← Book details Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 42

Sashe 1

Mai Daki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Book 2
001

Luuuu ya tafi zai fad’i Yaya Sulaiman yayi saurin taro shi yana fad’in, “Ka k’arfafa jikin ka Ibrahim; meye ribar zama da irin wannan matan masu son ganin bayan mazajen su saboda wani dalili wanda suka barwa kansu sani? dan ka rabu da ita shine zai saka ka fad’i?, to ka sani in ka samu ciwo kanka da d’anka ka cuta ba ita ba. Wuce muje chemist a gyara ciwon nan kafin cuta ta shiga.”

Shi dai Ibrahim jin komai yake yi a sama kamar baya cikin hankalin sa kamar kuma a mafarki, in ya tuna kalmar saki da ya furta akan Fiddausi sai yaji jiri na sake d’ibar sa kamar zai kifa. Koda wasa bai tab’a kawowa wannan ranar zata zo ba, ya d’auka rabuwar aure shida Fiddausi sai dai mutuwa. “Abba mu tafi kar Mama ta sake yanke maka hannu” Amir ya fad’a yana jinjiga hannun Ibrahim da shi ya manta ma dashi gabad’aya a kusa dashi.

Dakyar ya iya jawo k’afa ya fita ya samu Yaya har ya samu kwandon da za’a kulle gidan a maqota yana fitowa ya kulle gidan suke sake shiga ‘karamar motar Yaya suka tafi. ‘Karamin chemist suka tsaya aka gyara masa hannun bayan an masa allurar TT daga nan suka wuce gida kowa zuciyar sa babu dad’i, shi dai Ibrahim jin sa yake kamar ba shi ba dauriya kawai yake yi.

Suna shiga gidan Alhaji yana zaune a ‘kofar d’aki sun gama tattauna batun Ibrahim din kenan yana sauraren labaran karfe takwas na dare ya bisu da kallo ganin hannun Ibrahim a d’aure ya kalli Hajiya itama ta kalle shi kafin yace, “Lafiya kuka dawo? Kai ya same shi a hannun kuma?.” Kafin suyi magana Amir yace, “Mama ce ta yanki Abba da wuk’a jini yana ta zuba.” Yaya ya kalli Sadik da yake zaune a gefe yace, “Dauki Amir kaje ka siya masa Alewa.”

Ba musu ya tashi ya rik’e hannun Amir suka fita shi kuma ya zauna Ibrahim ma ya zauna. Hajiya tace, “Ban gane me Amir yake fada ba, da gaske itace ta yanke shi?.” Yaya ya girgiza kai alamun eh kafin yace, “Badan Allah yasa dani muka je gidan ba da wallahi zata iya kashe Ibrahim kamar yadda tace. Idanun ta ya rufe sai maganganu take yi na banza da wofi, ita bazata iya zama da talaka ba, ta gaji da rayuwar talauci, sabuwar rayuwa zata fara, maganganu dai kala-kala. Kana ji kasan daman ta shirya wani abun ne ya saka take yin duk abinda take yi.”
“Innalillahi wa’inna ilahiri raji’un! Yanzu akan wannan dalilin taso kashe shi? Ko kuma tana da wani dalilin mai k’arfi?.” Hajiya ta fada a gigice tana kallon sa.
“Haka kawai fa Hajiya, na fahimci kawai saki take so akwai wani abun da take hange ta gaji da zama da İbrahim kawai saki take nema. Duk abinda ta fad’a d’azu a gidan su ‘karya take yi kawai bata son zama dashi ne.”

Alhaji da mamaki ya gama mamaye shi yace, “A gaban idanun ka da d’anta Amir ta d’auki wuk’a ta yanke masa hannu haka?.” Yaya yace, “Sabida idanun ta ya rufe ko ganina nida Amir bata yi ba, kawai tayo kansa da wuk’a ne tace in bai sake ba wallahi sai ta kashe shi. Tana cewa ta gaji da zama da talaka mara amfani ta gaji da rayuwar talauci.”

Hajiya tace, “Sai da na fad’a tun farko a raba auren nan amma Alhaji yak’i, yanzu badan kana nan ba da me zai faru?.” Yaya ya numfasa yace, “Ai sai dai Alhaji a gafarce ni dan na saka shi ya mata saki daya, a lokacin in ba sakin ta yayi ba wallahi ba’a san me zai faru ba, dan har ni zata iya had’awa ta cakawa wuk’ar Tunda babu wanda yasan ta aikata. Zata iya bankawa gidan wuta su kune dukkan su.”
“Kayi daidai, abinda ya kamata ayi kenan, ai ba y’ar gwal bace da za’a dinga riritata kamar wata yarinyar goye. Yarinyar da tazo har har gabana tace bata son sa aka tilasta mata zata kashe shi daman meye amfanin ta?, ai ko mutuwa na kunyar Idon mahaifi, amma ta shafawa idanun ta toka tazo ta same ni tace wai ya sake ta bata son sa” Hajiya ta sake fad’a rai a b’ace kana ji kasan maganar tayi mata ciwo sosai.

Alhaji yace, “Ai shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, in da yuwar zata dawo Allah ya daidaita su in babu kuma Allah ya had’a kowa da rabon sa.” Hajiya ta amsa da amin tana kallon Ibrahim da ya saka cewa komai sai jinginar da kansa da yayi jikin bango idanun sa a kulle shi kad’ai yasan abinda yake tunani. Yana son Fiddausi Allah y sani amma ba rabuwa da ita bane yake d’aga masa hankali, mamakin sa da gaske daman zata iya kashe shi akan wani abu na duniya?.

Hajiya ta sake cewa, “A gaban d’ank ka dinga hauka kamar mara ilimi, ilimin addinin nata da akayi kwad’ayi aka auro ta bai amfana mata da komai ba, bata aiki dashi da ita gwara wata wacce bata zauna a makaranta ba daman kasan tun farko bata je makarantar ba, ita kuwa fa?.” Shiru yayi baice komai ba kafin Alhaji yace, “ya isa haka, Kiyi hakuri dan Allah.” Shiru kawai tayi tana girgiza kai cikin k’unar rai, Yaya Sulaima mik’e yayi musu sallama ya tafi shima Ibrahim bai ce komai ba ya tashi ya fita dan yana buk’atar shan iska ko zai ji dadi zuciyar sa a cushe take.

Yadda Fiddausi ta shiga gida sai ka d’auka zaki ne ya biyo ta ko kura, yadda ta fad’o tsakiyar gidan kamar mahaukaciya sai hakki take ga marar ta da take mata ciwo mat’uka hakan ya taimaka wajan sake gigicewar ta. Hankali tashe kowa yake tambayar ta Lafiya ta zube a wajan tana fad’in, “Ya sake ni, ya sake ni Mama, Ibrahim ya sake ni…..” sai tayi luuuu ta zube a wajan jini ya fara zuba daga jikin ta.
Bata san me ya faru ba ta dai fara jiyo magana a kanta sama-sama kafin ta daina jin komai idanun ta ya rufe ruff duhu ya mamaye mata idanun ta.

Ameenatu tana zaune ita a kad’ai tun bayan tafiyar kawayen ta kamar ko yaushe Zaytun tana kan cinyar ta tana wasa ita kuma ta zubawa waje d’aya ido tana kallo kamar mai son ganin wani abun a bangon amma babu abinda take gani kawai damuwar da take ranta ce tayi yawa.

Bata san ma Yusuf ya zo wajan ba hankalin ta ya tafi wajan tunani bata ji maganar da yake yi a waya ba balle kuma takun takalmin sa, kallon ta yayi ganin ya mata magana bata ji ba hakan ya saka ya daki kujerar da take kai yace, “Bakya ji ne?.” Zabura tayi ta kalle shi kamar yadda yake kallon ta zaiyi magana yaga Zaytun na mik’a masa hannu tana kiran Daddy.

D’aukar ta yayi daga jikin Ameena ya d’aga ta sama yana yi mata wasa tana darıya shima yana dariya, tana hannun sa ya sake kallon Ameena wacce take kallon abinda ya shigo dashi saitin manyan akwatina ne wata a cikin wata baza ta banbance guda nawa bane amma kai da gani kasan suna da yawa a ciki dan yanayin babbar ta farko zai tabbatar maka da wanda suke binta suna da yawa. Kallon abinda take kallo yayi y sake kallon ta yace, “kin yanke shawarar abinda kike so?.”

Had’a ido sukayi bata janye nata idanun ba shima haka ta girgiza kai alamun A’a tace, “Ban yanke komai ba.”
“Bakya so ne hala?.” Shiru tayi bata amsa masa ba ya tab’e baki jin bata amsa ba d’auke kai daga kallon ta yace, “Ba haifata kika yi ba balle na dinga binki Ina lallab’a ki dan na samu lada ba, in kin karb’a kanki, in baki karb’a bama ba damuwana bace. Karb’ar ki da rashin sa wannan ke ta shafa, hakan bazai canja komai ba.”

Murmushi tayi bata ce komai ba ya kalle ta yana mamakin dalilin murmushin yace, “ki kawo min abinci sama” ya fad’a yana niyar tafiya bayan ya tura akwatinan gaba.
“Ban yi girki ba” ya jiyo maganar ta daga bayan sa ya juyo ya kalle ta yace, “Wai ke wanne irin iskanci kika fara koyowa ne haka? Kin daina bani abinci kenan kike nufi ko me?.”

Jin yadda yayi maganar a fusace ba kamar yadda ya gama yi mata magana yanzu ba ya saka ta karyar da murya tace, “in na dafa baci kake ba shiyasa……”
“Shiyasa kika daina sabida bana ci? Saboda ke kike siyowa ai ko?. Shikenan Ameena kar kiyi in baki ba ita in ta shigo ai zata min zanci kuma, kar kuma ki fara yi min k’orafin bana cin abincin ki koda nan gaba, Kiyi kuka da kanki” yana fad’ar hakan ya bar wajan Zaytun na hannun sa.

“Uhummmmm! Innalillahi wa’inna ilahir raji’un. Allah ka kawo min mafita da d’auki a lamarina” ta fad’a hawaye na zubo mata ta share ta tashi kanta na ciwo sosai dan Kullum cikin ciwon kai take ta hau saman zuwa d’aki ta. Bata jima da shiga ba wayar ta ta fara k’ara ta duba ganin shine yake kiran ta ya saka ta d’auka kafin tayi magana yace, “Kizo ki d’auke ta” yana fad’a ya datse kiran ta lumshe ido ta bud’e.

Lokacin da yake fad’a mata baya so su dinga raba shimfid’a ne ya fad’o mata a rai, a lokacin da yake cewa duk runtsi duk wahala, duk fad’a duk gabar da zasu yi kar su raba wajan kwanciya kowa wani bazai kula wani ba. saurin kawar da tunanin tayi ta tafi zuwa saman nasa, a zaune ta ganshi Zaytun tana cinyar sa tayi bacci shi kum yana danna waya. Da sallama ta shiga ya d’ago ya kalle ta ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya amsa ba ta k’araso ta d’auki Zaytun din a jikin sa ta juya zata fita yace, “Baki ji ba.”
Chapter 1 · 0% Book details