Sashe 4
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji yace, "Amin, amma ki tuna itace uwar d'an sa ko da nan gaba in yaji yana da sha'awar mayar da iya ai ba wani abun bane ba. Kuma shi kansa mahaifinta wallahi ba’a son ransa hakan ta faru ba, yana son zaman y’arsa da İbrahim dan ya fad’a min cikin yaran sa mata ita kadai ce ba’a kawo masa case d’in sa gaban sa.”
"To yanzu ai y’ar tasa ta nuna bata yi kaga shikenan ai kowa ya huta, Zan rik’e Amir daga nan har girman sa in sha Allah, koda babu ni nasan y’an uwan sa zasu rik’e shi bazai tab’a kukan rashin uwa ba a rayuwar sa.”
"Kedai yarinyar nan ta fita daga ranki kamar ba kece kike son ta kafin auren ba. Yadda kika so yarinyar nan ko matan yayyen sa baki so haka ba.”
"Na so ta sosai Alhaji, amma ai Alhaji duk Wanda zai zo gaban idanun ka yace baya son d'anka baya qaunar sa kuma sai ya kashe shi duk son da kake masa daga ranar ko bai fita ba sai kaso mafi yawa ya ragu.”
Alhaji yace, "Gaskiya ne, kai Ibrahim kana son dawo da ita ne?." Ya girgiza kai yace, "A'a Alhaji Allah ya had'a kowa da rabon sa, taje inda take hange ni kuma na tsaya a matsayina."
Alhaji yace, "Amma karatun addinin nata da aka yi kwadayi aka auro ta bai amfana mata da komai ba, tayi abinda wata wacce bata je islamiyya bama bazata aikata shi ba. Ni kaina daga lokacin da tazo nan ta fad’i kalaman nan taji duk duniya ta fita daga raina, Ina yi ne sabida nason kana sonta, Ina yi kuma saboda Amir. Amma Tunda yanzu haka ya zama shikenan Allah yasa shine alkhairi." Suka amsa da amin kafin İbrahim ya tashi ya fita dan wajan aiki yake son wucewa, yayi alqawarin mantawa da komai ya fuskanci rayuwar sa, ya kuma alqawarin bazai bar wata damuwa tayi tasiri a kansa ba. Fiddausi ko itace mace d’aya tal a duniya ya barta.
*Bayan kwana biyu.*
Nana Haleema
Mai daki
Boook2
Paid
500.
Book2
003
A cikin kwanakin Fiddausi ta ware ta shiga harkokin ta kamar ba ita ba ta mayar da komai ba komai bane sabgar ta kawai take suna zuba soyayya ita da Alhaji a waya tunda bata bashi damar zuwa ba har lokacin. Soyayya suke kamar saurayi da budurwa ya shagab’ata da kud’i komai take so sai ya bata, ko bata tambaya ba zai bata hakan ya saka take saka son sa sosai suna Shan soyayya abin su. Sosai tayi kyau abin ta tayi k'iba ta sake yin haske kamar ba ita ba.
A safiyar ranar litinin Wanda yayi daidai da sati uku da rabuwar su da ibrahim suna waya ita da Alhaji ya takura akan shi sai yazo gida gaskiya dole ta bashi dama yaje wajan Kawu Sa’idu. Tana kashe wayar taji Mama na kiran ta ta taso ta fito Mama ta dube ta tace, "Wai zaman me kike da a d’aki ko yaushe ko motsin ki ba'a ji ai ta kiran ki bakya Jin mutane?."
Fiddausi tace, "Kaina ne yake ciwo kuma Muna magana dasu Ameenatu ne."
"Abban kune zai yi tafiya zai je qauyen ku yake kiran ki har ya tafi."
"Ban ji ba wallahi, dana fito mun yi sallama." Mama tace, "Sai ki zo ki d’ora mana abinci rana ta fito" ta fad'a tanaa tashi ta shiga daki ba tare da ta sake cewa komai ba.
Fiddausi ta b'ata rai ita bata son wannan aikin da ake saka ta wallahi, ko yaushe ace tazo tayi girki tana zaune a kwala mata kira ace tazo tayi wannan ita wallahi ta gaji. Kitchen din ta shiga tana mita a zuciyar ta a haka ta d'ora girkin ranta a b'ace. Burin ta kawai ta gama ta fice daga gidan kar a sake saka ta wani aikin.
Tana gama abincin ta shiga d’aki tayi sallar azahar tayi wanka tana shiryawa taji muryar y’an gidan su da alama sun zo. Tana gama shirya wa ta fito ta tarar suna cin abincin da ta gama dafawa tayi murmushi tace, "Yaya Sannu d zuwa." Ta kalle ta tace, "Yauwa Fiddausi, ya zaman gıda?." Kafin tayi magana Mama tace, "Zaman gıda gashi nan tana yi Kullum tana zaune a d'aki tana aikin danna waya."
Mama ta sake kallon ta tace, "Yayar ki da y'ay'an ki sun cinye abincin da kika dafa, sai dai ki sake d'orawa dan ko naki babu. Nima ban samu ba, kece kika dafa kad’an ga abinci a gida sai ki dafa kad’an kamar wanda aka sammana.” Wani iri taji a zuciyar ta tace, “Kar na dafa da yawa yayi yawa ne ganin Abba baya nan.”
“Gashi ai ya k’are yanzu, sai ki dafa abinda zaki ci.” kamar zatayi magana sai ta fasa ta zauna Yaya tace, "Kije ki dafa mun cinye wannan, bamu san baki ci ba ai da bamu cinye ba.”
"A'a basai na dafa ba a k'oshe nake." Sai kuma ta mike tace, "Mama zanje gidan Zakiyya."
Mama tace, "Babu inda zaki je, Kullum daga yawo nan sai can bakya son zama a gida gabad’aya kamar a kanki aka fara zawarci . Haka kika fita shekaran jiya Amir yazo ya gama zaman sa bakya nan haka aka mayar dashi har magriba bakya gidan. Babu inda zaki je ko koma d’aki ki cigaba da danna waya amma baza ki fita ba.” Fiddausi bata ce komai ba ta koma d’aki gabad’aya zaman gidan ya ishe ta gwara ma tayi auren ta huta da fadan da Mama take mata ga aiki komai ita.
Asiya shirye-shiryen biki kawai ake yi dan lokacin bikin saura sati biyar kashe kudi kawai suke Dan duk abinda suke so Yusuf yana yi musu shiyasa suke abinda suke so saboda akwai kud’i a hannu. Umma Sakina na zaune ita da Umma suna tattauna yadda abubuwa zasu tafi Asiya suka shigo ita da Maimunatu da Kaya a hannun su sosai manya-manyan ledoji suka shigo.
Ajjiye kayan sukayi Asiya tace, "Wallahi na gaji Umma, kin ji bayana?." Umma Sakina tayi dariya tace, "Waye ya fad’a miki zama amarya sauk’i ne dashi?." Umma tace, "kun siyo kayan gabadaya?."
Maimuna tace, "Fridge ne yana akorikura tare da Fauziyya yanzu zasu ‘karaso."
Umma ta kalli Umma Sakina tace, "Sakina babu kud’in tv ma, Gashi gida yake ginawa makeke tv din ma a saka uku ko hud’u ma. Dan fa Mun samu ma yace zai zuba kayan gado da kujeru ne mu na kitchen ne kawai dasu tv da fridge, amma kinga kud’in nan yana kakarewa.” Umma Sakina ta kalli Umma tace, “ai babu ta inda kud’i zai kakare mana bayan akwai Yusuf” ta kalli Asiya tace, "Ke Asiya ki sake kiran sa ko d'ari biyar ne mu sake karba." Asiya ta b'ata fuska tace, "Umma Sakina miliyan uku fa ya bayar yanzu sai na sake yi masa maganar wani kud’in? Ni wallahi bazan iya ba."
Umma Sakina tace, "Had'a ni dashi ni na fad’a masa Tunda baza ki iya ba.” Asiya ta wara ido cikin mamaki tace, "Haba dan Allah ni wallahi na gaji da tambayar sa kud’i wallahi. Wannan ai sai yaga kamar ma kudin nake so.” Umma Sakina ta girgiza kai ta rik’e hab’a tace, "Zaka zamuyi dake Asiya? Muna murna zaki shiga inda zamu huta mu samu abinda muke so tun yanzu kin fara yi mana hanya-hanya?."
Asiya tace, "Ba haka bane bafa Umma Sakina, kawai dai bana so yaga Ina yawan karbar kudi a hannun sane shiyasa kawai.”
Umma tace, "Waye ya fad’a miki zai ga kina k'arba a hannun sa?" Umma ta kalli Sakina tace, "Duk shirin da muke yiwa yarinyar nan gani take a banza yake, duk kudin da aka karb’a ba ita aka kashewa ba,? Inda tasan abinda aka yi da bata ce haka ba.” Umma Sakina tace, "D’auka take yi ai mu kud’in banza muke kashewa. Malama ki tashi kiyi masa waya kice kina so ki ganshi in yazo ki san yadda zakiyi ya k'ara miki kudi, ke ai macece kina da kissa a jinin ki, in ya tashi zuwa ki tabbatar kin shafa wannan turaren da na baki."
Asiya tace, “Yanzun zan kira shi?.
“Eh Yanzun nan.” ta tashi ta shiga d’aki ita sam bata son abinda suke sakata yanzu ta fisu so sai ta shiga gidan a lokacin ya zama matar sa babu abinda zai yi mata ko me zatayi, yadda ko bai bata ba zata d'auka amma yanzu sai ya raina ta.
Yadda take masa shagwab'a waya dole yace mata da yamma zai zo dan ta rikita shi burin sa yazo ya ganta yaje meye damuwar dan baya son damuwar ta kk kad’an. Kafin yamma d’in tayi wanka ta shirya sai khamshi take yi na turaren da aka bata har lokacin Umma Sakina tana haka tazo ta wuce su lokacin da yazo har ya shigo cikin gidan.
Fuska babu walwala ta shiga yana hango ta sai ya mik’e tsaye yana kallon ta yace, "My love lafiya kike?."K’arasowa tayi ta zauna tayi shiru bata ce komai ba shima ya zauna yana kallon ta yace, "Meya faru ne wai?." Asiya ta kalle shi tace, "Ni ban San ta inda zan fara ba."
"Fara ta ko Ina my love." Tayi shiru na wani lokaci kafin sauke numfashi tace, "Wacce zata yi min gyaran jiki ce na bata kudina har naira dubu dari biyar shine ta hadu da scammers suka kwashe mata kudin account gabadaya basu bar ko sisi ba, atm din ta ta yar a wajan biki akayi amfani dashi aka kwashe komai my love. ni ban san me zance ba ta kira ni tana ta kuka k’arshe tazo gidan nan tana fad’awa su Umma."