Sashe 15
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wato da yake yana so ya isar mata da gobe ma zasu zo sai gashi ya tako a k’afar sa har inda take wai tayi hak’uri tazo suje sama, murmushin takaici ta sake yi ta goge idanun ta har lokacin kallon inda ya fita take yi tana mamakin hali irin na Yusuf kafin ta sake rufe idanun ta ta cigaba da lazumi.
_In na koma gidan Yaya na d’ora mata nauyii duba da yanayin mijin ta bashi da hali sosai, bamu da gıda gidan mu an jima da rabo gado da me zai zaunar dani a gidan nan? Dan kawai Yaya Adam ba mazaunin kano bane aikin sa baya barın sa zama waje d’aya wallahi da gidan sa zan koma na gaji da zaman gidan nan gabad’aya ya fita daga raina, inda Ina da gata da Ina zan zauna? me zai zaunar dani a gidan nan?._ abinda take fad’a a zuciyar ta kenan tana ji kamar ta tashi ta fita daga gidan ta huta da abinda take ji.
Yaya Maimuna ta tasa Asiya a gaba suna tattaunawa akan Ameena tace, “Kin sanar dashi abinda nace kice?.” Asiya tace, “Na fad’a masa, naji kuma da alama bai ji dad’i ba.” Yaya Maimuna ta girgiza kai tace, “Yauwa haka nake so, yarinyar akwai kyau da haske ne dole sai Muna had’awa da makirci in ba haka ba akwai matsala wallahi. Dana ganta d’azu sai da gabana ya fad’i, amma kyaun ta ba wani abun bane a wajen mu.”
Asiya kamar zatayi kuka tace, “Yaya da gaske dai tana da kyau sosai ko? Na shiga uku.”
“Baki shiga uku ba Asiya, amma dan kyau fa tana da kyau ba zancen k’arya amma zamuyi maganin ta. Kyaun zai zama bashi da wani amfani kece dai a gaba.”
“Yanzu ya za’ayi?.”
“Na tabbata gobe zai saka ayi mana abinci; to a hakan ma baza mu kyale ta ba wallahi, sai Mun ‘kirkiri wani abun da sai ta zubar da hawaye. Ta wannan hanyar zamu dinga cusa masa yana ganin bata qaunar ki yadda da kin shiga gidan in ma wuk’a kika ce ta biyo ki da ita zata kashe ki zai amince.”
Asiya tace, “Ni jikina yayi sanyi da kika ce tana da kyau wallahi, bana so ta fini ta ko wanna bangare, yadda yafi sona so nake son ya tabbata har abada.” Yaya Maimuna tace, “Kar ki wani damu hakan shine zai tabbata, Ina zuwa” ta fad’a tana fita daga d’akin ta barta ita kadai a zaune.
Umma ce ta shigo ta same ta a haka ta kalle ta tace, “ke kuma Lafiya?.” Asiya ta kalle ta tace, “Umma tunda Yaya Maimuna ta fad’a min kyaun matar sa nake Jin zuciyata na zafi wallahi.” Umma tayi dariya tace, “Yaro man kaza, to meye amfanin kyaun babu mai yabawa?.” Asiya tace, “Umma bana so ko kad’an ta fini a wajan sa ne wallahi.”
“Ke bud’e ido ki kalle ni, yadda nake a gidan nan na kafa kaina dangin mahaifin ku ma tsorona suke ji haka kema zaki kafa gwamnati a gidan Yusuf, kar ki damu kyau na banza ne tunda babu soyayya, kina dani kina da Umman ki Sakina ko babu ni zata tsaya wajan ganin kin kasance ta gaban Gashi balle gani gata. Kar wannan ya dame ki kyau na banza da wofi ne tunda babu soyayya bashi da amfani.”
Asiya tayi murmushi tace, “Har naji dad’i Umma” ta fad’a tana tasowa tana rungume Umma. Umma tayi dariya ta dake ta a baya tace, “Ai ba irin su Yusuf ake yiwa rik’o wasa ba, gam zamu kama shi ta yadda bai isa ya kwace ba wallahi. Kedai kije ki cigaba da shirye-shiryen ki mu namu shirin ya jima da yin nisa.” A guje Asiya ta fita zuciyar ta fari kal dan babban burin ta ace yau tafi Ameena a gidan Yusuf, ko kusa ko alama bata so Ameena ta fita wani abun ko ya ya yake kuwa.
#Nana Haleema
#Book2
#paid
#500
Book2
010
Saboda gudun ya ‘bata mata rai ga Amira a gidan ya saka tun safe ta saka Ameera ta saka Amira ta d’ora musu abinci a babbar tukunya aka yi musu shinkafa jellof mai rai da lafiya wacce taji nama a ciki aka juye a babban kula aka ajjiye plates da cokula a kai. Sai bayan Amira ta gama komai sannan ta sakko sabida ciwon kai ta kalli Amira tace, “Sannu da aiki” ta fad’a tana bud’e abincin taga abincin yayi kyau sai khamshi yake yi ta d’auki cokali guda daya ta d’iba taci ta girgiza kai tace, “Gaskiya yayi dad’i sosai, kin sha aiki.”
Amira tace, “Ai ba wani yawa, me zan dafa mana mu?.” Ameena tace, A’a aikin yayi miki yawa, kawai ki d’iba kici Zaytun tasha custard.” Sai kuma ta kalle ta tace, “Amma in bakaya son shinkafar ki dafa abinda kike so nidai bana ci” ta fad’a tana fita daga kitchen d’in.
Bata jima da zama a falon ba ta fara ji ana shigowa gidan daman tasan sune basu shigo kamar jiya ba ta aika Amira ta kai abincin ta dawo suka zauna suna kallon tv badan Ameena na fahimtar abinda ake yi a cikin tv din ba sai dan bata son zama tana tunani ne shiyasa. Sai azahar ta tashi ta hau sama Amira ma ta tashi da niyar yin sallah.
Haka aka cigaba da shirin biki dangin amarya sun gama kafi a gidan amarya gabad’aya daman abubuwa kad’an suka zuba sauran kaya ango ne ya zuba da kansa. Ameena koda wasa bata yin hanyar apartment din ko fita zatayi bata kallon wajan mota take hawa ta fita bata ma sha’awar kallon sa balle ma ta shiga. Zaman Amira ya saka taji dad’i sosai suna hira tana debe mata kewa safe da dare.
B’angaren Amarya ana ta shagali sun gabatar da ‘kananun event sun shirya dinner wacce za’ayi bayan an d’aura aure daga nan amarya da ango zasu wuce gidan su shiyasa tun kafin ranar dinner din ake ta kawo mutane gidan suna gani dan babu kai amarya. Ranar d’aurin auren Ameeana tana tare da k’awayen ta sai Amira sai kuma Yayar Yusuf da Humaira da suka zo basu jima ba su suka tafi aka bar ta da k’awayen ta suna hira dan d’ebe kewa.
Ameena da take ta kallon Fiddausi itama ita ta kalla tace, “Sai wani kallona kike yi kamar na canja miki, ke naga alama ko a jikin ki ace yau d’aurin auren mijin ki kina zaune baki da ko wacce damuwa. Ko da yake inda kud’i wallahi ba’a wani kishi.” Ameena tayi dariya tace, “Gani nayi sai kyau kike sake yi kina haske meye sirrin?.”
Tayi shewa tace, “Ke kin raina zawarci ne? Wallahi dad’i ne dashi ba kad’an ba.”
Zakiyya tace, “Ke naki zawarcin ma ai mai dadi ne, kwanaki kad’an fa ya rage kiyi aure.”
Ameena da mamaki tace, “Har an samu wani kenan?.” Zakiyya tace, “Alhaji Bello Sagagi shine ya haukace a akanta, ke badan Abban su bama ai da yanzu tana gidan sa tunda babu idda akan ta.” Ameena tace, “Wai Bello Sagagi dai dana ke Jin labari?.” Fiddausi tayi farrr da ido tace, “Shifa.” Ameena ta girgiza kai tace, “Amma shine babu labari sai yanzu? Ruky kin sani?.” Rukayya ya tab’e baki kawai bata ce komai ba Fiddausi tace, “nayi niyar sanar daku nasan hali ne yanzu zaku fara cemin ai bai dace ba shiyasa na share ku.” Ameeena tace, “amma ni kodan saboda Amir wallahi nafi son ki koma gidan İbrahim.”
Fiddausi ta wara ido tace, “a’uzubillahi minal shaid’ar rajim! Haba Ameena wannan wanne irin fata ne?. Dan Allah zubar da bak’in yawu.” Ameena ta kalli Rukayya da bata ce komai ba tunda aka fara maganar ta sake kallon Fiddausi tace, “Wannan korar shaidan haka kamar na kira sunan wani k’Aton aljanin?.”
Zakiyya tace, “Ba gwara ki kira aljani da ki kira İbrahim ba?, ke ana zancen cigaba kina so ki mayar da rayuwar ta baya, ai tafi k’arfin Ibrahim yanzu wallahi.”
Rukayya tayi dariya tace, “Ameena na fad’a miki bakin Fidy da Kiyya d’aya wallahi. Ko me d’aya zata aikata d’aya ta sani, duk wannan abinda ya faru shirin su ne, hatta fitowr ta daga gidsn Ibrahim zan iya cewa su suka shirya.” Fiddausi tayi dariya tace, “Ke ai iriin zuciyar Ameena gare ki shiyasa bana sabga dske yanzu zaki fara cemin Allah yace annabi yace, ke mai zuciyar auren talaka ga Ameena nan ta auri mai kud’i ta barki da zuciyar har yanzu. wallahi ki yiwa kanki fad’a akan son talakawan nan baki san illar su bane.” Ameena tace, “Wani talakan yafi mai kud’in ai, wallahi Rukayya da ki samu wani mai kud’in gwara ki samu wani talakan mai rufin asiri da zai kula dake. Meye amfanin kud’i in babu kwanciyar hankali wai?.”
Zakiyya tayi caraf tace, “Wallahi cutar ki take Rukayya, babu wannan zancen. Ko a addini mai kud’i yafi talaka, mai kud’i ne yake zakka da zuwa aikin hajji talaka fa?.” Fiddausi tace, “Wai taya talaka zaifi mai kud’i wani kwanciyar hankali? Kud’i fa sune kwanciyar hankali ba wani abun ba. Wallahi kudi ko ba naki bane aka baki ajjiye dad’i ne dasu balle ace naki ne. Ke ko kallon wannan gidan naki ma ace kece a ciki shi kad’ai ya ishe ka farin ciki balle ga komai an ajjiye maka. Wallahi Rukayya ki neme mai kud’i domin a wannan zamanin kud’i sune komai, in kana auren mai kud’i a gidan ku ma anfi ji dakai dan ni naga izina a kaina.”
Rukayya ta tab’e baki tace, “Ni duka basa gabana, Allah dai ya zab’a abinda yafi alkhairi, in mai kud’in ne alkhairi Allah ya kawo shi, in talakan ne ma Allah ya kawo shi.” Fiddausi ta Harare ta tace, “Baki da hankali wallahi, ke in ana zancen alkhairi ma sai ki sako lamarin talaka a ciki? Ai duk inda mai kud’i yake wallahi shine alkhairi.” Ameenatu tayi murmushi kawai gaban ta yana fad’uwa dan zuwa wannan lokacin ta tabbatar an d’aura auren mijin ta sa wata.