Sashe 35
Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayar tace ta d’auki k’ara ta katse mata tunani ta duba taga lambar k’asar waje ce kamar yadda Fiddausi ta saba kiran ta tayi murmushi ta d’auka a bayyane tace, “Amaryar Alhaji Bello.” Fiddausi daga can b’angaren tace, “Fadi ki k’ara fad’a amarya nake wallahi.” Sukayi dariya a tare Rukayya tace, “ya New York din?.”
“Bari kawai Ruky, Allah jina nake kamar sabuwar halitta komai ya canja. Kud’i sunyi ta ko wanne b’angare.”
Rukayya tace, “Yayi kyau hajiyata. Allah yasa an samo mana babyn New York.”
“Ke akayi ciki yanzu ai harka ta lalace, kina ji ni kiran ki nayi neman alfarma Allah yasa zaki min.”
“Wacce alfarma?.”
“Wallahi kwana biyu mafarkin Ameer nake yi, dan Allah kije gidan su Ibrahim ki had’a ni dashi a waya mu gaisa sai ki dawo. Dan Allah kar kice a’a ke kadai nake da ita da zaki iya yi min. Nasan Hali yanzu sai kice baza ki fita ba ki taimaka dan Allah.”
Rukayya tace, “Gidan su Ibrahim da kika ce? To ni zan gane gidan ma balle naje zanje?.” Fiddausi tace, “Zan miki kwatance dan Allah kije in kin kije sai ki kira ni WhatsApp call.”
“Anya zan iya zuwa kuwa Fidy?, a wanne matsayi zan shiga gidan su yanzu?.”
“Matsayin babar Amir mana, dan Allah kije, zan turo miki kud’i yanzu ki dan siya masa chocolates da dan biskit ki kai masa.”
“To bara na tambayi Umma in zata barni.”
“Yauwa tambaye ta kar ki kashe, ko ki bani na tambaye ta da kaina.”
Wayar na kunnen ta ta isa d’akin Umma tace, “Umma.” Ta amsa da Na’am tana kallon ta tace, “Fiddausi ce zaku gaisa.” Umma ta karb’i wayar ta saka a kunne suka gaisa da Fiddausi kafin tace, “Dan Allah Umma ki bar Rukayya taje ta gano min d’anta Amir ta had’a mu a waya wallahi kwana biyu mafarki sa nake kar naje ko bashi da lafiya.” Umma ta kalli Rukayya tace, “Babu komai Fiddausi zata je ai itama dan tane.” Fiddausi tayi godiya Umma ta mik’awa Rukayya wayar ta kashe Umma tace, “Kije kiyi sauri ki dawo, daman ai ya kamata ace ana duba shi duk da yana hannun baban sa dan anje duba shi ba wani abun bane. Kema babar sace ai” ta fad’a tana tashi daga inda take zuwa gaban madubin d’akin.
Sai bayan la’asar sannan Rukayya d’auki hijjabi ta saka ta d’auki wayar ta nan taji shigowar kud’in da Fiddausi ta saka mata sai ta d’auki atm ta fita dashi. Store ta fara shiga ta siyi abinda tace ta siya masa sannan ta nufi gidan da tayi mata kwatance haka kawai take ji gaban ta yana fad’uwa.
Da tambaya aka nuna mata gidan ta shiga da sallama mata guda biyu suka amsa daga cikin falon ta shiga, a guje Amir yayo wajan ta yana fad’in, “Aunty Rukayya.” Ta rik’e shi tana murmushi kafin ta zauna ta kalli Hajiya da wacce take kusa da ita tace, “Barkan ku da yamma.” Wacce take kusa da Hajiya ta amsa tana fadin, “Rukayya daman kin san gidan nan ne? Naga Amir ya d’afe ki yana murna.”
Rukayya tayi murmushi ganin wacce ta saba zuwa gidan su wajan Umma tace, “Lahh Aunty nasan gidan duk da nasan yau aka fara ganin fuska ta.” Hajiya tace, “ina ta tunanin inda dai na sanki.” Ta sake yin murmushi tace, “Ni k’awar Fiddausi ce.” Hajiya tace, “Allah sarki.” Wacce take kusa da Umma tace, “Daman kin San Fiddausi?.”
“Sosai ma kuwa.”
Rukayya ta sake cewa, “itace ta kira ni tace dan Allah nazo na m had’ata da Amir a waya.” Amir da yake jikin ta yace, “ni ki tafi dani wajan Mama na ina so na ganta.” Rukayya tace, “Yanzu zaku fara yin waya in na sake dawowa sai muje ko?.” Kai ya d’aga tayi dariya ta d’auki waya tayi kamar yadda tace ta d’auka ta bashi wayar ya saka a kunne ya tashi a guje ya shiga d’ak.
Da sallama Ibrahim ya shigo falon suka amsa duka ganin Rukayya sai yayi murmushi yace, “Rukayya kece a gidan namu?.” Murmushi tayi tace, “Eh wallahi, ina wuni.” Ya amsa gaisuwar yace, “kin kyauta” daga haka sai ya fita. Tana zaune shiru bata iya cewa komai har Amir ya fito ya bata wayar ta d’auki ledar ta bashi tace, “ga alawa kaje kayi ta sha.” Ya karb’a yana tsalle sai yace, ni ke zan bi mu tafi.” Ta wara idanu tace, “Ai Maman naka bata nan Amir.” Ganin kamar zaiyi kuka tace, “Kana ji, ka kwantar da hankalin ka tana dawowa zan zo na d’auke ka kaje wajan ta kana so?.” Ya d’aga kai alamun eh tayi murmushi tace, “to kar kayi kuka mana.” Sai yayi dariya ta bashi hannu tace, “to mu tafa.” Sai kuwa suka tafa tayi dariya sosai ta kalli Hajiya da yake kallon ta da murmushi tace, “ni zan koma Mama.”
Hajiya tace, “ke kuwa ko ruwa baza ki tsaya ki sha ba?.”
“Sauri nake yi ne bana so magriba tayi min a hanya.”
“To mun gode sosai, ki gaida mutanen gidan” ta amsa da in sha Allah ta fita daga falon.
Tana fita Mama Suwaiba ta cewa Hajiya, “Itace yarinyar da nake fad’a miki, ke kanki nasan kin shaida nutsuwar ta da hankali ko? Dan naga sai kallon ta kike kina murmushi.” Hajiya tace, “wallahi lokaci d’aya naji ta shiga raina, ga fara’a da hankali gata kyakykyawa har tafi Fiddausin kyau.”
Mama Suwaiba tace, “tana da shiga rai saboda akwai nutsuwa sosai ma sha Allah. In naje gidan su baza kice tana nan ba saboda bata da hayaniya ko kad’an. Yadda suke wasa da Amir suka saba haka sai na sake yiwa Ibrahim sha’awar auren ta wallahi.” Hajiya tace, “to babu wanda dai yasan abinda Allah ya b’oye sai dai mu zuba ido kawai muga yadda zai yi damu.” Mama Suwaiba tace, “haka ne. Nima bara na gudu zan lek’a gidan rasuwa daga nan zanyi gida.” Hajiya ta amsa mata sukayi sallama ta fita.
Tana fita Ibrahim ya shigo ya tarar da Amir yana ta shan chocolate yana kallon sa yace, “Abba kaga abinda Aunty Rukayya ta kawo min.” Yayi murmushi yace, “an gode.” Hajiya ya kalla bayan ya zauna yace, “Yunwa ce ta dawo dani nazo na ganki da bak’i.” Hajiya tace, “eh wallahi, tazo duba Amir ne wai babar ce tace tazo ta bashi waya su gaisa, ashe kasan yarinyar?”.
Ya kalli Hajiya yace, “Wai Rukayya? Na santa farin sani ma Hajiya. Ai tana daga cikin aminan Fiddausi dan tare duk sukayi makaranta.”
“Allah sarki, ni wallahi nutsuwar ta ta burge ni sosai, Gashi sun saba da Amir.”
“Gaskiya babu laifi, a lokacin baya in tazo gidan mu ina ji takan yiwa Fiddausi fad’a akan abinda take yi.”
Hajiya tace, “kuma budurwa ce ko tana da aure?” Ta tambaya kamar bata sani ba. Ibrahim yace, “Gaskiya bata da aure amma ban san ynzu ba.”
“To Ibrahim mai zai hana baza ka aure ta ba?.” Gaban sa ya yanke ya fad’i ya kalli Hajiya da sauri da kuma mamaki yace, “Hajiya na aure ta fa? Na fad’a miki k’awar Fiddausi ce fa.”
“Dan k’awar tace sai me Ibrahim? Ai ba k’anwar ta bace ba ko?.”
“Eh haka ne, amma dai gaskiya bana jin hakan a raina ko kusa.”
Hajiya tace, “ko itama halin Fiddausin ne da ita?.” Ibrahim yace, “Taya zan sani Hajiya; nida ban zauna da ita ba?.” Hajiya tayi murmushi tace, “Nidai zuciyata ta amince da ita wallahi, in rabon kace Allah ya baka.” Kallon Hajiya yayi haka kawai baice komai ba ya samu zuciyar sa da harbawa sosai sai kawai ya tashi ya tsaye ta kalle shi tace, “ya ka mik’e? Abincin fa?.” Yace,”in n dawo zanci.” Abinda yace kenan ya fita Hajiya tayi dariya kawai ta cigaba da abinda yake gaban ta.
Yusuf kuwa wunin ranar a gida ya yishi ya kasa fita ko ina dan gabad’aya wani iri yake jin sa gashi babu dama a kira shi a waya sai gaban sa fad’i sai ya d’auka Ammah ce take kiran sa ta samu labarin abinda ya faru. Yana zaune a b’angaren Asiya a falon kasa gabad’aya baya jin dad’in zaman saboda wani irin khamshin gidan yake masa kamar na kayan wankin da suka jima a ajjiye ruwa ya tab’a su.
Tunawa da akwai abinda ya ajjiye sai ya tashi ya shiga kitchen d’in Asiya, a share yake amma k’udaje sunyi yawa a ciki yayi tsaki ya kulle tagar kitchen d’in ya bud’e store d’in kitchen din ya shiga. Neman abinda ya ajjiye yayi can ya hango shi wani k’aramin k’arfe ne na motar sa ya d’auka har zai fita sai ya dawo da baya yana kallon store din ganin babu kayan abincin ga shinkafa da take buhu uku a ajjiye Saura buhu d’aya itama kuma an bud’e.
Mamaki abin yayi sai ya fito akwai ya hau sama d’akin sa, clashing sukayi da ita zata fito daga d’akin nasa shi kuma zai shiga yaga duk ta diririce kamar mara gaskiya ya bita da kallo ta koma da baya ya shiga yana kallon d’aki wai sunan a share amma kana taka kafar ka zaka ji k’asa. Tace, “my love daman wajan ka zanje.” Kallon ta yayi rigar jikin ta daban siket d’in ma haka yace, “gani ai” ya fad’a yana wucewa wajan drawer ya saka k’arfen da ya tawo dashi.
“Kabi bayan Aunty Ameena kuwa?.” Jin abinda tace sai ya kalle ta kamar zai ce wani abun sai ya fasa tace, “dan Allah kaje ka dawo da ita koma meye mu Mun yafe, wannan abun ai bai kai ace anyi saki ba my love.”
Da mamaki yake kallon ta yace, “Ce miki akayi na sake ta ne?.” Ta kalle shi tace, “nima bana fatan hakan kawai ina so kaje ne ka dawo da ita, mu zauna lafiya shine fatana.”
Baice komai ba ya sake kallon drawer din yace, “kamar na ajjiye kudi a nan ko?.” Gaban ta ya fad’i amma sai ta maze tace, “kudi kuma? Yaushe kenan?” Ta fad’a tana k’arasowa wajan tana dubawa amma babu komai a wajan. Yusuf yace, “bana ce ga ranar ba, shikenan nan dai. Naga abincin store yayi k’asa sosai.”