← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 42

Sashe 25

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Book2
016

        Bayan sallar Azahar suka shirya shida ita suka tafi gidan Ammah, a harabar gidan yayi parking ta kalle shi tayi kyau cikin lace pink color tace, "Nayi kyau ko?." Murmushi yayi yaja kumatun ta yace, "Sau nawa zan maimaita miki kinyi kyau?kin tambaye ni ya kai sau biyar kenan nace kin yi kyau ki yarda Kinyi din. Muje" ya fad'a yana bud'e motar suka fita zuwa cikin gidan.

Babu kowa a babban falon sai kayan wasan  jikokin gidan a baje a falon ya kalle ta yace, "Zauna bara na kira Ammah." Kallon falon take yi Allah Allah take idanun ta su hango mata kudi ko wani abun d'auka tayi ta saka a jaka kafin a farga  amma babu komai sai kayan wasa tayi tsaki kawai ta zauna jiran Ammah din.

Ya jima a ciki sannan suka fito tare da Ammah tana cewa, "meyasa baka tawo min da takwara ba?." Daidai lokacin suka shigo falon Ammah tayi murmushi cikin fara'a tace, "Amarya barka da zuwa." Itama Asiya tayi murmushi da girmamawa ta sakko daga kujerar ta zauna akan carpet bayan Ammah ya zauna akan kujera tace, "Barka da rana Amma."
"Barka dai Asiya, ya gida?."
"Alhamdulillah, mu same ku lafiya?."
"Lafiya lau, ya mutanen gidan naku?."
"Lafiya lau Ammah suke, da mukayi waya da Umma ma tace na gaishe ki."
"Ina amsawa, a gaishe ta da kyau" Ammah ta fad'a tana kallon sa taga gabad'aya ita yake kallo sai murmushi yake yi ta girgiza kai kawai bata ce komai ba.

Ganin kallon da yake yiwa Asiya yayi yawa ya saka tace, "Yusuf ka kawo mata ruwa mana." Asiya ta girgiza kai tace, "Haba Ammah kamar wata bakuwa? A'a na koshi wallahi." Amma tace, "Gaskiya ne ba bak'uwa bace ba." Ta kalli Yusuf tace, "Baka je store bane?."
"Eh, sai nayi la'asar zanje yanzu zanje wata jana'iza na dawo."
Ammah tace, "Allah ya jikan rai." Ya amsa da amin ya fita ya bar Asiya a gidan.

Ta sake sosai kamar ba ita ba Ammah ma bata nuna mata komai ba tayi mata tambaya akan zaman gidan nasu  ta amsa da Lafiya lau daga nan Ammah ta tashi ta aiko mata Humaira dan suyi hira. 

Bayan sallar la'asar ta idar da sallah a d'akin Humaira take bin d'akin da kallo tana so ta ga wani abu wanda zaiyi kud'in in za'a siyar nan idanun ta ya kai kan wani smart watch na Humaira akan mudubi ta bishi da kallo kafin ta k'arasa wajan ta d'auka ta juya shi tace, "Wannan da gani babban ne wallahi, in aka siyar zai yi abinda ake so" ta fad'a tana ta saka shi a cikin jakar ta ta koma ta zauna kamar bata d'auki komai ba. Idanun ta suka sake kai kan wani karamin yari guda biyu kai kana gani kasan yarin na gold ne sai kuwa ta mik'e ta sake d'auka ta saka a jaka ta koma ta zauna.

Humaira ce  dawo tana fadin, "Na barki ke kad'ai ko? Kizo ga abinci can, ko na kawo miki nan?." Asiya tayi dariya tace, "A'a muje can din naci." Tare suka fita ta zauna akan kujera Humaira ta bata abincin ta d'iba ta fara ci.

Tana gama ci Ammah ta shigo falon bayan ta Ameena ce da Humaira da yake rik'e da Zaitun tana cewa, "kuma bai fad'a min zaki zo ba." Ameena ta zauna tace, "ya manta ne, na kwana biyu bamu gaisa ba shiyasa na biyo." Ammah tayi murmushi tace, "Gaskiya ne." Ameena suka had'o ido da Asiya kafin Ameena tayi magana Asiya tace, "Aunty barka da zuwa." Ameena tayi murmushi tace, "Ashe kina nan?."
"Wallahi tun d'azu." Ameena ta murmusa kawai bata ce komai ba.

Humaira ta kalli Ameena da ta jingina da kujera ta dafe kanta tace, "Mummy anya lafiya kike kuwa? Nifa idona wata rama nake ganin kinyi wallahi, sannan ga yanayin ki ya nuna kamar baki da lafiya." Ammah tace, "nima na gani." Humaira tace, "Ko da yake ai kanwar Zaytun aka samu." Ameena murmushi akwai tayi sab'anin Asiya da kirjin ta ya buga ta sake kallon Ameena wai ta tabbatar ciki ne da ita amma bata gane ba, lallai ya kamata ta d'auki mataki kafin hakan ya tabbata. Dole ma ta tambayi Yusuf dan taji maganar gaskiya ce.

Humaira ta shiga d'akin ta ta d'auki wayar ta sai taga wayar tayi connecting da smart watch din ta tayi tsaki tace, "Ina na ajjiye shi ne nayi disconnecting?." Dubawa take bata ganshi ba tace, "abu kamar aljani yanzu fa na ajjiye shi." Sai tayi tsaki sai ta saka wak'a a wayar ta tana bin ki Ina na d'akin yadda zata ji sautin wak'ar yana fitowa ta agogon.

Har ta gota jakar Asiya sai ta dawo jin kamar fa daga jakar take jin sautin wak'ar na fitowa, kamar baza ta bud'e ba sai  ta zuge sai kuwa ga agogon ta a ciki ta wara ido tace, "Kai!" Ta fad'a tana sake duba jakar nan taga yarin gold din ta Karami wanda ta cire jiya ta ajjiye.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kenan Yaya Yusuf mai halin b'era ya d'auko mana?." Sai kuma ta kyalkyale da dariya tace, "Amma yarinyar nan bata da hankali, ta rasa a inda zatayi sata sai gidan sirikan ta?, gidan sirikan ma kuma zuwan farko?" Ta sake yin dariya tace, "lallai dole amma taji labarin nan."

Mayar mata da jakar tayi inda ta ajjiye ta ta saka agogon a hannun ta ta fito dan Asiya din ta gani taga ya yanayin ta zai koma. Hira suke tayi a haka har sai da ta saka  Asiya ta kalli agogon sai taga tayi saurin d'auke ido ita kuma tayi dariya kawai bata nuna ba ganin Asiya din ta basar.

Sun jima a gidan har bayan magriba Abbah ya dawo suka je suka gaisa ya musu nasiha ita da Ameena suka dawo falon Ammah a nan suka tarar da Yusuf. Tunda suka tawo yake kallon Ameena wacce ko inda yake bata kalla ba ganin hakan ya lumshe ido ya sake bud'ewa yana kallon ta sai kuma ya d'auke kansa ya cigaba da wasa da Zaytun.

Ammah ta kalle shi tace, "To dare yayi sai ku tafi kar a shiga hakkın su." Yusuf yace, "ba gida zanje ba store zan koma yanzu Ammah, sai dai su jira ni na dawo." Ammah tace, "A'a baza ayi haka ba, tunda Ameena mota a take sai su koma tare bazata ji dadin zama ba kaga bak'uwa ce." Yusuf yace, "to su je ni zan koma yanzu" ya fad'a yana fita tare da Zaytun dan ba jimawa zai yi ba shiyasa ya tafi da ita tayi masa rakiya.

          Kafin su tafi sai da Humaira ta tabbatar ta sake duba jakar Asiya taga babu komai wanda ta sata sannan ta bari Asiya ta dauki jakar suka fito suka shiga mota suka tafi.
Sun yi nisa a tafiyar Asiya sai kallon Ameena take yi tana so ta samo hanyar da zata bi wajan shirya sabon makirci yadda baza su kwana Lafiya ba, dan tana Lura da kallon da yake mata a gidan Ammah ya zama dole ta lalata musu daren. nan da nan wani abun ya shiga zuciyar ta tace, "Lah Aunty sauke ni a nan kije kawai zan shiga gidan Yayata sai ta kawo ni."

Ameena tace, "kodai na jira ki? Bakya ganin dare yayi zaki sha wahala kafin ki samu abin hawa?." Tayi dariya tace, "A'a kije kawai zan tawo." Ameena ta faka Asiya ta fita su kuma sukayi gaba. Tana fita Amira tace, " Wallahi Tunda ta shigo motar nan khamshin ta ya canja sai toshe hanci nake yi, dak'yar nake han numfashi wallahi duk da akwai a.c ga khamshin motar amma wari take. lallai Daddy yana fama."
Amman'a tayi dariya dan itama taji kawai ta basar ne bata ce komai ba, tunawa da Yusuf baya son wari sai Ameena tayi dariya a zuciyar tana aiyana ko ya zasu kwashe da ita dai oho.

Yusuf bai dawo da wuri ba dan har Zaytun tayi bacci   Sannan ya dawo, yana shigowa wajan Asiya ya shiga dan yayi mata sallama ya wuce wajan Ameena sai kuma da safe, abin mamaki bata ciki ya duba ko Ina bata nan ya fito nan ya lura da Momi kanwar ta a gefe har ta fara bacci ya k'arasa yace, "Momi!." Da hanzari ta tashi tana kallon sa alamun mai bacci yace, "Ina Asiyan?."
"Har yanzu bata dawo ba."
"Bata dawo ba?" Ya maimaita sai kuma yace, "Shiga ciki ki kwanta Ina zuwa" ya fad'a yana fita daga b'angaren ya shiga wajan Ameena.

           A falon tsakiya ya same ta tana shan ruwa ya kwantar da Zaytun kan kujera yace, "ya na ganki a nan ita kuma bata nan, ba tare kuke ba?." Ameena ta kalle shi tace, "wa kenan?."
"Asiya." Ameena tace, "bata dawo ba?." Da mamaki yake kallon ta murya a tausashe yace, "ni zaki tambaya bata dawo ba Ameena bayan tare kuke?, ba tare kuka tawo daga gidan Ammah ba?." Zatayi magana suka ji an bud'e gate ya karasa ya bud'e window ya hango Asiya wujiga-wujiga tana shigowa gidan ta zube a k'asa, juyawa yayi  ya sauka  ba tare da  yace komai ba ta kalli Asiya ta window din a bayyane tace, "ta kullo wani abun kenan, sai tayi ai daga ita har mijin basa gabana, komai ta shiryo a kanta zai k'are" ta fad'a tana gyara zaman labulen tagar ta bar wajan.

          Yusuf yana sauka wajan ta ya nufa yana fad'in, "Asiya lafiya kike?." Rik'o ta yayi suka mik'e zuwa cikin gidan ta suka shiga falo ya zaunar da ita ya bata ruwa yace, "Sha." Ba musu ta karba ta shanye tass yace, "ya akayi kika rabu? Daga Ina kike ke bayan tun d'azu su dawo?."
Chapter 25 · 0% Book details