Sashe 16
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zakiyya tace, “ke ko zaman turaka da yin komai da komai a ciki in a a.c ne a kan k’aton gado kafi gane me ake yi, amma kana cikin zafi dame zaka ji?.” Fiddausi tace, “Wallahi kamar ka mutu saboda b’acin rai, ke ai naga tashin hankali a gidan Ibrahim sai da na yakice wannan sabgar daga raina, in kuma shi yake so to sai dai yabi dare in an kawo wuta.” Tare suka kyalkyale da dariya ita da Zakiyya suka tafa Zakiyya tace, “kefe original yar iska ce Wallahi Fiddausi, Wato sai dai yabi dare?.”
Fiddausi tana dariya tace, “To abin yayi yawa ai ga zafi, gashi ba wani fahimta abin ma ake ba, ga zafin fatar jikin mutum, gashi da an gama ka fito rijiya d’iban ruwa, ka shiga band’aki a tsakar gida. Duk sanyi haka zaki zubawa kanki ruwan sanyi in ba haka ba sai dai kunna gawayi.” Suka sake tafawa suna dariya Fiddausi ta sake cewa, “Wallahi Ruky ki raba kanki da talauci, in ba haka ba haka za’a yi first night ga zafin gari ga zafin abu na farko ga b’akin cikin talauci.”
Ameena tana Jin su sai dai tayi murmushi kawai kafin Zakiyya ta kalli Agogo tace, “Yanzu ma an d’aura ai.” Duk tare suka kalli Ameena da nan take hawaye ya sakko mata daga idanun ta. Duk sai jikin su yayi sanyi suka dawo kusa da ita Fiddausi tace, “meye kuma na kukan Ameena? duk hakurin da kika yi ana neman auren sai yanzu kuma zuciyar ki zata karye?, ki daina wannan kukan dan Allah ki ta addu’a.”
Zakiyya tace, “Muma zamu taya ki addu’a dan bamu da wata hanya sai wannan din.” Ameena ta goge idanun ta tace, “Bawai fa Ina kuka dan an d’aura auren sa bane, kamar yadda Fid tace inda kud’i ai ba’a kishi.” Ruky tace, “Kar kiyi mana wani prending Malama, kowa yasan kishi kike kuma halak ne. Kin saba zama da mijin ki ko yaushe yanzu sai dai ya raba muku ku biyu dole Keda wata ki yi kishi. Zancen ma ba shi kike yi bai tashi ba kawai ki yi hak’uri.”
Kai kawai ta girgiza suka dinga bata baki suna rarrashi suna hira sallah ce kawai take tashin su dan koda Amira ta kawo musu abinci ta dole suka saka Ameena taci. Har bayan magriba suna nan da suna so a kawo amaryar suna nan dan suyi mata kallon tsaf amma dare kasancewar suna wajan dinner dole suka tafi suka barta.
Bata jira ma dawowar sa ba ta koma sama bayan ta kashe komai na k’asan ta kuma kulle duk abinda yake yi jikin ta a mace yake sosai zuciyar ta na tafasa kamar ruwan zafi sai da tasha maganin ciwon kai amma duk da haka a banza. Wanka tayi ta shirya tana shirin kwanciya Amira t shigo tana fad’in, “Aunty ga Amma nayi miki waya.” Wayar ta karb’a ta saka a kunne Amira ta fita kafin tace, “Amma barka da dare.”
Daga can b’angaren Amma tace, “Nasan yau bak’in dare ne a wajan ki Ameena, rana ce mai muni wacce baza ki manta da ita ba a tarihin rayuwar amma kiyi hak’uri, wannan hakurin da zaki ji ana cewa kiyi sai kin daure domin yana da matuk’ar wahala kafin ki yishi zaki sha Ameenatu. Kiyi hak’uri Ameenatu komai zai wuce kamar ba’a yi ba, in kika saka damuwa a ranki zaki cutu ne shi kuma yana tare da amaryar sa kinga kenan kanki kawai kika cuta babu shi, amma in kika kwantar da hankalin ki kowa sai ya zauna lafiya. Ki daure akwai wahala amma Kiyi hakuri ki kuma dinga addu’a.”
Kalaman Amma sai suke tuna mata da Maman ta hakan y saka ta hawaye bata shirya ba tace, “In sha Allah Amma zanyi, ki cigaba da min addu’a.”
“Addu’a ana yi miki Ameena, kamar yadda zan yiwa Yusuf addu’a haka zan yi miki domin kema y’ata ce, Kiyi hak’uri kinji duk abinda kika ji bai miki ba ki kira ki sanar dani ko kizo nan din. Kar ki bar damuwa a zuciyar ki ki fad’a min kinji ko?.”
Kamar tana gaban ta Ameena ta d’aga kai ta cigaba da yi mata nasiha kafin ta kashe wayar. Amira ce ta shigo ta kwanta a gefen ta ita da Zaytun ita kuma tana jingine da fuskar gado tana hasashen abubuwa kala-kala. Sai sha d’aya da rabi taji dirar motar Yusuf ko ba’a fad’a ba tasan shida amarya ne ta kulle idanun ta bacci take so tayi amma ta kasa. Shaid’an ne yake ta kawo mata abubuwa kala-kala a ranta hakan ya saka ta mik’e ta saka Hijjabi kawai ta tayar da sallah.
B’angaren Ango da amarya babu wanda ya kai su farin ciki a wannan ranar lokacin da suka shiga b’angaren babu kowa sai khamshin turare yake yi an gyara shi anyi komai amarya ta zauna a kan kujerar falon tana kallon falon zuciyar ta cike da farin ciki Wai wannan falon gidan tane.
Yusuf ya kalle ta yace, “Madam tashi zaki yi mu hau sama dare yayi fa.” Murmushi tayi ta mike tace, “To my love.” Shima murmushi yayi ya rik’e hannun ta zuwa saman. Asiya kuwa girgiza kai take yi a zuciyar ta tana fad’in, _Lallai Ameena bata da wani mahimmaci a wajan sa, tund asuka tawo baiyi zancen zai shiga wajan ta ba balle yace zamu je nida shi ya tara mu kamar yadda masu mata suke yi in sun k’ara aure, ko yanzu da muka zo ko k’ofar ta bai kalla ba. Ya zama dole na dage n sake watsar da ragowar mutuncin ta da yake gani._
Suna hawa saman tace, “kwalliyar fuskata ta dame ni.” Ya girgiza akai yace, “jeki ki wanke, kar ki manta Kiyi alwala nima zanyi yanzu zan fito” ya fad’a yana shiga d’aki da yake nasa a b’angaren itama ta shiga na kusa dashi.
Fuskar ta wanke sharp-sharp tayi wanka tare da alwalar ta fito ta shafe jikin ta da turaren da aka bata nan take ta fara wani shegen khamshin Wanda ya Karad’e dakin gabad’aya. Duk wani magani da aka bata aka tabbatar mata da tayi amfani dashi a daren a lokacin tayi dan bazata yi sake ba ko kad’an. Yana bud’e k’ofar khamshin ya bugi hancin sa ya lumshe idanu yana kallon ta Allah ya sani yana son khamshi sosai, tana tsaye cikin riga da wando ‘kasa na bacci yayi saurin kawar da abinda yazo ransa yace, “Muyi sallah.”
Babu bata lokaci suka tayar da sallah kamar ko wanne ma’aurata bayan sun idar ya gabatar mata da abinda ake shigowa amarya dashi, abinda ya bashi mamaki bata tsaya wani b’ata lokaci ba taja kazar tana ci abinta tana yi tana lumshe idanu dan gashin ya ji magi da yaji taci son ranta shi dai kallon ta yake yi kawai cikin mamakin ta dan bai tab’a jin labarin amaryar da tayi haka ba.
Lokacin su da Ameena ne ya fad’o masa a rai yadda ko d’and’ana naman batayi ba yayi saurin kawarwa yana kallon ta tashi ta shiga bandaki jin kad’an ta fito ta zauna a gefen gadon. Mik’ewa yayi ya rik’e hannun ta yace, “Muje dakina.” Duk da tana Jin tsoron abinda zai faru amma zuciyar ta farin ciki take yi ta shagwab’e fuska tace, “Ni a nan zan kwana.” Ya girgiza akai yace, “Ai d’akina nan ne wajan kwanciyar matata, taso muje.” Ba musu ta tashi ta bi bayan sa suka fita zuwa d’akin.
Kai tsaye wajan taga ya k’arasa bayan sun shiga ya d’aga labulen yana kallon tagar da take kallon tagar d’akin Ameena, Hasken d’akin ya gani a kunne kafin yayi wani tunani yaga an kashe ya sauke numfashi kamar mai tunanin wani abun. Asiya kuwa inda kayan sa suke ta kalla taga wanda ya cire a jikin wata doguwar anga ga kud’i a ajjiye akan madubi da yawa sabbi fil a mik’e ko wacce na jikin rafar ta.
Ido ta wara zuciyar ta na fad’a mata taje ta d’an ciro wani abun ta fara tarawa tun yanzu, ta d’aga ‘kafa da niyar zuwa wajan ya juyo tare da sakin labulen sai ta basar ta dawo ta zauna a gefen gadon ya kalle ta yayi murmushi yace, “Tunanin me kike yi?.” Kallon sa tayi sai ta sunkuyar da kai idanun ta wajan kud’in dan ko bata d’auka a yanzu ba tabbas da safe zata d’auka addu’ar ta kawai Allah yasa kar ya d’auke kafin lokacin.
Kwanciya tayi shima ya kwanta a bayan ta idanun ta a rufe kawai so take taji an wuce wajan duk da tana Jin tsoro amma ka’idar abinda aka bata ta shafa ne ba’a so ya wuce ranar ango bai kwanta da ita ba in ba haka ba aikin sa bazai yi tasiri yadda ake so ba. Kamar yasan tunanin abinda take yi kenan bai tsaya b’ata lokaci ba ya fara gabatar da abinda yake zuciyar sa shima dan saboda ya tanadarwa ranar gashi ya jima bai samu abinda yake so ba a wajan Ameena.
Tabbas a wannan dare hankalin sa ya gushe ya manta da kowa sai Asiya kawai, ya gigice a wannan dare har yake jin da bai same ta ba da zai iya rasa rayuwar sa. ya samu abinda yake so a tare da ita domin budurwa ce cikakkiya shine na farko da ya fara sanin ta sai dai akasin da aka samu na wani abun daban.
Sun jima suna bacci har suka makara sallah sai k’arfe bakwai na safe ya farka ya kalli agogo yayi saurin tashi yana sako k’afar sa k’asa ya taka bra d’inta ta da yake yashe a wajan. Tashi tsayen yayi ya tsuguna ya d’auki brazier yana latsa ta tare da bi da kallo. Gabad’aya katifa ce a jikin ta a haka ma in ka ajjiye sai ka d’auka an saka wani abun saboda yadda take a cike sosai kamar akwai kirjin a jiki. Kallon Asiyan yayi da take bacci ya tuna abinda ya tarar a jiyan sai yayi saurin ajjiye brazier ya shiga band’aki yana tambayar kansa, kenan abinda yaji gaskiya ne ba rud’ewa yayi ba? Kenan Asiya ciko take yi duk abinda yake marari a jikin ta ba nata bane kenan ko me……..?.