Sashe 6
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hajiya tace, "To Ina Jinka."
"Hajiya mai gidan bulon da nake aiki daman ai na fad’a miki kwanaki indai zai zo duba mu yaga ya muke aikin ni kawai yake samu wajan ko?."
"Eh ka fad’a min wannan."
"Yau ma yazo ya tarar dani ni kad’ai a wajan aikin, sai ya kira ni muka je babban company sa na sarrafa siminti tare dashi, yanzu ya mayar dani can yace yaga Ina mayar da hankali akan aiki sosai. Hajiya albashi duk wata dubu dari biyu yake bayarwa kin ga ma..." ya fad'a yana saka hannu aljihu ya fito da kud’in yace, "har ya bani na wannan watan wai tunda yayi tsakiya nazo nayi shirye-shiryen fara aiki a sabon waje" ya fad'a yana ajjiye kud’in a gaban Hajiya.
A tare suka had’a baki suka ce, "Alhamdulillah! Allah mai iko, Allah mai yadda taso.” Yaya Hadiza tace, "Kaga alkhairi lokaci d'aya, Allah ya rik’e maka Ibrahim yasa a fara a sa'a, Allah yasa shine madub'in arzukin ka." Ya amsa da amin Mariya tace, "Kai ai fitar Fiddausi daga rayuwar ka ai alkhairi ne, kwata-kwata yau kwana ta nawa da fita daga gidan ka har alkhairi ya same ka haka?. Sai tayi dani sani nan gaba wallahi Allah ya bamu rai da lafiya. Mai farar k'afa kawai."
Yaya tace, “mai farar k’afar gaske, watakila ma itace take daqile taurarin alkhairin sa, yanzu gashi tana fita ana samun cigaba.”
Ibrahim da yake jin su dariya yayi kawai dan yanzu basa son wanda zai ce ma yana son Fiddausi balle kuma so sota yace, "Babu mai farar k'afa fa a addinince, magana ce irin taku ta hausawa.” Hadiza tace, “eh babar d’an kace ai dole
Kace haka.” Yayi dariya mai sauti ya kalli Hajiya da take yi masa addu’ar samun nasara da dacewa yana amsawa da amin ya tashi ya fita ya bar kud’in a hannun hajiya yace ta ajjiye masa.
#Nana Haleema
#book2
Book2
004
Ameena tana gama shan tea din sama ta hau kamar kar ta yi hanyar saman sa sai kuma tabi hanyar saman da nufin gyara masa dakin, duk fad’a da masifar da zai mata bata iya yin banza sa gyaran d’akin sa sai ta gyara masa har ta saba ma. tana shiga ta zaunar da Zaytaun akan kujera ta fara gyara gadon kamar ko yaushe gefe d’aya ne zai tabbatar maka da mutum ya kwana a d’akin. A gefen bedside taga wayar sa na chaji a bayyane tace, "Mantawa yayi kenan." Bata je inda wayar take ba ta cigaba da gyara d’akin.
Kira ne yake ta shigowa cikin wayar bata kalla ba ta cigaba da abinda take yi har ta gama gyara d’akin tayi masa turaren wuta ta wanke band’aki, ta fito daga band’akin ta sake jin kira ya shigo sai ta ja ta tsaya tace, "maybe ko yana tunanin ya yar da wayar ne yake kira" ta fad'a tana nufar wajan a lokacin kiran ya katse taga number ce dai take ta kira. Wani kiran ne ya sake shigowa ba tare da tunanin komai ba ta d'auka ta saka a kunne kafin tayi magana akace, "my love Ina ta kira baka d’auka, Ina ka shiga yau baka kira ni ba nayi missing sweet voice din ka ba?.”
Dum dum zuciyar Ameena ta buga ta cire wayar daga kunnen ta sake kallan wayar taga number ce babu suna gaban ta na fad’uwa sosai jikin ta har rawa yake yi ta rasa me zatayi kashe wayar zatayi ko magana zatayi? Dakyar ta iya cewa, "ya manta wayar a gida" tana fad'a ta yanke kiran ta zube akan gado tana hakki zuciyar ta na bugawa duf duf duf, da sauri ta d’auki ruwan da yake gefen gadon tasha ta lumshe idanun ta saboda abinda take ji a zuciyar ta.
Ta jima a haka wayar na hannun ta kafin ta ajjiye ta a gefe ta kalli screen din wayar hoton Zaytun ya bayyana a kai tana dariya ta had’d’iye abu mai d'aci tana kulle idanun ta, dakyar ta iya jan numfashi ta ajjiye wayar a kan gadon ta tashi ta d’auki Zaytun ta rike hannu Zaytun da take ta kai kawo a d’akin suka fita. Tana sakkowa ‘kasan yana shigowa ganin ta ya saka yace, "Kinga wayata?". Kai ta d’aga alamun eh ya hau saman da sauri ita kuma ta zauna akan kujera.
Ba jimawa ya sakko ya fita daga falon fitar sa ba jimawa Rukayya ta shigo kana kallon fuskar ta kasan akwai damuwa sosai a kai dan idanun ta yayi ja sosai alamun tasha kuka, ga fuskar ta wajan kumatun ta shima yayi ja sosai abin ka da farar fata, bata yi mata magana ba har ta zauna sannan ta kalle ta tace, "Rukky me yake damun ki haka?." Sai kawai Rukayya ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ganin haka sai Ameena tayi shiru ta barta tayi kukan dan zata ji dad’i.
Ta jima tana kukan kafin ta tsagaita Ameena ta tashi ta dauk’o mata ruwa tace, "karb’i ki sha." Ba musu ta karb’a tasha ta ajjiye kofin tana sauke Ajiyar zuciya sosai itama ta zauna kusa da ita tana kallon ta. Rukayya ta tashi shiga bandaki ba tare da tace komai ba amma kallon ta kasan akwai abinda yake damun ta, Ameena ta bita da kallo dan tasan maganar bazata wuce guda d'aya ba.
A fusace taga ya shigo ta d’ago ta kalle shi kafin tayi magana tana yana bin ta da kallo sai tayi shiru ta kawar da kai dan tasan akwai abinda zai ce yace, "Waye ya baki izinin tab'a min waya?." Kafin ta samu damar magana ya sake yace, "Waye yace ki tab’a min waya!?." Yadda yayi tsawar sai da ta firgita Zaytun ta nutsu sosai kamar ita ake yiwa fad’an tana kallon sa.
"Ina ruwan ki da wanda yake min waya da zaki d’auka har ki fad'i maganganu mara dadi? Ke a ganin ki wannan shine kishin?, ki dauki waya kina zagin yarinya k'arama akan kawai zata auri mijin ki, waye ya fada miki har yanzu ana wannan shashancin? Waye ya fad’a miki ana wannan shirmen har yanzu?.”
Ameena bata ce komai ba ya nuna ta da yatsa yace, "Kin zubar da girman ki a idanun ta tun kafin ta shigo, in ma kina yi dan ki tsoratata akan kar ta aure ni kin yi a banza wallahi Ameena, aure babu fashi sai dai Kiyi duk abinda zakiyi, kuma wallahi aka sake min waya kika d’auka sai ranki yayi mugun b'aci, dan wallahi sai nayi miki abinda baki tab'a zato ba. a haka kamar baza kiyi ba ashe mage ce mai kwanciyar d’aukar rai, ke ga mai miji ko? Ki fad’a min me kike yiwa mijin naki har da zaki wata kiyi mata warning?."
In kujerun falon sun motsa itama ta motsa bata ce komai ba yaja tsaki yace, "Allah ya baki ikon sake tab'a min waya ki gani" yana fad’a ya juya zai fita suka had'a ido da Rukayya da take tsaye a bayan sa tana kallon sa cikin mamaki da tsoro dan duk abinda yace taji ta kuma gani. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya wuce ta ya fita fuskar sa a d'aure.
Ameena har lokacin kanta yana sunkuye bata d'ago ba Rukayy ta tako a hankali tazo kusa da ita ta dafa kafad'ar ta sai a lokacin hawaye ya zubo mata tayi saurin gogewa taja numfashi wani abu mai nauyi ya tsaya mata a tsakiyar kirjin ta sai sukar ta yake yi. Dukkan su shiru sukayi aka rasa mai magana Ameenatu ta kalli Zaytun da tsoron tsawar ya saka ta bacci a akan kujera tayi murmushi ta sake goge idanun ta har lokacin bata ce komai ba.
Ameenatu ta kalli Eukayya tace, "Muje sama." Tare suka mik’e Rukayya ta d’auki Zaytun sauka hau sama har cikin d’akin Ameenatou suka zauna a kan gado. A gefen bedside Rukayya taga maganin da yake ajjiye ta kalli Ameenatou ta sake kallon maganin tace, "Ameena maganin waye wannan? Amma dai ba naki bane ba ko?.” Ameena ta kalle ta batayi magana ba Ameena tayi murmushi tace, "Ke a ganin ki wannan tsawar da fad’an na iya yau ne? Hmmmm!."
Rukayya ta sake kallon maganin ta kalle tace, "Kin rame da yawa Ameenatu duk kin koma kamar ba ke ba." Murmushi Ameenatu tayi tace, "Kiris ya rage a d’auki gawata a gidan nan Rukayya, na gaji da zaman gidan nan na gaji Ruky!" Sai ta fashe da kuka sosai wanda ya tab’awa Rukayya zuciya itama ta fashe da kuka.
"Rukayya Jin dadin aure na wata hud’u zuwa biyar kawai nayi a gidan nan daga nan komai ya canja, Yusuf din da na sani a baya bashi bane ba yanzu, ya canja."
Kuka suke sosai dukka su biyun babu mai rarrashin wani duk kansu da dalilin yin kukan nasa, sun jima a haka kafin Ameenatu ta goge idanun ta ta kalli Rukayya tace, "Kema ki daina kukan ya isa haka, babu abinda kuka zai magana addu'a itace maganin mu. Ban d’auka kina da damuwa ba ganin ki a gidan nan ga mijin ki yana sonki ban d’auka akwai damuwar da zata saka ki zubar da hawaye ba Ameena.”
Rukayya ta sake cewa, "Ameenatu ban San inda zan saka raina a gidan mu ba, Umma kamar ba itace ta haife ni ba fad’an yau daban na gobe daban, Kullum kallo take nak’i aure tunda duk wanda ta kawo ban aure shi ba. Umma da ya kamata ta jani jikin ta ta rarrashe ni ita take min fada Ameenatou, su Zuhra duk sun Raina ni ban isa na saka su suyi ba sabida suna ganin kan mu daya dasu. Yau Umma ta bud'e baki tace ita ta gaji zata saka ayi cigiya a masallaci Wanda yace yana sona zata bada ni, Ameena wai nice nak’i aure ne? Meyasa Umma da mutanen Unguwa suka kasa gane lokaci ne baiyi ba?."