Sashe 23
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi tayi kawai ta shiga d’aki ta kira Alhaji Bello a waya bai d’auka ba ba jimawa ya biyo kiran ta d’auka tace, “Ina ka ajjiye wayar Ina kira baka d’auka ba?.” Yace, “Yi hak’uri Fidy Ina aiki ne.”
“Albishir na kıra nayi maka.”
“Ina jin ki masoyiya.”
“Yau dai Abba ya tafi umrah, kuma ya bar komai a hannun Kawu dan haka kazo kawai a daura auren jibi jumu’a a wuce wajan. Kawu bashi da matsala nasan da kazo da batun shikenan.”
Cikin yanayin farin ciki taji yana cewa, “Da gaske kike baby? Kai amma naji dadi sosai, a safiyar nan zan taso daga Abuja na tawo Kano ayi komai na tafi dake. Kewar ki a Kullum kamar zata kashe ni haka nake ji, kai nayi farin ciki sosai.”
Yadda ya gigice ya bata nishadi sosai tace, “Kayi aikin naka yanzu, in ka gama mayi magana.”
“Ai in na gama na dawo ba wajan ki zan tawo ba wajan Kawu zanje kawai ayi a wuce wajan na gaji da zama babu ke.”
“Shikenan sai naji labari mai dadi” ta fad’a tana kashe wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane tace, “Da zarar an d’aura mana aure ranar a hannun y’an sanda Ibrahim zai kwana” ta fad’a tana girgiza kai domin tayi alqawarin tabbatar masa da ita ba matar da zai daka bace ya zauna lafiya.
A safiyar Ibrahim yana zaune suna ta hıra da Hajiya sallamar da akayi ne aka shigo ya saka shi mik’ewa tsaye wacce ta shigo ta kalle shi tace, “A’a d’an tsoho dan ka ganni kuma sai ka tashi?.” Yayi murmushi yace, “A’a daman zan wuce wajan aiki. Ina kwana.”
“Lafiya lau, ya aikin naka?.”
“Alhamdulillah.”
“Allah ya taimaka ya bada nasara.” Ya amsa da amin kafin ya kalli Hajiya yace, “Hajiya na tafi.”
Hajiya tace, “To Allah ya kiyaye ya bada abinda aka je nema.” Ya amsa da amin ya fita da machine d’insa. Wacce ta shigo ya bishi da kallo kafin ta kalli Hajiya tace, “Tunda yaron nan ya rabu da Fiddausi shikenan komai ya zama ma sha Allah. Ki duba yadda yayi kyau k’uruciyar sa ta bayyana da duk yana yawo a rame.”
Hajiya tace, “Bari kawai, ni kaina abin mamaki yake bani. Wallahi in kika alkhairin da ya samu bayan rabuwar su sai kin yi mamaki. Yanzu haka dubu goma ya bani kyauta yace nayi dinki.” Wacce take amsa sunan Suwaiba kanwar Hajiya tace, “ai naga alama wallahi, babu abinda zamu ce Allah sai godiya. Yanzu matar aure ya kamata a samo masa ya aura.”
Hajiya tace, “nima zuwa yanzu Ina so yayi auren ya wuce zama haka babu mata duba da akwai k’uruciya a tare dashi, watak’ila yana son yin auren kawaici da zurfin ciki irin nasa ne ya saka bazai fad’a ba, amma matan ne sai a hankali duba da halin Fiddausi na zahiri daban dana bad’ini. Ba kwarya bane balle ka kwankwansa Kaji mai k’wari a cikin su
“Ai ba kowa bane kamar Fiddausi, ba duka aka zama d’aya ba ai.”
“Haka ne, Allah ya had’a shi da matar da zai so ya aura mai hankali ko bazawara ce dan auren budurwa a yanzu akwai wahala, sai anyi ta tsarabe-tsaraben kashe kudi.”
Suwaiba tace, “Ni kuwa da zai amince akwai yarinya mai hankali da kyau kawai jinkirin aure ta samu har ta kawo wannan lokacin, amma hankali yarinyar nan tana dashi babu karya wallahi ga ladabi ko bata sanki ba ta ganki a hanya zata gaishe ki ba.” Hajiya tace, “A Ina take?.”
“Itama a Yakasai take dan gidan su dana Fiddausi ai babu wani nisa, Ina jin ma tasan Fiddausi sunan ta Rukayya yarinyar. Wallahi tana da hankali sosai Allah ne bai kawo mata miji ba har yanzu, ga mahifinta babban mutum na kirki gaba da baya.
Hajiya tace, “To Allah ya zaba abinda yafi alkhairi, in itace rabon sa Allah ya had’a su in ma ba ita bace Allah ya kawo wata mai alkhairi. Haka aka gano Fiddausi ma ai aka dinga murnar tana da hankali da ilimi sai gashi babu amfanin da sukayi a zaman auren ta.” Ta amsa da amin suka cigaba da tattaunawa akan abubuwan da suka shafe su.
B’angaren Yusuf k’arar wayar sace ta tashe shi daga bacci tun bayan fitar Ameena da yasha giya ya koshi ya baje yana bacci bai farka ba sai lokacin. Yamutsa fuska yake ya kalli agogo yaga lokaci ya tafi baiyi sallah ba ya zabura zai sakko daga kan gadon aka sake masa waya hakan ya saka shi ya kalli wayar ganin sunan Yayan sa ya saka shi ya d’auka ya saka sa kunne yace, “Yusuf kana Ina tun d’azu nake maka waya baka d’auka ba?.” Yusuf yace, “bacci nake yanzu na tashi.”
“To da ka shirya kazo gıdana yanzu nan Ina neman ka” to kawai yace ya katse wayar sai kuma kiran Abbah ya shigo.
Gaban sa ya fad’i sosai tunawa da yace ya kai masa sark’a gashi bai san inda take ba a haka ya d’auka yace, “Abbah barka da safiya.” Abbah yace, “Barka. Kana ji ka bar sark’ar a wajan ka yace sai nan da sati d’aya zai zo ya amsa basai ka fito da ita ba.” Ajiyar zuciya yayi yace, “To Abbah.” Daga haka Abbah ya yanke wayar shi kuma ya shiga bandaki.
A gaggauce yayi wanka ya fito ya saka kaya ya tayar da sallah bayan ya idar ya shirya sosai cikin manyan kaya wanda suka yi masa kyau ya d’auki makullin mota ya sakko zuwa k’asa. Shiru babu motsin kowa ga wuta a kunne ta ko Ina haske ne yasan kuma ba haka ta saba ba tana kashe komai ne sai tana wajan take kunna haske. Gaban sane ya fad’i hakan ya saka shi nufar d’akin ta da sauri yana shiga ya tarar bata nan.
Ya dafe kai a bayyane yace, “Ina taje kuma?.” Da sauri ya fito ya duba ko Ina bata nan kai tsaye ya shiga b’angaren Asiya. Yana shiga khamshin turare mai k’auri da wari ya daki hancin sa har sai da idanun sa ya tara ruwa saboda hayak’i da kuma kaurin turaren a bayyane yace, “Wannan wanne irin turare ne mai hawa kai?.”
“Asiya!” Ya fad’a da karfi ta fito a guje tana fad’in, “my love barka da zuwa.” Zata fad’a jikin sa yayi sauri ja baya domin tun kafin ta k’araso ya jiyo tashin da jikin ta yake yi ya kalle ta yace, “Wanne irin turare ne wannan mai hawa kai?.” Ta kalle shi tace, “hawa kai kuma? Ni banji ba.”
Yayi k’aramin tsaki yace, “Kinga Ameena ne da safen nan?.” Asiya tace, “tun dai dare da naji alamun za’a kunna mota sai na fita dan a zatona wani ne babu Lafiya na ganta tana shiga mota nace waye babu lafiya tayi min banza dana matsa sai ta fad’a min sai take masifa tana cewa ai nice silar komai Allah ya isa bata yafe ba ta shiga mota ta fita.”
Ya wara ido yace, “kina so kice tun dare ta bar gidan nan?.” Ta d’aga kai alamun eh ya dafe kai yace, “Ke kuma da yake baki da hankali shine baza kizo ki sanar dani ba…..?” Ya fad’a yana juyawa ya fita cikin tunanin inda zai ga Ameena ya bar Asiya a daskare a wajan tana tunanin lallai ya kamata ta canja shiri domin shirin nata baiyi aikin da take so ba ko kusa.
#Mai daki
#Book2
#Paid
#500
#Nana Haleema
Book2
015
Yana fitowa wayar Abie ya sake shigowa bai d’auka ba ya shiga mota kai tsaye ya nufi gidan sa dan bai san kiran da yake masa ba dole yaje yaji dalilin kiran. A harabar motar ya faka ya shiga cikin gidan da sallama ya same shi shida matar sa a zaune a falo yana shiga Abie yace, “tun d’azu nake jiran ka sai yanzu zaka zo?.” Ya karasa ya zauna yace, “ban san kana kırana ba, hankalina ne gabad’aya baya jikina. Ina kwana.”
“Lafiya lau” ya amsa yana kallon sa Yusuf ya kalli matar sa yace, “Ina kwana Aunty.”
Tace, “lafiya lau Yusuf, ya amarya?.”
“Tana nan lafiya.”
“Yaushe zaka kawo mana ita?.” Ya murmusa yace, “zata zo in sha Allah.” Ta mik’e tana fad’in, “Allah ya kawo ta” ta fad’a tana basu waje dan su tattauna.
Abie ya kalle shi yace, “Lafiya kake na ganka a rud’e?.” Yusuf ya kalle shi ya d’an yi ‘karamin tsaki yace, “Babu komai Lafiya lau nake.” Ya girgiza kai yace, “naga motar matar ka da daddare Jiya Ina taje ka bari ta fito ita kad’ai?.” Gaban Yusuf ya fad’i ya kalle shi ya bud’e baki kamar zaiyi magana sai ya fasa dan bai san abinda zai ce ba.
Abie ya girgiza kai yace, “Wallahi ban tabbatar da abinda Ammah take fad’a a kanka gaskiya bane sai yanzu, Yusuf in baka son yarinyar ka sake ta mana ka huta itama ta huta, wannan wahalar da kake bata duk ta meye?.” da sauri ya kalli Abie shima shi yake kallo yace, “Eh ka sake ta, wannan wahalar da kake bata in wani abun ya same ta wallahi baza’a kyale ka ba.” Yusuf yace, “Wallahi Abie ban san ta fito ba kuma har bayan ta nabi naje gidan Ammah akace min bata zo ba, shiyasa ka ganni a rud’e hankalina yana wajan ta wallahi, ban san inda take ba.”
Abie yace, “Hmmm! Shiyasa naga Ina ta kira kana bacci ko?.” Yayi shiru baice komai ba Abie yace, “Jiya da daddare mun fita a k’asa munje dubiya muka ga motar ta a nan gaba damu da alama yawo kawai take a titi ta rasa inda zata je, Umaima ce take fad’a min waccan motar Ameena ce nake mamakin abinda ya fito da ita da daddare muka k’arasa muka tabbatar itace daga ita har yarinyar da suke tare Amira da y’ar taka mai sunan Ammah kuka suke, sai Umaima ce ta karb’i tuk’in suka k’araso gidan nan. Yadda naga yanayin ta ya tabbatar min da abinda kayi mata ba ‘karami bane hakan ya saka ta baro gidan kana dare.”