Sashe 26
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asiya ta fara hawaye tace, "haka kawai muna cikin tafiya mun fito daga gidan Ammah lafiya muna hira Muna yo nisa ta tsayar da motar tace na fita bata sona bata qauna ganina, wai na aure ka na raba ku shiyasa itama bazata soni ba kuma wallahi sai tayi duk abinda zatayi ganin ta fitar dani daga gidan nan. My love Ina son Aunty da zuciya d'aya amma ban san meyasa ita bata sona ba, nasan laifina ne dana auri mijin ta amma ta manta kaddarar aure ce ta had'a mu? ta manta cewa Allah ya rubuta kai mijina ne tun Ina cikin Umma na?."
Ta share hawayen ta tace, "ban fita da kud'i ba saboda tare muke dakai gashi ba wani sanin unguwar nan nayi ba kuma koda da kudin babu masu napep da zan hawo na k'araso, a k'afa nazo har gidan nan Ina jin tsoron kar dare yayi ayi min wani abun a hanya" ta fad'a tana fashewa da kuka ta kifa kanta a kirjin sa.
Bubbuga bayan ta yake yi gabad'aya ta bashi tausayi ya rasa me ta tare wa Ameena da bata qaunar ta bayan ita da zuciya d'aya take zaune da ita, ai ko dan soyayyar da take mata yaci ace ta sassauta nata kishin, cikin kukan yaji ta sake cewa, "dan Allah ka bata hak'uri inda akwai abinda nayi mata tayi hak'uri ta yafe min, laifina nasan bai wuce auren ka ba nasan dole taji babu dadi amma tayi hak'uri haka Allah ya nufa. Bazan ce na daina kula ta ba amma kayi hak'uri ni bazan sake shiga motar ta ba saboda gudun kar raina ya b'aci nima muyi fad'a a hanya mu zubar maka da mutunci. Gwara na hau napep duk inda zanje ya kai yafi min alkhairi."
Numfashi yake saukewa a hankali ya rasa abinda yake damun Ameena wallahi gabadaya ta gama canjawa kamar ba wacce ya sani a baya ba, tashen magana da rashin kunya take ji dashi ko shi d'in bata k'yale balle Asiya. Yace, "Kiyi hak'uri kema zan siya miki taki motar na samar miki da driver kafin ki koya, kar ki rik'e ta a zuciyar kiyi hak'uri watakila ranta ne a b'ace."
Asiya tace, "Ina jin haka ne, amma bai kamata tayi min haka akan hanya ba ko babu komai matar aure ce ni bai kamata ba. Amma babu komai ai ya wuce ni bazan rik'e ta ba saboda kai." Yayi murmushi kafin yayi magana tace, "ban d'auka zaka yarda bama dan naji tace ka yarda da ita komai nace maka baza ka yarda ba ni zaka karyata, Allah yasan ba k'arya nake mata ba kuma ban fad'a maka dan wani abun ba sai dan kayi mata magana a gyara nan gaba" ta sake fashewa da kuka yace, "ya isa ki daina kuka kiyi hak'uri kinji, Momi tana sama tana jiran ki muje na raka ki." Har saman ya raka ta tana takawa dakyar ta shiga d'aki ya saka Momi tazo ta kulle ko Ina shi kuma ya fita zuwa wajan Ameena ransa ya b'aci sosai akan abinda ta aikata.
Yana fita Asiya ta 'karasa wajan window da sauri tana kallon sa har ya shiga wajan Ameena tace, "Ameena baki san wa aka d'auko miki a matsayin kishiya ba, duk wannan rawar kan da kike sai na sauke shi wallahi."
Momi ta kalle ta tace, "Ya kuka yi?." Asiya ta kalle ta tace, "Barni da ita akwai, kedai aikin ki yayi kyau da kika kwanta a bakin kofa kinga yanzu ya sanar dani zai siya min mota kinga cigaba na farko kenan, cigaba na biyu kuma...." Ta 'karasa wajan taga tana kallon wajan Ameena tace, "Na fitar da waccan Shegiyar daga gidan nan, dan indai ban fiddata ba hankalina bazai kwanta ba wallahi."
Momi ta dafa kafad'ar ta suna kallon tagar tace, "Kina yin komai yadda ya kamata sai a cigaba daga inda aka tsaya. amma wallahi jikin ki tsami yake, na fad'a miki ki dinga daurewa kina wanka saboda mijin ki amma kin kasa saboda kin saba zama haka a goda." Asiya ta shanshana jikin ta tace, "a daren nan zanyi wanka? Ashe baza'a yi ba" ta fad'a tana fita daga dakin Momi tayi murmushi kawai a bayyane tace, "ai kuwa zaku samu matsala da mijin ki akan wannan Shegiyar k'azantar taki." Itama ta biyo bayan ta tana jininga kazantar Asiya bata son wanka ko kusa.
#Mai daki
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema.
Book2
017
Yusuf yana hawa saman ya sake ganin ta a tsaye a falon sa ta d'auki waya tana dannawa, ya tsaya ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya wuce zuwa nata falon yaga Amira a zaune a kan kujera yace, "Amira a Ina kuka sauke Asiya?." Amira tace, "A kan hanya." Bai sake cewa komai ba ya dawo inda ya bar Ameena tana tsaye jikin window iska na shigowa sanyin yana ratsa ta idanun ta a kulle da alama iskar nayi mata dadi.
Murya a tausashe yace, "Abinda kika yi kin kyauta kenan?." Ba tare da ta kalle shi ba tace, "Diamond na sace kuma?." Ya bita da kallon mamaki dan gabad'aya ta canja masa, inda a lokacin baya ne bazata iya ce masa haka ba amma yanzu duk abinda yazo bakin ta fad'a take yi kai tsaye ba tare da fargaba ba. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya wuce ta zuwa sama itama ta kulle tagar ta wuce d'akin ta dan so take ta daina sakawa ranta damuwar sa dan taga alama kashe kanta zatayi a banza.
Humaira so take kawai Ammah ta taso daga falo zuwa d'aki dan ta fesa mata labarin barauniyar amarya, ai kam tana shigowa ta biyo bayan ta tace, "Ammah kin San wani abu?." Ammah ta zauna tace, "Sai kin fad'a." Tayi dariya tace, "Labarin barauniyar Amarya zan baki."
Ammah tace, "ba yanzu aka gama film din a arewa 24 ba? Ke ni bana son ji bacci zanyi."
"Ai Ammah wannan ta zahiri ce ba ta film ba, ai Yaya Yusuf ya kawo mana b'arauniyar amarya." Ammah ta kalle ta tace, "ban gane ba." Humaira tayi dariya tace, "Wallahi amaryar sa barauniyar ce, daga zaman ta a d'akina har ta sace min smart watch da wannan yarin" ta fad'a tana nuna mata yarin da kuma agogon.
Ammah ta Harare ta tace, "ke bana son shirme fa, dan bakya son ta ba haka yana nufin ki dinga jifan ta da wadannan kalamai ba ko babu komai matar Yayan ki ce."
"Wallahi Ammah ba k'arya nake yi ba, a jakar ta naga agogona da kuma yarin nan wallahi, ai bazan mata k'arya ba itama tasan na gani. Meyasa ban tab'a cewa Ameena tayi ba sai ita?."
"To ya akayi suke a hannun ki tunda kince ta sata?."
"Nayi connecting na agogon da wayata sai na Nemi shi na rasa kawai sai na kunna waka Ina bin sautin ko Ina yadda zan jiyo kawai na jiyo shi a jakar ta Ina bud'ewa na ganshi had'e da wannan yarin."
Ammah ta girgiza kai cikin mamaki tace, "ikon Allah!."
"Abin haushin ma sata a gidan sirikai."
"Ke ban amince da abinda kika ce bafa kar naji maganar a wajan wani ko wata, in halin ta ne nan gaba zata sake yi. Tashi ki bani waje" ta fad'a tana kwanciya dan bata son zuciyar ta ta fara zargin yarinyar amma tunda da ta ganta ita kanta bata yi mata ba kawai dai babu yadda zatayi ne ta Riga ta zama matar d'an ta.
Washe gari.
Kud'i masu yawa Alhaji bello ya ajjiye a gaban Kawu ya kalle shi yace, "Kawu ni in da dama gobe nake so a daura aurena da ita bayan sallar juma'a in ka amince." Kawu ya kalli kud'in ya kalle shi yayi dariya yace, "Baka da damuwa Alhaji in ma yanzu kake so a d'aura sai a daura auren ba wani abun damuwa bane ba ai."
Alhaji bello yayi dariyar farin ciki yace, "Inda za'a daura a yanzun ai dana ji dad'i sosai wallahi, amma mu jira goben in Allah ya kaimu sai a daura auren a masallaci mutane da dama su shaida." Kawu yace, "Shikenan babu laifi, Allah yanına mana goben Lafiya." Ya amsa da amin sukayi sallama ya wuce shi kuma kai tsaye gidan su Fidy ya nufo.
Da sallama ya shiga ya same su daga ita sai Mama ya zauna suka gaida da Mama ya d'auko kudin ya mik'awa Mama yace, "Ga sadaki da kud'in komai na aure wanda zai auri Fiddausi ya kawo, gobe in Allah ya kaimu za'a d'aura musu aure bayan sallar juma'a." Mama ta karbi kudin tana juyawa kafin tace, "Da wuri haka?."
"To me za'a jira? Ai gwara ayi a wuce wajan kawai. Ki shirya gobe za'a daura auren daga nan sai a San abinda za'ayi." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba amma cikin zuciyar ta ba k'aramin farin ciki take yi ba burin ta zai cika bata kashe auren ta a banza ba.
A cikin mintina kad'an ta sanar da Zakiyya aka fara shiri a waya kafin ta fad'awa Ruky da kuma Ameena suna ta mamakin saurin abun sai suka ce mata zasu shigo gidan nasu. Fiddausi sai rawar kai ake ana rawar k'afa za'a shiga gidan mai kudi ta rasa nutsuwar ta gabad'aya a lokacin saboda farin ciki.
Har dare Fiddausi farin ciki take buri kawai take gobe tayi a daura mata aure da masoyin ta kuma abin alfaharin ta. Tun safiyar da Kawu yazo take jiran shigowar Rukayya amma bata zo ba kasancewar suna kusa a yanzu duk sai taji babu dad'i dan tana so ta samu abokiyar da zata taya ta murna a wannan lokacin, har dare babu Rukayya sai waya take yi mata duk ta damu.
A daren Rukayya na tsaye a kan titin Tarauni tana ta zagaye babu abin hawa ga dare yayi ga yanayi na sanyi babu jama'a sosai a hanyar gabad'aya a tsorace take dan bata saba kaiwa haka a waje ba. Hankalin ta ya tashi tana ji wayar ta na vibrating amma bata d'auka ba saboda tasan kiran bazai wuce na Baba ko Umma ba shiyasa ta ki d'auko wayar dan bata san ma abinda zata ce ba.