Sashe 28
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fita tayi baya ta zauna kamar mahaukaciya sai kuma ta zubara ta mik'e tsaye ta fita daga d’akin zuwa nata d’akin ta d’auki waya hannun ta har rawa yake yi ta kira layin Yaya Maimuna bata d’auka ba ta cillar da wayar gabad’aya wani iri take ji a zuciyar ta kamar zata fito saboda bak’in cikin abinda yace mata.
K'arar wayar ce ta saka ta koma wajan da sauri ta d’auka ganin Yaya Maimuna ce take waya ya saka ta dauka ta saka a kunne daga can b’angaren tace, "Asiya ya akayi?."
"Yaya na shiga uku." Jin abinda tace sai Maimunatu tace, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, meye ya faru?."
Asiya tace, "Yaya Yusuf ne." Maimuna hankalin ta ya sake tashi tace, "Meya faru da Yusuf din? Wani abun yayi miki?." Asiya kamar tana gaban ta ta girgiza kai tace, "Yaya yau kwata-kwata sati na uku nake a gidan nan amma yau shine yake bud'e baki yake cemin wai yana son matar sa, Yaya ko mararina bayayi yana tashi da safe zai fita ya koma b’angaren ta kamar ba amarya ba. Ni wallahi ba haka nake so ba Yaya bana so ya dinga sauraron ta kuyi wani abun dan Allah."
Maimuna da take jin ta tace, "Dallah Malama ki yi min shiru kin saka gabana ya fadi na d’auka wani abun ne ya faru wallahi. An fad’a miki ana kan shirya miki wani babban shiri da zata fita ta bar miki gidan gabad’aya, ki kwantar sa hankalin ki ki daina nuna masa damuwa akan hakan in ba haka ba zai yi saurin gano ki.” Asiya tace, "Yanzu haka fa ya tafi wajan ta ko karyawa baiyi a wajena ba, abinda nake so na zama itace ta zama a yanzu Yaya."
"Ki kwantar da hankalin ki, rashin cin abincin ki wannan laifin kine kuma ai, kina nan kina fama da wannan shegiyar k'azantar ba dole ya dinga barin wajan ki da wuri ba?. Momi ta fad’a min ko turaren wuta bakya yiwa gidan ki zauna kaca-kaca gida ma haka ba dole ya tafi ba?. Ki daure ki gyara kanki mu kuma zamu gyara miki zaman ki, wallahi sai yarinyar ta fita ta bar miki gidan ki domin Yusuf naki ne kawai." Sai a sannan tayi Ajiyar zuciya tace, "Naji dadin hakan Yaya, zan gyara kuma in sha Alla. Ni yawan wanka ne damuna yake amma zan gyara.”
"Yauwa, ki gyara kanki kar kuma ki sake ko da wasa ki k’ara yi masa magana a kanta ki dinga nuna ke sonta kike yi ba wani abun ba kin gane?."
"To Yaya Ina yi."
"Ki sake, ni kuma zan shirya miki abinda za'a yi ki jira ki gani" tana fad'a ta yanke wayar ta sauke Ajiyar zuciya ta ajjiye wayar ta fita daga dakin zuwa k'asa.
Yusuf kuwa ko da ya shiga b’angaren Ameena sai da ya lumshe ido kamar ko yaushe khamshi kawai falon yake wanda ya zama dauwamamme a falon ko yaushe khamshi d'aya yake yi koda bata turara shi ba khamshin yana nan. Sakkowa take yi ita da Zaytun suna ta dariya tana yi mata wasa kafin Zaytun tace, "Mummy Ina daddy?." Zata bata amsa taji yace, "Ga daddy nan." Sai kuwa ta fizge rik’on da Ameena tayi mata ta k’araso a guje wajan sa ya d'auke ta yana mata wasa tana dariya shima haka.
Kallon Ameena yayi bayan sun gama dariyar ya ganta a tsaye tana had’a tea a kofi kafin yaga ta d’auka tana sha, had'a ido sukayi sai ta sauke kofin a bakin ta tace, "Ina kwana." Fuskar ta ba yabo babu fallasa haka tayi maganar, kai tsaye baza kace fushi take ba sannan baza kace farin ciki take yi ba, shi kuma kallon ta yake tayi kyau da haske a idanun sa amma ramar da yake gani tana nan har lokacin. Dakyar ya iya cewa, "ya kuka tashi?."
"Alhamdulillah" ta bashi amsa a takaice.
"Ki fad’a min meye yake damun ki kike ramewa haka Ameena." Ta kalle shi tayi murmushi Tce, "Babu komai na fad’a daman a haka nake baka kula ne sai yanzu. zanje gidan su Fiddausi yau ake d'aura mata aure." Yace, "Fiddausi ba tana da aure ba?."
"Eh tana dashi a da, yanzu babu sabon aure zatayi."
"Allah sarki Allah ya sanya alkhairi, sai kin dawo."
Ta kalli zaitun tace, "Zo kici abinci." Ta nok'e kafad'a tace, "Da daddy zanci." Ameena bata sake cewa komai ba ya zauna akan kujera yace, "bani abincin na bata." Bata mu sa ba ta bashi tea din da dankali ya karb'a yana bata ita kuma ta hau sama ta bar shi a wajan. Ba jimawa suka sakko ita da Amira lokacin ta gama ci tace, "Zaytun muje?." Ganin Unguwa za'a tafi ya saka ta sakko daga jikin Yusuf ta tafi wajan Ameena.
Amira tace, "Daddy Ina kwana." Ya kalle ta yace, "Lafiya lau Amira." Jan hannun Zaytun tayi suka fita bayan sun fita ya kalli Ameena yace, "kije Ina nan basai kin kulle ba." Bata ce komai ba ta juya zata fita sai kuma ta tsaya tana tunanin kar da Asiya tazo tayi mata wani abun a cikin gidan, kamar zata ce wani abu sai yaga ga fasa ta fita yana zaune taji tashin motar ta alamun ta fita.
Da sauri ya tashi ya k’arasa dining yana bud’e abinda ya gani a ajjiye nan ya zauna yana ci dan yunwa yake ji amma baya son cin abincin Asiya saboda karni yake ji yana yi. Sai da yaci ya koshi ya tashi ya hau sama dan yayi wanka.
A gidan su Fiddausi a nan ta tarar da suka k’awayen ta suna daki ana hira shigar ta ya saka su yin ihu gabad'aya sai tayi dariya tace, "ana yi babu ni kenan ko?" Ta fada tana k’arasowa ta zauna duk suka bita da kallo. Zakiyya tace, "Ameena wai kishiyar nan da aka yi miki ce ta saka kika fige haka? Wai kina kallon kanki kuwa?."
Ameena tayi murmushi tace, "Wallahi sai na kwana na tashi ban tuna da ita ba, ni kaina ban San me yake saka ni rama ba." Fiddausi tace, "Gaskiya dai kin rame wallahi, da in sun fad’a ma bana gani amma yanzu na gani." Ameena tayi dariya kadan tace, "Ke ku share kawai, sai muka ji batun aure kwatsam daman Kun San da labarin ne?." Rukayya tace, "Bari kedai, jira muke kawai lokacin daurin aure yayi a daura kawai."
Ameena tace, "Amma kin yi sa'a Fidy yadda ake zaman zawarci yanzu ke kin samu miji da wuri, a hakan ma fa dan kin jira kwanakin idda ne da yanzu ma watakila kina da ciki." Sukayi dariya Zakiyya tace, "Ina Zaytun ne?." Ameena tace, "Tana wajan Amira suna falon Mama."
Rukayya tace, "Amma bawai zan dawo da abinda ya wuce bane, har ga Allah nafi so ta komawa Ibrahim tsohon mijin ta, a jikina nake ji bazata samu abinda ta samu a wajan sa ba.” Dogon tsaki Fiddausi tayi tace, "ana abin arzuk'i zaki saka raina ya b’aci wallahi, yanzu dan Allah ke aka ce na komawa Ibrahim sai ki amince?."
Ameena tace, "to meye dan kin koma?." Fiddausi tace, "Har abada nida shi wallahi sai dai mu had’u a hanya na bashi sadakar na abinci, na barwa Rukayya in tana so." Zakiyya tace, "wai meye haka kike yi ne Fiddausi?, ya zaki dinga kin bar mata hakan fa babu dad’i.” Fiddausi tace, "to itace ta damu da lamarin sa ko yaushe sai tayi min maganar sa, ni wallahi dan yana son ta ya aure ta ko a jikina murna ma zanyi domin nasan Amir ya samu uwa wacce zata iya fina kula dashi. Talaka take son aure ai kinga Ibrahim din shine daidai ita."
Ameena tace, "ai gaskiya take fad’a miki badan wai zata aure shi ba.”
"Dan fa ta aure shi wallahi ba wani abun bane, tana son talaka kuma shi talaka ne basai su zauna ba." Rukayya tace, "dan Ina fad’a miki gaskiya ai ba hakan yana nufin zan aure shi bane, kawai dai ni gani nake baza ki sake samun miji kamar sa bane. Ki daina had’a ni dashi tunda bakya so Allah ya baki wannan kike so sai ki gode masa.”
Fiddausi tayi saurin dakatar da ita tace, "daina yi min baki na samu wanda ya fishi in sha Allah. Godiya cikin yin ta nake ko da yaushe Alhamdulillah. Ameena tace, "Shikenan dai a yanzu kin samu wanda yafi Ibrahim Allah ya bada zaman lafiya, ke kuma Ruky Allah ya kawo miki na gari kema ki huta." Suka amsa da amin suka cigaba da hira har lokacin sallah yayi. Bayan sun idar da sallah ne Zakiyya take cewa, “yanzu na saka Surayya halin yau tayi miki had’in kaza ta musamman, gobe za’a kawo sai ki cinye Tass.”
Ameena tace, “Gaskiya matar nan maganin ta yana dakyau sosai, Tunda kika had’a ni da ita na daina Shan ko wanne maganin sanyi sai nata. Kin San bayan haihuwar Zaytun infection yaso yayi min karfi a jikina shine ai nake fada miki kika bani maganin ina sha na dinga fitsarin sa kamar hauka. Kai naji dadin sa wallahi sosai.”
Zakiyya tace, “had’in da tayi miki na bayan haihuwa fa? Shi me zaki ce a kansa?.” Ameena tayi dariya tace, “shima karshe sosai fa, na fad’a miki gaskiya kayan ta suna da kyau.” Fiddausi da take jin su tace, “bani lambar ta bazai yu ku dinga hira ina ji ni ban Santa ba, maza bani nayi saving a waya Tunda tana kaiwa ko ina daga nan a dinga kai min Abuja.” Rukayya tace, “inye kaga y’an Abuja.”
Sukayi dariya Zakiyya tace, “080.” Fiddausi ta maimaita tana sakawa a wayar ta, Zakiyya t sake duba waya tace, “08032773332.” Fiddausi ta saka lambar nan a wayar ta tace, “Yanzu naji batu ai, a wajan ta zamu had’a kaya kafin na tare in sha Allah.” Sukayi dariya aka cigaba da hira.
A wannan lokacin Alhaji bello yake mata waya ya sanar da ita an d’aura auren su, ihu Fiddausi tayi ta rungume Zakiyya da take kusa da ita ana murna kafin a ci abinci ana cigaba da hirar yadda komai zai kasance.