Sashe 33
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dr Mansura tace, “Gaskiya in ba’a cire ta daga cikin wannan damuwar da take ciki ba zuciyar ta zata iya kamuwa da ciwo. Yanzu zancen da nake maka jinin ta ya hau diye da tunanin ka badan anyi gaggawar kawo ta ba wallahi in ta fad’i zata iya gamuwa da cutar shanyewar b’arin jiki. Bama sai ta fad’i ba haka kawai za’a iya wayar gari aga ta kasa motsi ko kad’an. Damuwa tayi mata yawa na sha fad’a mata ta daina saka damuwa a zuciyar ta amma bata ganewa, wallahi damuwar da take ciki ko d’an shekara hamsin ne yake a irin ta zaunar dashi ake ana tambayar sa abinda yake faruwa saboda lafiyar sa, ya kamata a zauna da ita aji meye damuwar ta dan yadda jinin mata ya hau a yanzu sai na canja mata magungunan da take sha an bata wanda yafi na baya k’arfi.”
Yaya Adam ya girgiza kai yace, “Kenan in na fahimta Ameena tana da hawan jinin da har an d’ora ta akan magani ko?.”
“Kwarai kuwa, kusan wata hud’u kenan tana kan maganin hawan jini, a baya ban da jinin yake hawa ban d’ora ta kan magani ba ni kaina, saboda k’arancin shekarun ta tayi k’arama da fara Shan maganin hawan jini, amma yadda jinin yake hawa baya sauka ya zama dole na d’ora ta akan magani saboda rana irin ta yau.”
“Ameena k’anwata itace take da hawan jini? Damuwa ce ta haifar da hakan ko?.”
“Tabbas damuwa ce, dan wata ran in tazo zuciyar ta bata bugawa daidai saboda damuwar da tayi mata yawa. Sai na saka ta huta sosai nake bari tana tafiya gida. A ganina tunda kaine uba a gare ta gaskiya kayi wani abu dan ba iya hawan jini gare ta ba tana shan maganin kwantar da sha’awa.”
Da sauri ya kalle ta cikin tashin hankali da mamaki da tsoro Dr mansura tace, “Kwarai kuwa, da farko ban bata magani ba shima sai shawarwari da nake bata yadda zata samu kwanciyar hankali in hakan ya taso ba tare da an sha magani ba amma abin sai yaci tura dole ta takura sai da na bata magani, in na tambaya sai tace mijin ta baya nan yayi tafiya nace ta sanar a gida a d’auki mataki ko ya daina tafiyar ko ya dinga tafiya da ita sai tace to zatayi. Badan babu ruwana akan lamarin iyali ba da har gidan zanje na samu mijin nata nayi masa bayani tunda ya sanni na sanshi amma sai banje ba” ta kalli Ameena da take bacci tace, “Yanzu ya kai ya kawo maganin k’arfin maganin ya yi mata kad’an sai dai a bata wanda yafi shi k’arfi kuma hakan babbar illa ce ga rayuwar ya gabadaya.”
Yaya Adam girgiza kai yake cikin b’acin rai da zallar bak’in ciki had’i da takaicin halin da Yusuf ya aka kanwar sa yace, “Yaushe duka wannan abubuwan suka faru?.” Dr tace, “an jima sosai gaskiya, wani lokaci nice nake zuwa gidan saboda kar ta tawo ita kad’ai ban san meye zai faru da ita ba.”
Yaya Adam ya girgiza kai cikin gamsuwa da kalaman ta yace, “Yanzu in ta farka zata dawo daidai?.”
“İn sha Allah, zuwa safiya ma sai ku tafi gida lokacin jinin nata ya ya sauka.”
“Shikenan likita Mun gode.” Murmushi kawai tayi ta fita ya kalli Amira yace, “Ke a gaban ki yake dukan ta meyasa baki tab’a fad’a min ba ko a waya?.”
Amira tace, “bai tab’a dukan ta a gabana ba gaskiya sai dai naga ranta ya b’aci ko tana kuka, ranar nan ma cemin tayi mu bar gidan da daddare wajan sha d’aya muka fita ta rasa inda zamu je kawai tayi parking tana kuka. Sai Allah ya kawo Yayan Yusuf din wajan ya hana mu tafiya ko ina muje gidan sa a can ma muka kwana washe gari muka dawo gidan. Yaya har mota ta d’auka taje Bauchi ita kadai saboda damuwar Yusuf, Yaya kar ka barta dashi dan Allah ka hanata komawa gidan sa.”
Ya girgiza kai yace, “Zauna da ita ina zuwa” ya fad’a yana fita ta k’arasa kusa da ita ta zauna ta kwantar da Zaytun a kusa da Ameena dan tayi bacci tuni.
Lokacin da a Ameena suka fito Asiya suna tsaye ta taga suna kallon komai ganin ta fita suka kyalkyale da dariya suka tafa cikin shu’umanci Maimuna tace, “Shikenan ta fita in sha Allah bazata dawo ba.” Asiya tace, “Amma waye wannan naga ya fito daga gidan?.” Momi tace, “Oho kuma dai tunda dai ta fita ai shikenan.”
Maimuna tace, “mu zamu koma yanzu, ashe fa Momi tana nan ni zan wuce yanzu kije b’angaren nata da niyar rarrashi dan kiga halin da yake ciki.” Asiya tace, “To bara naje yanzu, mu fita tare” tare suka sakko suka fito zuwa b’angaren Ameena ita Maimuna ta fita ita kuma ta shiga.
Saman ta hau kai tsaye zuwa d’akin sa ta shiga ta ganshi a zaune a gefen gado ya had’e hannayen sa biyu yana kallon k’asa, da sauri ta shiga ta zauna kusa dashi tace, “My love naga Ameena ta fita da daddare nan ina taje? Badai wani abun kayi mata ba akan abinda ya faru d’azu?.” Banza yayi mata bai kula ta ba ta dan ba ta ita yake ba shi kad’ai yasan abinda yake zuciyar sa, kalaman ta yake tunawa da take cewa indai ta fita daga gidan ya saka a ransa ta fita kenan, bata fahimci baya son damuwa ba ta sake cewa, “Dan Allah ka fad’a min me kayi mata, nifa bance kayi mata komai ba wallahi yanzu ina ta tafi?” Ta fad’a tana shirin yin kuka yana kallon sa.
D’ago jajayen idanun sa yayi ya kalle ta yace, “Tashi ki fita.” Gaban ta ya fad’i ganin yadda idanun sa suka canja kala zuwa ja, ga fuskar sa a d’aure kamar bashi ba ta daure ta kalle shi tace, “Amma my love…..” da tsawa ya katse ta yace, “Nace ki tashi ki fita ko!?.” Yadda yayi tsawar sai da ta tsorata bata san ta mik’e tsaye ba tana kallon sa tana ja baya amma bata fita ba ya sake kallon ta ya girgiza kai yace, “Wallahi kika bari na taso sai jikin ki ya fad’a miki.” Jin abinda yace ya saka ta fita jiki a sanyaye zuciyar ta na bugawa tana tunanin me hakan yake nufi kenan?.
Yusuf ya rasa inda zai saka kansa bai san abinda yake damun sa ba gabad’aya komai ji yake ya fita daga ransa duniyar na juya masa take ba tare da tasan dalilin hakan ba, tashi yayi yana zaga d’akin abubuwan da suka faru suna sake yi masa yawo a zuciyar sa da idanun sa.
“Meyasa nace mata bana sonta? Meyasa na fad’a?!” Ya fad’a da karfi yana dukan wardrobe da take gefe yana sauke numfashi kamar yayi gudu. “Meyasa in raina ya b’aci bana daidaita kaina a yanzu? Meyasa zan yiwa Ameena haka? Ameena ta fa?” Ya sake fad’a a bayyane tare da kulle idanun sa ya bud’e yana kallon sama tare da cigaba da yawo a d’akin. Tsayawa yayi cak ya sauke numfashi ya kalli wata drawer kawai ya k’arasa wajan ya bud’e ya d’auko kwalba madaidaiciya mars girma sosai ya bud’e kanta har zai fara sha sai kuma ya tsaya, tunawa yayi yace bazai kuma sha ba sai kuma ya share tunanin ya kafa kai yana sha har sai da yasha rabi sannan ya ajjiye kwalbar yana sauke numfashi.
Ameena bata jima tana baccin ba ta farka ita kanta taji dad’inciwon kan da yake damun ta idanun ta biyu har asuba sai bayan anyi sallah ne ta sake yin bacci ta farka k’arfe tara na safe. Tana farkawa Yaya Adam yana shigowa suka had’a ido ta tashi zaune ya kalle ta yace, “Ameena kin tashi? Me yake damun ki?” Ya fad’a yana k’arasowa kusa da ya dafa kafadar ta mike zaune sosai tace, “Da sauki Yaya, ina kwana.”
“Lafiya lau, ya jikin naki?.”
“Naji sauk’i sosai kan nawa ma ya daina ciwo.”
“Haka ake so, likitan da ta duba ki ta tashi amma tace min in kin farka zamu iya tafiya. K’ok’arta ki tashi muje dan Amira ta samu ta huta itama.”
Tsaf Ameena ta mik’e tsaye kamar ba ita ba ta saka mayafin ta suka fito tare suka shiga mota kai tsaye gidan sa ya wuce. Daman matar sa tasan da zuwan su ta gyarawa Ameena d’akin da take ajjiye kaya in suna Kano suna zuwa can suka wuce Ameena a nan taga kayan ta ajjiye ta zauna a gefen katifar Amira kuma ta shiga bandaki.
Sai bayan Amira tayi wanka ta yiwa Zaytun sun shirya sannan ta d’auke ta ta fita a lokacin Yaya ya shigowa Ameena da abinci da kansa ya zauna akan kujera yana kallon ta yace, “Sannu, D’auki kici Ameena.” Ba musu ta d’auka tana shan tea da aka had’o mata yasha madara tana cin bread d’in sai da yaga taci sosai sannan ya bari ta ajjiye. Kallon fuskar ta yake har lokacin a kunbure take sai ya ciro waya ya kira duka k’annen sa yace suzo gobe gida yana son ganin ko wacce a cikin su.
Yana yanke wayar kiran Yayan Bauchi yana shigowa ya d’auka kafin tayi magana yace, “Ai kin yin laifin da banyi tunanin zaki yi shi ba, kin nuna min ban isa da Ameena ba kece kuke cike d’aya da ita ni ba wani abun bane ba Samira.” Daga can b’angaren tace, “kayi hakuri dan Allah Yaya, Amira ta sanar dani komai ina hanya gobe nima zan zo. Ya jikin Ameenah?.” Ya kalli Ameena yace, “taji sauki abinci ta gama ci yanzu.”
“Alhamdulillah, tun jiya da Amira ta fad’a min banyi bacci ba wallahi, abun yayi yawa Yusuf bashi da mutunci baya kyautawa kamar ba auren soyayya sukayi ba.” Yaya Adam yayi k’aramin tsaki yace, “ai duk laifin kine, da kin fad’a min da ba’a zo nan ba.” Yaya tace, “kayi hak’uri dan Allah, sai na shigo Yaya.” Bai ce komai ba ya yanke wayar ya kalli Ameena da kanta yake a k’asa.