Sashe 2
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba ya kashe wayar yace, “In kina da buk’atar wani abun ki fad’a.” Sai a sannan ta juyo ya kalle shi da mamaki tace, “Kamar me?.” Ya d’age gira sama fuskar sa a washe yace, “Kamar abinda nake nufi wanda yake zuciyar ki yake hana ki bacci.” D’an jimmm tayi alamun tunani ta girgiza kai tace, “Ban gane ba.”
Dariyar rainin hankali yayi yace, “Karya kike Ameena kin gane, is better for you ki fito kiyi magana kar kiga nayi magana ki d’auka wai ni nake so” ya girgiza kai kafin yace, “sam babu wannan a zuciyata, kawai dai nayi miki tayi ne kar azo ana cewa ai ga zance ga magana. Daman kuma Wanda yake buk’atar abu shine yake zuwa ya nema in ya samu daman haka yake so in bai samu ba kuma yayi hak’uri, ki gwada yanzu watakila Ina cikin farin cikin da hakan zai saka na amince miki.” Ya hard’e hannayen sa yace, “A rashin tayi ake barin arha Ameenatou.”
Yadda yake maganar yana murmushi sai take kallon sa itama tayi murmushi kamar yadda yake yi tace, “To ai ni ban ma fahimci inda zancen ya saka gaba ba balle ma nayi abinda kace.”
“Da gaske?.”
Kai ta d’aga alamun eh yayi murmushi yace, “shikenan jeki, da alama kin barwa amarya.”
Ameena tayi dariya kad’an tace, “Daman ita take da bukata, mu kam ya ishe mu” ta fad’a tana niyar barın d’akin taji yace, “İn ma zuga ki ake kike mayar min da magana haka cutar ki ake yi, ki koma yadda kike a baya yafi dacewa dake wannan sabon salon bazai haifar miki da d’a mai ido ba.”
“Sai da safe” ta furta a taqaice ta fita tare da ja masa k’ofar. Iska ya fesar ya naushi iska ya daki goshin sa dan shi Sam ba haka yaso ba, yana buk’atar tane a lokacin ya d’auka zata amshi tayin sa shiyasa yayi mata haka. Ya mike tsaye a bayyane yace, “Yaushe kika koma haka ne Ameena? Ina tarin soyayyar da kike min ya tafi…?” Ya fad’a yana yin ball da jarkar ruwan da take gaban sa ya juya ya shiga band’aki.
Ameena d’aki ta wuce ta kwantar da Zaytun ta tsaya jikin window tana mayar da numfashi kamar wacce tayi gudu zuciyar ta na harbawa a guje marar ta na d’aurewa. Tabbas a matuqar buqace take da mijin ta, yadda yayi amfani da kalamai na ko in kula a kanta ya saka taji baza ta iya kasancewa dashi ba gwara ta zauna a haka koda zata cutu
Kuka ta fashe dashi sosai mai sauti zuciyar ta nayi mata ciwo ga yadda kanta yake sarawa har biyu-biyu take gani. Ta jima tana kuka kafin ta duba agogo taga karfe goma na dare har ta wuce ta d’auki wayar ta tare da kiran likitan da take gani.
Sai bayan wayar ta shiga kuma sai tayi tunanin kar fa tana gıda bata ne aiki ba amma kafin ta katse har ta d’auka dole tayi sallama ta amsa mata kafin tace, “I’m sorry Dr na Kira ki da daddare.” Daga can b’angaren tace, “Ahh babu damuwa daman Ina on duty ne ai yanzu, Lafiya dai ko?.”
“Ciwon kan ne dai har yanzu nake fama dashi Dr, ga jiri da yake d’auka ta sometimes sai na zauna na huta ko tafiya nake yi, ciwon marar nan ma yana damuna.”
Dr tace, “Ciwon kai da jirin da kike ji watakila jinin ki ne ya sake hawa ki shigo gobe da safe mu auna bp din, ciwo Mara kuma na fad’a miki matsalar ki bai kamata ki dinga sakaci ba, kina da aure ba baki da aure ba, bai kamata hakan ta dinga kasancewa dake ba.”
“Mijin nawa baya nan ne Dr shiyasa.”
“Ai fad’a masa zaki yi duk inda zai tafi ya dinga tafiya dake ai hakkin kine, in kuma hakan bazai yu ba ya dinga takaita tafiyar dan kina cutuwa hakkin kuma a wuyan sa yake Ameena. amma tunda yanzu baya nan ki sha ruwan zafi kar ki saka sugar zallar ruwa mai dumi zaki sha ki d’an tattaka kamar taku Arab’ın haka sai ki sha p.c.m ki kwanta.”
Ameena tace, “in sha Allah, na gode sai nazo.” Daga nan suka sallama ta kashe ita kuma ta tashi tayi abinda tace mata cikin ikon Allah ta samu ta dan ji daidai ta kwanta kusa da y’arta bacci ya d’auke ta.
…….A asibiti ta bud’e ido ta ganta hannun ta sanye da ledar ruwa gefe d’aya ga Mama ta ga kuma Zakiyya ga Yayar ta a zaune suna kallon gadon da take kwance suna magana. Muryar Yayar ta taji tana cewa, “Ai yayi mata wulakanci wallahi, ki duba yadda ya fasa mata baki fa dan Allah, ta nemi saki suka zo suka bada hak’uri aka hak’ura ta koma shine kuma ya sake mata dukan da cikin jikin t sai da ya fita, me ake da auren talaka irin Ibrahim?. Ashe duk yabon nasa da ake yi duk na banza ne tunda ga abinda ya faru a k’arshe.”
Zakiyya tace, “Ai Yaya ta jima tana fad’a min damuwar ta akan Ibrahim kawai dai bata fad’a ne a gida, tace bata tab’a kawo k’ara gıda ba amma tasan in ta kawo Abba bazai amince ba gani zaiyi karya take yi. Tazo tayi min kuka na rarrashe ta na bata hak’uri ta koma duk bai gani ba sai da ya yi mata wulakanci. Ai gwara zaman nasu da yazo k’arshe naji dad’in hakan wallahi.”
Yaya tayi kwafa tace, “Ai badan wani abun ba ko wallahi sai na saka an kama shi ya kwana a cell dan yasan kanwata ya tab’a, to Amir nake kallo ko babu komai ya had’a mu amma da shi din banza da wofi. Ya sake ta kuma yayi mata dukan da cikin ta ya zube Kaga ya hutar da ita idda ko gobe aure zatayi ta wuce takaici. Gwara ma da cikin ya zube ai kowa ma ya huta.”
Mama ta girgiza kai tace, “Bai kyauta ba gaskiya wallahi, kuma ko waya har yanzu babu wanda yayi daga gidan su, ta inda aka hau ai ta nan ake sauka da sai su kira Abban ku ya fad’a masa komai. Ya bani mamaki sosai ban d’auka zai aikata haka ba, ina yabon sa sallah sai gashi ya kasa alwala.”
Zakiyya tace, “Bar talaka Mama, ai bai san halacci bane shiyasa. Duk soyayyar da ta nuna masa yana malamin islamiyya amma shine zai mata wannan rashin mutuncin, yanzu fa aikin d’aukar bulo suke yi ta daure ta zauna dashi, abinci ma gararta yake wani lokacin, dan Baku san komai bane wallahi Mama da ko kallon sa baza ku sake yi ba. Ta rufa masa asiri sosai dan matar rufin asiri ce amma duk bai gani ba. ko da yake ai kansa ya yiwa samun mace kamar ta ai sai dai a mafarki.”
“Washhh!” Ta furta bayan ta gama jin dukkan maganganun su ta mik’e ta jingina da bayan gadon Yaya tace, “Kiyi a hankali an yi miki wankin ciki ne fa.” Cize baki take yi har ta mik’e zaune ta kalli Yayan tace, “Ina Jin kwari ai, har gari ya waye ne?.”
Mama tace, “eh, kwana muka yi a nan.”
“Ikon Allah ban ma san ina nan ba” ta fad’a tana cize bakin ta kafin ta kalli Yaya tace, “Yaya naji kince wankin ciki.”
Yaya tace, “Eh, dukan da yayi miki ya saka cikin ya zube bayan ya sake ki, ke ki gode Allah ma kin huta idda.”
“Amma Yaya Ina son cikin” ta fada kamar zatayi kuka tana kallon Yaya, Yaya ta fusata tace, “Sai kije ya sake yi miki wani ai, banza wacce bata san kanta ba.”
Shiru tayi bata amsa ba nan kuwa zuciyar ta fess take kamar ta taka rawa haka take ji ta kalli Zakiyya tace, “Zan yi fitsari.” Zakiyya ta taimaka mata ta tashi tace, “muje na raka ki.” A hankali suke takawa suna magana har bandaki k’asa-k’asa Fiddausi tace, “Ke an ina aka samo labarin yayi min dukan da ciki ya fita bayan ke kin san magani nasha?.” Zakiyya tace, “Banza duk plan d’ina ne, kedai ki daure ki warware mu koma gida a d’ora daga inda aka tsaya. Ai labari yazo karshe sai dai mu ce the end!.”
Dariya tayi kad’an kafin ta shiga bandakin bata jima ba ta fito tasha tea din da Yaya ta kawowa Mama sosai taji dadin jikin ta likita yazo ya basu sallama suka tarkata suka koma gida.
Book2
002
Ameena kuwa koda ta tashi bata iya yin komai ba har safiya kanta ciwo yake yi Zaytun ma yar aikin ta ta bawa ita ta yi mata wanka ta shirya ta ita kuma ta samu tayi wanka ta saka dogon hijjabi ta fito a falo ta had’u dashi yana amsa waya ta tsaya daga gefe tana kallon sa har ya gama kafin tace, "Ina kwana." Kallon sama da ‘kasa yayi mata dan kwana yayi yana jin haushin ta akan abinda tayi masa kafin yace, "Sai Ina?."
"Zanje asibiti ne wajan Dr Mansura."
"Sai kin dawo" yana fad’a ya wuce ya sauka ba tare da ya tambaye ta abinda ya same ta ko me zai kaita asibitin ba. Jingina tayi da bango ta lumshe ido zuciyar ta nayi mata k'una sosai ta sauke numfashi ta bud’e idanun ta sakko itama. Bata same shi a falon ba sai mai aikin ta d’auke da Zaytun tana bata abinci tayi murmushi tace, "Sannu da aiki."
"Yauwa sannu da fitowa Hajiya, ya ciwon kan?."
"Gashi dai Ina fama, asibiti ma zanje yanzu".
"Allah ya k’ara Lafiya."
Ameena tace, "Amin. Da Zata zauna ma ai dana je na dawo tana wajan ki." Tyi dariya tace, "Tunda kika sakko ta daina cin abincin tana kallon ki, ai baza ta zauna ba." Dariya tayi kad’an ta karb’e ta ta tsayar da ita tare da rike hannun ta suna takawa a hankali har wajan motar ta.