Sashe 8
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru yayi bai amsa ba ransa y sake b'aci akan abinda Ameena ta aikata ta sake cewa, "Tunda ta d'auki wayar a raina nasan itace saboda nasan in ba ita ba babu wanda zai d'auki wayar ka, bata fara magana ba sai da na gama magana na d'auka kaine hakan y saka na ambaci my love da nasan itace da bazan fad'a ba kodan gudun b'acin rant. Da tayi magana na d'auka zamu gaisa ne ko babu komai y'arr uwar tace ni a yadda na d'auka ba kishiya ba ashe a wajan ta ni kishiya ce. Wani zagin ban tab'a Jin irin sa ba a rayuwata!" Ta fad'a tana Jan numfashi tare da goge idanun ta.
"Ya isa haka ki yi hak'uri ki daina wannan kukan" ya fad'a a sanyaye yana kallon ta. Ta kalle shi tace, "Na fara jin tsoron auren ka my love, Allah ya sani bana son tashin hankali musamman tsakanin kishiyoyi. In hakan zai jawo matsala gwara na hak'ura dakai na bar mata......" kafin ta k'arasa ya katse ta yace, "Akan me? Saboda ita? Ke kina ganin ko ke kin hak'ura ni zan hak'ura ne?. Ki bar wannan maganar bana so domin bazata yu ba."
"Nidai ka bata hak'uri dan Allah, ban fad'a maka dan na 'bata maka rai ba, na fad'a ne d'azu saboda raina ya b'aci kuma saboda ka yiwa tukfar hanci kafin shigowa ta gidan ka. Kaga in tana fad'a min Ina yin shiru watarana bazan yi shiru ba sai dai kazo Kaga Muna dambe hakan kuma kai zai tayarwa da hankali."
Kai ya girgiza yace, "Haka ne, kar ki damu na gode da kulawar ki a gare ni, ke mai son kwanciyar hankalina ce na san da hakan. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru kinji?." Kai ta d'aga tayi murmushi shima yayi yace, "Har naji dad'i da gabad'aya kin tayar min da hankali."
"To ka tashi ka tafi dare yayi kar nayi wani laifin a wajan ta."
"Kawai korata kike."
"Ni na isa? Kawai dai bana son shiga hakkin tane."
Tashi tsaye yayi tare da yin murmushi yana kallon ta yace, "Wani dare nake jira irin na yau wanda baza kice na tafi dare yayi ba." Murmushi tayi ta tashi tsaye tace, "nima haka my love." Murmushi yayi itama tayi suka yi sallama daga wajan ya tafi. Yana fita ta saki darıya tare da tafa hannu tace, "Yanzu aka fara Ameena, sai kin bar gidan Yusuf da k'afar ki wallahi, domin Yusuf nawa ne ni kad'ai wallahi, baki isa nayi kishi dake ba" ta fad'a tana shiga cikin gida.
Yusuf yana komawa kai tsaye dakin Ameenatu ya nufa ransa a b'ace sosai ji yake kamar a lokacin ma abin ya faru ya same ta a falon ta na sama a zaune tana kallon tv, yadda aka turo k'ofar sai da taji tsoro ta kalle shi shima ita yake kallo yama rasa ta inda zai fara. Ransa a b'ace yake so yake ya tabbatar mata da hakan shiyasa yayi shiru yana so ya samo abinda zai fad'a mata wanda itama zata ji abinda yake ji.
Ganin baiyi magana ba itama sai tayi shiru ta mayar da hankalin ta kan tv din kamar bata san yana wajan ba sai a sannan yace, "Ke wai duk abinda zuciyar ki ta raya miki a ganin ki shine daidai?." Kallon sa tayi so take taga in a buge yake yasha giyar sa ta tattara ta gudu dan bazai jibge ta a banza ba.
"Ba magana nake miki ba!?" Ya fad'a cikin tsawa. Ta kalle shi ta tabbatar a hankalin sa yake tace, "Ban San abinda nayi ba ai shiyasa."
"Okay baki sani ba ko? Zagin wacce zan aura da kika yi duk baki san kin yi ba ko?."
"To naga d'azu kayi min masifar a gaban k'awata me ya sake dawo da ita yanzu?." Idanu ya wara yana kallon ta yana takowa inda take yace, "Masifa? Nine masifaffen?."
Ameena tace, "Naga ai ya wuce ko?."
"In ke a wajan ki ya wuce a wajena bai wuce ba, domin tana da mahimmaci a rayuwa Ina sonta dan son da nake mata zan kawo ta gidan nan, in ma bak'in ciki kike da hakan ya kamata ki ajjiye ki sauke shi domin babu abinda zai hana ni aure ta."
"Daman kaji nace zan hana ka ne? Nasan ai ban isa na hanaka ba, ko sanda kace min zaka aure ta saboda tausayi ne ni nasan ka fad'a ne dan na shiga maganar a wajan Amma ba wai dan hakan bane a zuciyar ka, Ko mata uku zaka k'aro suzo mana Allah ya kawo su lafiya ai ba a kaina zasu zauna ba" ta fad'a a tausashe tana mik'ewa da niyar barin wajan.
Hannun ta ya rik'e ta baya ta lumshe ido Jin d'umin hannun sa a jikin ta ba ta hanyar duka ba yace, "Ni kike fad'awa ko mata uku ne na kawo?." Ta zame hannun ta daga hannun sa ta kalle shi tace, "Eh mana, saboda ban isa na hana ba gwara ka kawo su din kowa ya huta."
"Lallai raini ya fara shigowa tsakanin mu kenan, har abin ya kai ina fad'a kina mayar min da magana Mara dad'i Ameena?" Ya girgiza kai yace, "amma kar ki damu zan goge rainin nan gaba ko ance ki fad'a min baki isa ba ki fada ba."
Tayi murmushi tana kallon sa bata ce komai ba shima ita yake kallo sai kuma yaja tsaki ya bar wajan ta shiga d'aki itama ta kulle kofa ta jawo akwati ta fara zuba kayan ta dana Zaytun domin safiya tana yi zata wuce Bauchi ta gaji da abubuwan da Yusuf yake mata tana shanyewa, gwara ta bar masa gidan yayi duk abinda yake so dashi.
K'arfe bakwai na safe ta sauka da jakar dan ta tabbatar bacci yake duk wani abu nata wanda tasan zatayi amfani dashi ta d'auka ta saka a bayan mota ta rufe, ta bud'e gaban mota ta ajjiye Zaytun da take bacci ta shiga mazaunin driver ta zauna tana kallon gaban ta tare da sauke numfashi, bata tab'a jan mota zuwa wani gari ba koda a cikin garin Kano ne balle kuma wajan Kano, amma a jikin ta take jin zata iya da dai ta zauna a gidan ya kashe ta gwara ta tattara ta bar masa gidan ya huta. Da wannan tunanin tayi addu'a ta yiwa motar key mai gadi ya bud'e mata ta fita daga gidan.
A safiyar Abban su Fiddausi ya dawo daga qauye bayan ya huta ne da yamma Kawu yazo ya same shi da maganar Alhaji nan da nan ransa ya b'aci ya saka aka kira Fiddausi yana ta fad'a akan hakan, lokacin da ta shigo ta zauna gaban ta fad'uwa kawai yake musamman da taga Kawu ya tabbatar maganar ce ya kalle ya yace, "Kawun ki yazo min da wata magana yanzun nan, abinda nake so naji shine daman shi Alhajin kuna tare dashi ne tun kina gidan Ibrahim?." Da sauri ta girgiza kai alamun A'a tana jin wani iri a jikin tace, "Ban San shi bama ni."
"To ya akayi yasan auren ki ya mutu kuma babu idda a kan ki? Ko kina so kice min a radio aka sanar da hakan?."
"Wallahi Allah ban sani ba" ta fad'a a bayyane a zuciyar ta tana karanto istigifari.
"Gaskiya akwai alamar tambaya a lamarin nan naki, meyasa wasu basu zo ba sai shi? Ya akayi ya sanki ya san auren ki ya mutu da ciki kuma yanzu babu cikin?." Shiru bata amsa ba tsoro duk ya mamaye mata zuciyar ta.
Abba ya kalli Kawu yace, "Akan me zaka bashi damar da zai zo yau ya ganta? Sai kace jira ake yi auren ta ya mutu a fara neman auren ta?." Kawu yace, "Nima nayi wannan tunanin Yaya, amma sai na tuna babu idda a kanta a yanzu."
"To dan babu idda a kanta daga mutuwar auren ta sai tayi wani auren kamar daman plan aka shirya? A Bari ta cike kwanakin iddar mana in yaso ranar da ta cika ma sai tayi auren ba damuwa ta bane, amma yanzu abin sam babu tsari kafin duniya tayi da kai kayi da kanka."
Mama da take wajan tace, "Amma ba haram aka aikata ba ai tunda babu idda a kanta." Abba yace, "Na fiki sanin ba haram aka aikata ba ai, amma ban amince a fara zuwa wajan ta da neman aure ba sai nan da wasu kwanaki, sai lokacin iddar ta ya cika sannan na amince wani yazo da wani batu na aure. shi kuma zan saka a bincika min shi duk da sanannen ne a bangaren kasuwanci amma tarihin sa da asalin sa da komai ba'a sani ba."
Ya kalli Fiddausi da kanta yake k'asa yace, "Tashi kije, kar ki saurare shi sai nan da wani lokaci nasan ba idda kike ba amma hakan nake so ayi. Ke bama shi ba indai ba Ibrahim tsohon mijin ki ba ban amince ki saurari wani a yanzu ba." Ta amsa da to ta fita tana ji yana yiwa Kawu d Mama zuciyar ta a cushe kamar ta kurma ihu haka take ji. Mama na shigowa falon ta mik'e tsaye tace, "Mama zanje gidan Yaya."
Mama ta kalle ta tace, "Me ake yi?."
"Babu komai."
"Sai kin dawo" ta fad'a tana shiga d'aki ita kuma ta saka hijjabi ta tafi.
Gidan yayar tata ta fara zuwa bata jima ba ta fita ta nufi gidan Zakiyya bayan ta yi masa waya in yana da lokaci yazo su had'u a gidan Zakiyya. Tana shiga ta cire hijjabin ta Zakiyya da take zaune tana Shan abu a kofi ta bita da kallo tace, "Malama saka hijjabin mijina bai fita ba."
Fiddausi tace, "amma na cewa Alhaji yazo nan."
"Yanzu zai fita ai." Motsin sa taji ya saka ta saka hijjabi ya fito suka gaisa yace, "Naji abu mara dadi a wajan Zakiyya, Allah yasa hakan ya zama alkhairi." Tayi murmushi tace, "Amin ya Allah daddyn Fahad, na gode." Ya kalli Zakiyya yace, "na wuce." Tabi bayan sa ta raka shi har ya fita kafin ta dawo.