← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 42

Sashe 22

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace, “Wayyo Allah! Yanzu kenan kud’in da k’afar su suka fita ko sark’ar da k’afar ta ta tafi?.”
“Amma d’azu ai Asiya ta shigo d’akin nan ka tamabaya kaji ko ta ganta.” Wara ido yayi yana kallon ta cikin mamaki yace, “ohh na gane, kenan dan ta shigo d’akin nan na wasu sakanni kawai shine har taga sak’ar da kudin da ke kika san inda suke kuma ta d’auka?, ina tasan inda suke? Ina tasan aka ajjiye?. Kenan ita kike so ki d’orawa bayan a wajan ki aka nema aka rasa….?!.”

#Nana Haleema
#Book2
#Mai Daki
#Paid
#500.

Book2
014

Kallon sa take yi cikin k’unar rai da zallar takaicin a zuciyar ta nan da nan ranta ya baci hakan ya bayyana a kan fuskar ta tace, “Ni kake cewa nayi maka sata? Ni Ameeena nice na d’aukar maka sark’a kuma nice na satar maka kudi?.” Yadda take kallon sa take magana sai ya d’an ja baya yace, “To nida waye a gidan in bake ba? Yaushe na dawo gidan nan? Ita wacce kike maganar bata tab’a shigowa gidan nan ba sai d’azu har ta Ina tasan inda ake ajjiye kud’i da zata d’auka?.”

Ameena ta girgiza idanun ta sukayi ja ta hana hawaye sauka tace, “Ban tab’a yi min abinda bazan manta dashi ba a duniya kamar abinda kace min yau, ni ka kalla ka cewa nayi maka sata duk tarin ajiyar da kake bani ban tab’a dauka ba sai wannan karon, me kud’in zasu yi min in na d’auka? Me zanyi ma dasu da satar maka sark’ar gold?. Ni ba b’arauniya bace kai ka sani, banga abinda zaka ajjiye na dauka ba Yusuf, koda duniyar nan zaka ajjiye bata ishe ni kallo ba dan ko wanda ya ajjiye din baya gabana balle kuma dukiyar sa. Kaje ka nemi wacce tayi maka sata amma ba Ameena ba.” Kallon ta yake itama tana kallon sa tana ja baya ta juya zata fita Zaytun da take zaune tana kallon su kamar tasan abinda suke yi ta fashe da kuka ta biyo bayan ta ta d’auke ta suka sauka daga saman da sauri.

D’akin ta shiga ta kalli Amira da take zaune tana danna waya tace, “Amira tashi ki saka hijjabin ki yau bazan kwana a cikin gidan nan ba” ta fad’a tana ajjiye Zaytun ta d’auki key din mota da wayar ta ta saka hijjabi. Amira ta mik’e tsaye tace, “Aunty Ina zamu je? K’arfe goma na dare fa.” Bata yi mata magana ba ta fita daga d’akin dole ta saka hijjabin ta d’auki wayar ta da Zaytun ta biyo bayan ta.

Mota ta bud’e ta shiga mazaunin driver Amira duk tsoro ya cika mata zuciya Allah yasa kar tace bauchi zasu tafi a daren nan ta shiga itama Ameena taja motar mai gadi ganin an kunna mota ya saka ya bud’e musu gate suka fita.

Tuk’i kawai take ba tare da tasan inda zata je ba sai a lokacin ne ta fara kuka, Amira ta kalle ta tace, “Mummy babu inda zamu je sai Bauchi kuma dare yayi.” Shiru tayi bata ce komai ba kawai tuk’a motar take yi jin zuciyar ta take in akace ta kwana a gidan Yusuf zata iya mutuwa saboda b’acin rai da take ciki a wannan lokacin.

Waje ta samu a gefen titi ta faka kawai ta kifa kanta a kan sitiyarin motar ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, kuka take sosai da iyakar k’arfin ta dan bata da abinda zatayi da ya wuce kukan a wannan lokacin. Amira ma hawaye ta fara sharewa dan ta tabbatar abinda Yusuf yayi mata ba k’arami bane tunda gashi tayi abinda bata tab’a yi ba.

Kwankwasa glass din gefen Amira ake yi Amira ta kalli matar ganin ta santa sai ta sauke glass din tana gama saukewa matar tace, “na fad’a maka motar Ameenan Yusuf ce gata a ciki” ta fad’a tana kallon wani daga gefe ya k’araso yana fad’in, “Ameena! A wannan Daren?.” Kallon Amira yayi da Ameena da ta kifa kanta har lokacin kuka take bata d’ago ya kalli Amira yace, “Me ya fito daku a wannan daren haka?, ina Yusuf?.” Amira tasan Yayan Yusuf ne hakan ya saka tace, “Ban sani ba, Nidai kawai tace min na tashi mu tafi bazata kwana a gidan ba. Mun fito kuma ta rasa inda zata je shine muka tsaya a nan tana kuka.”

Ya d’auko waya yace, “Bara na kira Yusuf din naji wanne rashin hankali ne zai saka ya barku ki fito ku kad’ai a daren nan.” Matar sa tace, “A’a kar ka kıra shi, tunda kaji hakan akwai wani abun. Zan shiga motar naja yanzu muje gıda ta kwana a can da safe sai ka kira shi zuwa lokacin ta wuce yanzu kiran bashi da amfani.” Ya girgiza kai alamun gamsuwa ta k’arasa inda Ameena take ta d’ago ta har lokacin idanun Ameena a kulle suke tana hawaye tace, “yi hak’uri Ameena, shiga baya zan ja motar mu k’arasa gida.”

Kamar Ameena bata ji ba bata motsa ba ta sake cewa, “yi hakuri ki fito muje.” A hankali ta fito ta bud’e mata baya ta shiga ita kuma ta shiga gaban ta kunna motar taja zuwa gidan ta.

A kan idanun Asiya Ameena ta fit adaga gidan ana kulle gate din ta kalli Momi da yake gefen ta sukayi dariya tare da tafawa, Momi tace, “Amma Asiya ke shaidan ce wallahi, sati biyu a gidan mijin ki har kin saka uwar gidan sa tayi yaji?.” Asiya tayi murmushi tace, “Taya zan barta su more wannan daren ni ina nan a zaune gani banza mara hankali? Har wani rawar jiki yake dan zai koma wajan ta ni kuma sai na bari? Ai wallahi bata isa ba tunda na shigo gidan nan wallahi Allah sai ta bar gidan ko ta wanne hali, banzo gidan nan na zama a bayan ta ba sai dan ta zama a bayana.”

Momi tace, “Dakyau jinin Umma, yanzu Ina kud’in da kika d’auko?.” Asiya ta ‘karasa wajan kayan ta ta d’auko dala dubu d’aya ta kalli Momy tace, “kin gansu nan” ta saka kud’in a hanci taja numfashi tace, “duk inda kud’i yake na shiga sai na jiyo khamshin su wallahi, kamar nasan yau zaiyi amfani dasu na d’auka sai gashi ya nema yace suna Ina tace bata sani ba.”Momi tace, “ke taya kika san hakan akayi?.”
“Momi Kenan, yanzu nida ke ne a d’akin nan na ajjiye kud’i na fita na dawo ban gan su ba wa zan tambaya?.”

Momi tace, “Ni zaki zarga.” Tayi murmushi tace, “Meyasa?.”
“Saboda ni kad’ai nake shigowa d’akin nan, kuma ni nasan kin ajjiye kud’i dole ni zaki tambaya.”
“In kika ce baki d’auka ba zan yarda?.”
“A’a, sai dai kawai kiyi kara ko kyale ni amma kin san ni na d’auka sabida kud’in basu da k’afa.”

Asiya tayi dariya tace, “İrin wannan tarkon na had’a mata kuma ta fad’a. Kud’i nice na d’auka kuma yadda na d’auka dole ka yarda sata akayi saboda ko wacce rafar dalar guda d’aya na d’auka a ciki” ta fad’a tana irga dalolin tana murmushi.Momi tace, “bani na rik’e nima na kafa tarihi na tab’a rik’e dala.” Bata tayi ta rik’e ta zauna a gefen gado ita kuma Momi tace, “Yanzu mayar masa dasu zakiyi?.”

Hararar ta tayi tace, “Baki da hankali, ai wannan da kike gani biyar na Umma ne ta gama biyan bashin biki biyar nawa ne dan azurta kaina zanyi wallahi.” Momi tace, “Da gaskiyar ki, amma naga matar tana da mota ke bai siya miki ba.”
“Next target d’ina akan mota ne Momi, dole ya siya min mota koda baya so.”
“Yanzu gobe me zaki kaiwa babar tasa?.” Ta sauke numfashi tace, “mu jira goben dai, koda ban farka da wuri ba ki tabbatar da safe kin k’ona wannan turaren da Umma ta bayar Ina so hankalin sa ya d’auke daga batun Ameena gabad’aya taje can ta karata.”

Momi tace, “Yanzu rik’e kud’in nan naki, bara naje na had’o shayi nima na zama yar gidan y’an gayu” ta fad’a tana bata kud’in ta sauka daga saman. Asiya ta tashi sai da ta tabbatar ta sauka ta bude wardrobe din ta ta d’auko sark’ar da ta d’auko daga d’akin Yusuf tana dubawa tace, “Wannan ai nasan kud’in ta a kalla zai yi miliyan biyar ko goma koma yafi haka, in na siyar ai na zama Hajiya na loda kud’in a banki babu wanda zai san na d’auka ni kad’ai zanci kudina” ta fad’a tana mayar da sark’ar mazaunin ta zuciyar ta fess dan ko Umma baza ta fad’awa ba.

Abban Fiddausi ya kira Kawun su Fiddausi akan maganar auren ta suna tattaunawa a kai yace, “Dan Allah ka tabbatar kayi bincike a kansa, badan yau zan wuce Umra ba ai da babu abinda zai hana banyi da kaina ba. Ayi bincike in ka tabbatar babu matsala ko yaushe yake so a d’aura mata auren tunda ranakun iddar ta sun k’are. Amma ka tabbatar anyi bincike kar ayi auren nan babu bincike.”

Kawu yace,”in sha Allah za’ayi komai kamar kana nan, babu abinda zai faru in sha Allah.” Abba yace, “haka nake so Allah ya sanya alkhairi.” Ya amsa da amin aka zo ana ta sallama da Abba kafin kafin Kawu ya wuce dan ya kaishi airport.

Duka y’an gidan suna nan bayan tafiyar Abba ne Mama take sanar dasu batun auren Fiddausi ya taso babbar yayar su wacce duk ta fisu auren mai kud’in mijin tane ma ya biyawa Abba Umrah tace, “A dai yi bincike a kansa kar aje ba na gari bane ba.” Mama tace, “Ai sanannen mutum ne halayyar sa bazata b’uya ba.”

Bata ce komai ba tayi shiru akwai Fiddausi ta kalle ta cikin mamaki ita bata tab’a sanin dan uwan da suke ciki d’aya uwa d’aya uba d’aya zai yiwa dan uwan bak’in ciki ba in ka samu abinda yafi nasa ba sai a gidan su.
Chapter 22 · 0% Book details