"Lallai rashin kunyar ki ta fara wuce inda nake tunani, lallai Ameena ni kike kallo kike fad’awa wannan maganar dan baki da kunya. Duk wanda yake zuga ki akan wannan banzayen halayen cutar ki yake.”

Ameena tace, "koma meye kaine ka saka na zama haka Yusuf. Kuma zan cigaba da zama gaba da haka ma indai baka fasa ba.” Kwafa tayi dan in ya cigaba da zama abinda take zai iya b’alla ta ya wuce ya fita da sauri ta zauna akan gadon tana kuka.

Ba kukan Mari ko kukan an mata sharri take yi ba, kukan sa'insa da ta fara da mijin ta take yi dan tafi son zaman kuramen da suke yi akan yazo yana d’aga mata murya dan bata iya jurewa kamar lokacin baya koda tayi niya bata iyawa gabad’aya. Zuciyar ta ta bushe a kansa kiris take jira yayi abu ta mayar masa.
Tana jin fitar sa a mota ta daure itama ta tashi ta shirya ta sakko suka fita iya da Amira zuwa wajan Dr Mansura.

Bata dawo ba har dare dan gidan d'aya daga cikin y’an uwanta ta wuce suka yi hira duk da babu wani sakewa sosai amma babu laifi, har sha d'aya na dare babu Yusuf babu labarin sa dan taga babu motar sa duk da tasan a wajan Asiya yake. A haka tayi bacci dan ita bata san ma yayi wata tafiya ba.

Tsahon kwanaki shida kenan baya nan ganin bata ganin giftawar sa ga kuma motar sa tana nan hakan ya saka ta tabbatar baya nan, gabadaya ga manta ma da wata Asiya a gidan sai dai in tana tsaye a taga tana kallon harabar gidan Asiya taga ana fitowa da kayan abinci daga gidan ana sakawa a sabuwar motar da ya siya mata ana fita dashi. Bata tab’a kawo komai a ranta ba sai dai ta saki labulen kawai.

Ranar da ya cika kwana bakwai da daddare tana zaune a kasa bayan i’sha suna waya da Fiddausi tana fad'a mata irin soyayyar da suke kwasa da mijin ta tana ta darıya in Fiddausi ta fad’i wani abun, sosai Fidy ta zare akan soyayya hakan shine yake bata darıya. Sallama akayi aka shigo Yayar Asiya ce Maimuna da kanwar ta Momi sai ita a bayan su.

Sai da gaban Ameena ya fadi da taga sun shigo amma bata nuna ba ta yanke wayar ta mik’e tana fadin, "Barkan ku da zuwa, Bismillah ku zauna mana." Maimuna ta bita da kallon wulakanci tace, "ba zama muka zo ba ai, in zama muka zo ai baki isa ki hana mu ba saboda gidan k’anwata ne." Ameena tace, "Tofa!.”

Amira da ta sakko lokacin tana kallon su bata ce komai ba Momi tace, "Zuwa mukayi mu rama duk wani wulakancin da kike yiwa Asiya a gidan nan." Amira da take gefe tace, "Ku kuma daga Ina?." Ameena ta kalli Amira tace, "Amira muje ciki in kare yana haushi ba'a zuwa inda yake" ta fad'a tana zuwa zata wuce sai kuwa Asiya ta damk’o rigarta ta baya tace, "Uwar ki Sa'adatu da take cikin kabari itace karya kuka itace take haushi ba Yayata ba."

Ameena ta jiyo a fusace bata san lokacin da ta d’auke Asiya da zazaafan mari ba tana kallon ta tana kad’a yatsa tace, “kul! Kar ki sake kar ki kuma maimaiwa, Koda wasa nan gaba kika sake zagin mahaifinta sai nayi miki abinda yafi haka.” Amira tazo wajan tace, "Kinyi daidai Mummy, nuna mata bata isa tazo har gidan tayi miki hauka ba.”
Maimunatu ta kalli Momi sai Momi ta fita daga falon sukayi kan Ameena zasu dake ta.

Ameena tayi baya Amira ma taja ta tsaya tana hararar su tace, "Tunda tashin hankalin kuke ji dashi na rantse da Allah daidai daku nake." Marin ta Asiya tayi sai kuwa tayi tsalle ta rama itama tana cewa, “ke baki San haushin ki daman nake ji ba? Ai yau kin kawo kanki inda aka fi k’arfin ki.” Maimuna ta chakumi Ameena zata dake ta Ameena ta dage ta cillar da ita k’asa Asiya ma tayi baya ta fad’i goshin ta ya daki table ya fashe daga gefe.
Chapter 31 · 0% Book details