Sashe 77
Love Circl Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💫❤Love cycle❤ (29)✨ Amoon ya wuce dakinsa ba tare daya kalli kowa dake cikin parlorn ba.. Yanda yake hadiyar zuciya a lokacin kamar wani mayunwacin zaki.. Yana shiga ya daki banko kofar da karfi yana nishi tare da cizgar lips dinsa.. "He's just hoping to see tomorrow dan yaga wane isashshen ne ze shigo cikin family din nan da sunan wanda ze auri Fannahr sa"... Ya runtse idanu yanajin yanda zuciyar sa ke wani irin bugawa.. Bude kofar akayi.. Ya daga jajayen idanun sa yana kallon sadeeq daya shigo.. Dauke kansa yayi ya cigaba da sauke ajiyar zuciya da karfi.. Kallo daya zaka masa kasan ransa yakai kololuwar baci .. Bude fridge sadeeq yayi ya dauki bottle water ya mikawa Amoon bayan ya bude... Karba Amoon yayi ya daga...ya shanye tass snn ya juya yana kallon sadeeq yace "inde har Fannah ta auri wani baniba, to mutuwa zanyi that's the end of me"... Sadeeq yace "stop saying that.. Inde Fannah har Fannah matarka ce wlh seka aure ta idan kau kaga baka aureta ba to ba matarka bace that's ur destiny".. Dan murmushi Amoon yayi wanda daga gani kasan he's boiling from inside yace "Abbakar bazaka gane ba Fannah is my hope she's my future".. Sadeeq yace "just keep praying and kayi hakuri nasan wnn duk kishi ne kesa wnn abun ko a yanayin condition dinka ai ka kwantar da hankalin ka..ni nasan sbd yanayin condition din yusrah suka matsa seka aureta sbd idan aka barta zata iya shiga wani hali tunda ba lafiya ta gama isarta ba.. Kuma kaga tunkan tasan kanta takesonka. And babu yanda za'ai a hana jiddah kuma tunda tun suna yara suke sonka".. Amoon yayi shiru bece komai ba amma yasan zuciyar sa bazata daukar ganin Fannah da wanin sa ba... Fannah kam daki ta shiga tasha kukan ta fuskar Amoon kawai take hangowa tasan bashi cikin yanayi me dadi.. Bayan tafiyar su sultan akayi kiran su fareeda.. Nan take ya fada masu duk hukuncin da suka yanke.. Abbu ya kalli fareeda yace "maganar sultan ki barta ga sageer nan inshaallahu nasan bazaki samu matsala dashi ba".. Gyada masa kai fareeda tayi gaban ta na faduwa.. Sageer din da bawani shiri suke dashi ba mutumin da yakeda mugun jin kai amma shine za'a aura mata.. Haka nan de kawai ta Amince zata aure sa amma zuciyar ta bnd bugawa babu abinda take.. Ita tana da mugun tsoro shiyasa ko Amoon bata shige masa... Yusrah kam farin ciki sosai jin Friday za'ayi baikon su da Amoon duk da harda jiddah Amma de tana farin ciki... Jiddah kam jikin ta yayi mugun mata sanyi.. Taga a yanayin da Amoon ya fito daki dazu hakama na Fannah hakanan kawai se jikin ta yayi sanyi... Chucu kam duk da tana farin ciki sede tausayin yayan nata da Fannah ya rufe hakan.. She wish ace itace yusrah da Jiddah data hakura yau kodan sbd farin cikin su da yanda suke son junan su... A ranar dayawa basuyi bacci ba cikin wadan da Abun ya shafa wasu farin ciki wasu kam kwana sukayi kuka irin su Fannah da fareeda.. Fareeda na ganin yanda sultan keta kiran ta da kuma tura messages.. yana bata hakuri da kuma rokonta akan dan Allah kartayi accepting sageer.. Babu amsar data basa.. Duk da tasan a lokacin can ita taja sultan ya barta amma dole itama ta share sa kamar yanda ya share ta wnn karon sbd fannah.. Kuma dukda tanasonsa dole tayi hakuri tunda Abbu ya hadata da sageer... Fannah kam taci kuka harta gode Allah chucu ce me lallashin ta... Amoon ya tura mata message amma bata duba ba bama tason dubawa sbd tanaso tabi umarnin iyayenta... Washe gari kamar yanda Abbu yace sageer yazo ya samu fareeda.. Itade ta gamajin abinda ya fada mata a matsayin wanda ke sonta ko daya bama tajin zata fara sonsa.. Sultan kau kamar zeyi hauka sharesa tayi ta nuna kamar ma bata san yanayi ba ... Can bayan la'asar Abbu yayi kiran Fannah... A hanyar ta ta zuwa ta hadu da Amoon dauke kai tayi zata wuce.. Yace "dama idan kika je kinuna beyi maki ba"... dan kallon sa tayi taga bama ita yake kallo ba ta dauke kai tayi wucewar ta.. Parlorn Abbu ta shiga ta same sa bayan ta gaisar dashi ya amsa ya danyi mata nasiha tare da fada mata ribar hakuri snn ya nuna mata parlon da yake ciki .. A hankali ta tashi ta shiga jikin ta duk a sanyaye tayi sallama ya amsa mata kanta kasa ta zauna.. Ta gaisar dashi ba tare data dago ba .. Ya amsa snn yace "khadeeja".. Dan dagowa tayi ta kallesa.. Shima matashi kamar su Amoon din duk wani abu daza'a soshi ya mallaka sede ina batajin zata iya son wani bayan Amoon duk maganganun da yake bama tajinsa.. Tade ji sunan sa Yusuf. Amma nan har ya gama surutun sa ba jinsa take ba.. itade seda yace ze tafi zuwa gobe ze dawo snn ta dago ta kallesa murmushi tayi snn tayi masa sallama.. Parlorn Abbu ta wuce ta yace "ya tafi mamana".. Ta gyada masa kai.. Yace "masha Allah ya kukayi dashi".. Tace "na amince Abbu".. Murmushi Abbu yayi "Allah ya maki Albarka" a sanyaye tace "Ameen".. Wnn karon bata iske Amoon ba se jiddah tare da farouq.. Babu wanda ta tankawa a cikin su ta shege daki sbd kukan dake cinta... Yusuf yazo ze shiga mota knn aka yi masa sallama ya juyo yana kallon Amoon da murmushi ya mika masa hannu suka gaisa... fuskar Amoon babu yabo ba fallasa yace "nasan neman aure kazo ko".. yusuf na murmushi yace "sure khadeeja".. Amoon ya dake gira trying hard be fito da bacin ransa ba yace "advisibly kar ka kara zuwa imda sunan wajen ta kazo cos tanada miji".. Dan kallo sa yusuf yayi snn yace "but ni ba'a fadamun tanada miji ba".. Amoon yace "for ur on good kar na kara ganin ka da matata".. Daga haka ya juya yabar Yusuf daya bisa da kallo.. Can kuma ya shiga motar sa... Fannah dake zaune jikin gado tana share yan hawayen ta ta daga ido ta dubi jiddah da farouq da suka shigo.. Dauke kai tayi ta cigaba da goge hawayen ta da sukaki tsaya mata... Jiddah ta zauna gefen ta farouq kuma ya tsaya jikin mirror yana kallon ta yace "jiddah is here to apologize".. Jiddah tace "kiyi hakuri for all what happened and still happening ina son yaya Amoon amma na hakura dashi because of you ke yake so bamu ba dan haka na hakura".. Ba tare da ta kalli jiddah ba tace "babu komai and maganar yaya Amoon kuma ni na hakura Abbu na hadani da wanda zan aura"... Jiddah ta dafa kafadar ta "Fannah nasan kina son Amoon and shima ke yake so.. Tunda nake bn tabajin yaya Amoon yace yanason wata ba se akanki nasan koda mun aure zuciyar sa na tare dake.. Ni ynx nayi wa yaya khaleefa magana and inshaallahu zuwa Friday zasu zo ayi mana baiko".. Fannah de batace komai ba sbd ita kade tasan yanda take ji... Mikewa jiddah tayi ganin Amoon fita sukayi farouq na bayan ta.. Duk da Fannah taji kamshin turaren sa Fannah bata dago ba.. Amoon ya karaso Yana kallon ta ganin yanda take kallon wani direction din yace "hope kin sallamesa".. Ba tare data kallesa ba tace "why will I do that bayan shine aka zabamun"..yace "aka zaba maki ai ba zabin kiba".. Ta juyo ta kallesa.. "Nima ynz zabi nane coz na riga na amince ma Abbu".. Amoon ya rinka kallon ta yace "look into my eyes and tell me kin amincema wani da aure bayan ni".. Kin yarda tayi ta kallesa.. Yace "khadeeja".. Fashe masa tayi da kuka "pls Aliyu let me ka kyale ni dan Allah na rokeka ka rabu dani".. Se kuma ta juya tana ta kuka sosai... Sosai ta basa tausayi amma yasan duk abinda take ji be kai rabin wanda yakeji ba ya fita damuwa..he wish ace ze iya yin kuka he wish yace ze iya rungume ta suyi kukan tare daganan su samawa juna solution. Juyawa yayi a hankali ya fita... Seda taji karan rufe kofa snn ta dago.. Se kuma ta juya taci gaba da kukan .. Dakin dad dinsa yaje.... Dad yasan maganar data kawo dan nasa shiyasa yayi saurin dakatar dashi.. "Aliyu kayi hakuri da hukuncin da Aka yanke maku kawai ni bazan iya yanke komai ba wnn umarnin Baffa ne ba namu ba"... Tashi Amoon yayi ya fita.. Dad ya bisa da kallo... Sultan ko duk yanda yaso ko haduwa ma yayi da fareeda taki yarda ko kiransa bata dauka.. Ya tura text na ban hakuri yafi a kirga.. Yaje wajen mom tayi masa kaca kaca.. Ta korosa daga yau zuwa gobe kade aka basa ya samo mata ko a dauki wata a hadasu kawai.. Shi wlh ynx har zuciyar sa yasan ya hakura da Fannah fareeda yake so.. Itama gashi ynx taki sauraren sa... ..... Tunda yusuf ya gama parking yaga Amoon zaune seda gaban sa ya fadi.. Amma ya dake.. Amoon ya bisa da kallo zuciyar sa na tafarfasa... Fannah ta tashi bayan taga message din yusuf cewa ya karaso.. Hijab kawai ta saka ta fita zuwa can inda yake.. Karasawa tayi a hankali tayi masa sallama.. Ya dago "welcome beautiful".. Dan murmushi kawai tayi.. Ta zauna ta gaisar dashi ya amsa.. Zeyi magana knn ya tsaya Yana kallon Amoon daya nufo wajen.. Fannah ta juya ita kanta ganin Amoon seda gaban ta ya fadi.. Amma ta dake.. Yusuf yace "who is he".. Fannah ta dan kakalo murmushi "my brother".. Shide Yusuf be yarda ba dan yanda yaga Amoon ya taho cike da tsananin kishi a idanun sa yasan ba brother dinta bane.. Amoon na karasowa ba tare da ya kalli yusuf ba idanun sa akan Fannah yace "Fannah leave".. Ta dake tace "why"... A dan tsawace yace "I say leave".. Yusuf ne yace "brother I think ba haka yakamata kayi ba besides hakan ma da kakeyi be dace ba".. Amoon ya dubesa da jajayen idanun sa yace "how dare you to tell me what to and what not to do I say how dare you"..