Sashe 36
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asiya tace, “eh wallahi, kasan da yake nayi bak’i sosai da kayi tafiyar nan. A rana sai bak’i su zo sau goma haka akaita girki.” Kai ya girgiza yana kallon ta sama da k’asa yace, “yayi kyau” ya fad’a yana wuceta ya fita daga gidan ma gabad’aya ya koma b’angaren Ameena yana ji a ransa zaije ya bawa Yayan ta hak’uri ta dawo dan in bata dawo ba bai San ya zaiyi ba, dawowar ta shine jin dad’in sa ya tabbatar da hakan musamman yanzu da yake jin yunwa a yadda ya tarar da Asiya bazai iya cin abincin ta ba. A bayyane yace, “kiyi hakuri Ameena ki dawo, bazan sake miki komai ba. Ina sonki wallahi raina ne ya b’aci na fadi abinda na fad’a amma bawai dan haka abun yake ba.” Kallon falon yake a share tass ga khamshi ya lumshe ido ya bud’e yana tunanin yadda zasu kwashe da Yaya Adam dan yasan tun farko ba son sa yake da Ameena ba kawai dan tana son sane ya Bari akayi auren, Gashi yanzu an samu matsala a kan idanun sa ya tabbatar kafin ya hak’ura ya bashi Ameena a karo na biyu sai ya sha wahala sosai.
A bayyane ya sake cewa, “ko wacce wahala ce zan jure indai Ameena zata dawo gare ni, barın ta gidan nan babban gib’i ne a gare ni.” Band’aki ya shiga zuciyar sa cike da tnanin inda zai d’auko k’arfin guiwar tunkarar Yaya Adam da ita kanta Ameena d’in.
Book2
023
Kamar yadda Yaya Adam ya kira k’annen sa haka duk suka hallara a gidan tun safe babu wacce tasan dalilin kiran kawai sun ga Ameena a gidan basu kawo kuma komai ba sun d’auka yadda ya kira su haka ya kira ta. Dan basu San ma ya dawo ba wayar tasa ce ta tabbatar musu da ya dawo. Dukkan su sun hallara a babban falo yana zaune a kan kujera gabadayan su suna k’asa babu wacce tasan abinda zaiyi magana a akai ko wacce abinda yake zuciyar ta kenan.
Sai da ya bud’e taron da addu'a suka yiwa iyayen su addu'a sannan yace, "Nasan duk baku San na dawo Kano ba sai jiya da nayi muku waya, a daren shekaran jiya na dawo na kira ku jiya. Dalilin da ya saka nace duk kuzo yau wata magana nake so mu tattauna daku wacce zata amfani mu baki d’aya." Ya kalle su yace, "Tsakanin ku da Allah yaushe rabon da kuje gidan k’aramar qanwar mu dan kuga Lafiyar ta?” ya fad'a yana nuna Ameena da take zaune itama ya jingina kanta da jikin kujera.
Duk suka kalli Ameena suka kalli juna kafin d’aya tace, "ni naje lokacin da za'a yi mata kishiya amma kafin nan gaskiya rabona da gidan ta tun haihuwar Zaytun." Ya kalli Ameena yace, "Shekara biyu kenan ko?." Ameena ta d’aga kai alamun eh ya kalli sauran yace, "ku kuma fa?."
Daya tace, "Kwanaki hanya ta bi dani na shiga amma kafin nan nima tun haihuwar t." Yaya yace, "sauran ma basai kun ce komai ba kuma nasan tun haihuwar ne, amma ita bata zuwa inda kuke?." A tare suka had’a baki suka ce, "Tana zuwa." Yaya Sumayya tace, "tana zuwa gaskiya, dan ba'a jima sosai ba tazo gidana har la'asar tana nan."
Wacce take zaune kusa da ita tace, "nima anyi haka, ko bata zo ba zatayi mana magana ta WhatsApp a gaisa." Yaya ya girgiza kai yace, "Amma ku baku damu da kuje inda take ba saboda ba uwar ku d'aya ba ko? A haka kuna mijin ta yake baku zakka ki saka hannu ku karb’a ko?." Sai ya fusata ya fara fad’a cikin kakkausar murya yace, "Itace Autar gidan mu fa, itace mai ‘karamin shekaru a cikin mu, dukkan mu bamu da iyaye sun rasu amma meyasa bakwa tunanin a cikin mu itace marainiya bamu ba? Meyasa baku tab’a zama da ita kunce k’anwar mu ne yake damun ki ba?, saboda ba babar ku d'aya ba shiyasa kuka ware gefe a ganin ku wanda ake uba d'aya ba dan uwa bane ba ko?."
Jin yadda yake fad’a sai ko wacce tayi shiru sai Yaya Sumayya da tace, "Allah ya sani zuwan ta na k’arshe gidana na tambaye ta ko tana da damuwa ne naga ta rame sai tace min A'a sai na kyale ta." Kamar zai dake ta kuwa yace, "Dole ki kyale ta mana Tunda ba Jidda bace ko Zulaihat, inda sune ai baza ki kyale ba sai kin tabbatar kin San abinda yake damun su saboda su babar ku d'aya."
Dukkan su shiru sukayi ya sake cewa, "A ce yarinya k'arama babu wanda ya damu da lamarin ta a cikin ku saboda wata d'abi'ar banza da wofi da kuka saka a zuciyoyin ku, in baku kula da ita ba waye zai bata kulawa? Dukkan ku mata ne fa, kamata yayi ace kun jata jikin ku Kun nuna mata k'auna da kulawa saboda kasancewar ta k’arama a cikin ku amma baku yi ba. Ku duba yadda ta lalace ta rame saboda kawai babu mai kula da ita a tare da ita, duk gaku da yawa mata amma kun zama na banza da wofi tunda babu amfani, babu wanda zai tambaye ta damuwar ta, babu wanda zai kwantar mata da hankali, babu wanda zai rarrashe ta in tana kuka. Yanzu kenan da babu ni sai dai wata ran dukkan ku kuji labarin k’anwar ku ta mutu ko?."
Dukkan su jikin su yayi sanyi babu mai magana a cikin su ko wacce ta sunkuyar da kai ya sake cewa, "Yanzu in na fad’i na mutu kenan babu mai zumunci a tsakanin ku ko wacce sai dan d’akin su ta sani?, hakan a wajan ku shine daidai tsakani da Allah? Kun raina zumuncin dake tsakanin uba d'aya kenan ko?."
Yaya Sumayya tace, "Ba haka bane ba Yaya, kayi hak’uri zamu gyara in sha Allah. Tabbas munyi kuskure amma zamu daidaita komai in sha Allah."
"Kar ma ku gyara mana Sumayya, ku bar komai yadda yake Allah ya gani ai nayi iya bakin kokarina, kuma ni duka d'aya na d’auke ku babu wacce ta fi wata dan wai muna uwa d'aya da ita."
Yaya Saudatu tace, "Kayi hak’uri Yaya, in sha Allah zamu gyara." Yayan Bauchi ma tace, "Mun gane kuskuren mu in sha Allah zamu gyara, zamu bude’e group na WhatsApp yadda zamu dinga fad’awa junan mu damuwar mu koda bamu had’u ba, kayi hak’uri." Dukkan su hak’uri suka bashi sannan ya gamsu da yace, "Shikenan ai ya wuce, Allah ya had'a kanmu baki d'aya, ya jik’an iyayen mu." Duk suka amsa da amin kafin Yaya Sumayya tace, "Yaya meye yake damun Ameenah ne haka?."
Ya kalli Ameena da idanun ta suke a rufe tana kallon sama ya kalle su yace, "Damuwa ce tayi mata yawa itace ta mayar da ita haka, babu inda zata je ta fad’i abinda yake ranta, bata da kowa a kusa da zata fad’a masa damuwar ta shine ta koma haka." Kowa kallon tausayi yake yiwa Ameena dan ta rame sosai kafin Yayan Bauchi tace, "ta rame da yawa fuskar ta duk ta kumbura ."
Yaya yace, "Matsalar daga mijin tane amma zanyi maganin komai zai tabbatar da gatan Ameen ya dawo Kano, zai tabbatar da ni ba wanda ake tab’awa na kyale bane. Zai gano yayi kuskure da ni kuma yake zancen, an Ameena baza ta koma gidan sa ba na riga da na yanke hukunci." Sauran duk basu San me yake faruwa ba hakan ya saka basu da tacewa Yayan Bauchi tace, "ina bayan ka Yaya, kar ka bari ta koma in ba haka ba wata ran gawar Ameena zamu d'auka a gidan sa.”
Ya kalle ta ya harare ta yace, "kema ai kin bani haushi, in ita bata fad’a min ba kema sai ki yi min shiru ki k’i fad’a min abinda yake faruwa bayan kin san nine kawai zanyi maganin abun?. Ai hankalin ku ba d’aya ba, in ita tayi shiru ke bai kamata ace kin yi shiru da maganar ba, amma sai kika yi min shiru baki ce min komai ba.”
"Kayi hak’uri Yaya, amma wannan karon kar ka kyale Yusuf dan Allah." Mik’ewa tsaye yayi yace, "bai san waye ni bane shiyasa, kar na dawo gidan nan da daddare naga wata ta kai dare ko wacce ta tafi gida, ke ta nesa gobe ki shirya ki bar Kano. Ku karbi sak’o a wajan Aisha" yana fad'a ya fita suka yi godiya kowa ya koma kallon Ameena kafin su dinga janta da hira wai ko zata sake ayi hira damuwar ta bar zuciyar ta.
Yaya Adam mahaifin Yusuf ya kira a waya ya sanar dashi zuwan sa da daddare in yana nan ya tabbatar masa da yana gida yana kuma jiran sa sannan ya kashe wayar ya fita zuwa wani waje daban. Sai bayan sallar i’sha sannan ya nufi gidan su Yusuf, a k’ofar gidan su ya tsaya ya sanar da mai gadi zuwan sa aka shiga ana fad’awa Abbah ya bada izinin shigowar sa sannan ya shiga ciki.
A zaune ya samu Abbah da y'an uwan Yusuf maza har ma da Yusuf d’in ma da alama an shigo gaishe su ne ya shiga da sallama suka amsa fuska a sake Abbah cikin zolaya yana cewa, "Soja mazan fama, barka da zuwa." Murmushi yayi ya gaida Abbah cikin girmamawa suka gaisa da kowa kafin ya zauna. Abie yace, "Abbah tunda kayi bak’o bara mu wuce mu."
Yaya Adam yace, "A'a ku zauna daman dukka nake so mu had’u mu tattauna, inda hali ma a kira Hajiya itama tazo." Abie ya kalli Adam wanda zasu yi sa'a shida shi yace, "lafiya dai?." Ya kalli Yusuf da kansa yake a sunkuye ko motsi ya kasa ya kalli Abie yace, "Gaskiya ba Lafiya ba, shiyasa nake so a had’a kowa da kowa a nan in hakan zaiyu."