Sashe 26
Love Circl Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka amsa da "naam Abba" cike da mmki yanda ya ganesu... Ashe har haka suka damu dasu.. Duk sun ganesu babu wanda suka manta sunan sa... Ya mika masu hannu "come to ur Abba.." Da sauri suka karasa kusa dashi suna zauna kasa.. Ya shafa kansu.. Tare da musu barka da zuwa... Fannah wani dadi taji... Duk da taji be tambayi kowa cikin yan uwansa ba alamar har ynx yana fushi dasu knnn..... Fira suka rinka yi amma be tambayi kowa ba kawai sede firar aiki da ta karatu amma kallo daya zaka masu kasan yana cikin farin ciki..... Dinner ma tare sukayi da zasu tafi hanasu Tafiya yy yace su kwana tare suma su kwana gidan Abban su... Amma ya gargade su kada su kira masa kowa.. Daga karshe ma se karbe wayoyin su yy... Yace su sha fira kawai... Aikam sun dade suna fira kafin kowa ya tafi ya kwanta... ... Fannah se da tazo kwanciya snn ta tuna da maryam cewa gobe zata tafi.. Dan ma jirgin yamma ne... Se taji bata wani damu ba kamar da.. Dan tana ji a ranta ta kusa zuwa Nigeria... Snn tasa a ranta bazata fadawa maryam ba . Sede kawai ta ganta a Nigeria... Amah ne ya fado mata rai... Wani murmushi tayi tana kara rungume pillow she wish ace yana nan yaji wnn lvr.. Ta lumshe idanu a ranta tace "kilama a Nigeria zamu hadu"... Ta dan lumshe idanu kamar zatayi kuka.. Allah ne kade yasan sonda takewa wnn bawa.... Shine mutum na farko data fara so... Kuma bataji zata dena sonsa har karshen rayuwar ta".... Da wnn tunanin bacci me dadi ya dauketa.... Washe gari Fannah da kanta ta hada masu breakfast... Karfe 10 ta gama jera komai a dining.. Ta juyo tana kallon su sultan da suke zaune a parlor tace "hey brothers breakfast is ready kowa yazo ya cika tumbin sa"... Duk tasowa sukayi .. Sultan yace "weldone sistern mu"... Farouq yace "bari muji da dadi"... Dan hararar sa tayi... tace "se ka manta sunan ka"... Ya dage gira "reall.. " saukowar dady ce yasa yy shiru... Duk suka gaishe sa ya amsa masu da kulawa .. Fannah tayi serving kowa suka fara ci a natse... A hankali farouq ke danna wayar sa..... Ganin mahaifinsa online yasa yasa masa DM.. "Abie you knw what"... "what my son?".... Abie yayo masa reply... Ya sake tura masa... "Abie ina gidan brother din ka"... "Brother na kuma Farouq"... Vedio call ya kira mahaifinsa ya maida cameran back tare da saita daddy yanda abiensa ze gani da kyau idan ya dauka cikin hikima yy sa ba tare da sanin kowa ba... Alhaji Ibrahim na dauka idanun sa ya sauka akan kanin nasa wanda rabon sa dashi 19yrs knn .. Besan sanda ya mike ba.. Dan duk da an dauki shekaru sarai ya gane dan uwan nasa.... Ya zare glass din idanun sa.. domin ganin sa da kyau.. Sede kit yaji Farouq ya kashe wayar... Babu shiri ya kirasa ta nrml call ... Ganin haka yasa Farouq dauka ya saka a hands free... Muryar Abie ta karade parlorn.. "Hello Farouq me nake gani ina dan uwana hadani dashi yana ina"... Daddy ya daga kai yana kallon wayar zuciyar sa na masa wani irin rauni... Jin muryar babban wan nasa wacce rabon sa da ita shekara da shekaru... Farouq "ina Muhammad yake ka basa dan Allah kabani dan uwana inji muryar sa"... Tsam daddy ya mike jikin sa na wani irin rawa... "Bana son ganin kowa".... Daganan direct ya nufi kofar fita.. Seda yakai daidai kofa snn yace "banajin zan koma garesu... Sun gujeni a lokacin da nake bukatar su... Dan haka nima na barsu har abada kamar yanda suka bukata.. Ku yarana ne kuma ko da yaushe ina maku barka da zuwa nan gidan ku ne zaku iya zuwa a duk lokacin da kuka so but ni.. Bazan taba komawa wajen wadan da suka kyamaceni ba nagode da ziyara"... Daga haka ya fice.... Fannah ta fashe da kuka taje ta rumgume mummy "mummy kibasa hakuri dan Allah".. Shiru kawai mummy tayi amma bata iya tace komai ba.... Su fannah suna gani su farouq zasu fita.. Fannah tayi saurin shangabansu su.. Tace "au tafiya zakuyi ashe dama ba neman mu kuke da gske ba" sultan ya girgiza mata kai "no sister we're coming back"... Daga haka yaja hannun farouq suka fice.. Fannah na kallon su kamar wata shashasha... Tana gani sun fita ta fashe da kuka tare da zuwa ta rungume kanin ta.. Da take ji shine kade dan uwanta a duniya.... Kirane ya kara shigowa wayar farouq na kusn bakwai... Dagawa yy "hello abie".. "Farouq yaushe na zama tsaran wasan ka.. Ina Muhammad da nagani ta video call".... "Abie...... " nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fada masa.. *** ... Abie ya kashe wayar bayan yagamajin abinda farouq ke fada masa... Jiki a sanyaye ya dubi matar sa da ta mike tana son tabbatar da cewa Muhammad ya dawo... Tace "meya faru yana ina shi Muhammadun".. Ya dube ta "mamien yara Muhammad har ynx fushi yake damu"...mamie tace "yakamata kuyi wani abu tunda wnn damar ta samu kar mu bari ta subuce mna" ya gyada kai cikin gamsuwa kafin ya dauki waya yakira Ahmad dake America "hello Abie".. Abie yaji muryar diyar dan uwan nasa sumayya ta daga "Chucun abie"..."abie good morning" Abie ya saita muryar sa "morning chucu ina dad".. Mika masa wayar tayi.. Alhaji Ahmad ya amsa tare da sallama.. "Ko gaisuwar kirki basuyi ba ya fara sanar dashi dalilin kiran... . Alhaji Ahmad be san sanda ya mike ba zuciyar sa na masa wani irn rauni.. Jin abinda Muhammad din yafada ne yasa lokaci daya ya yanke shawarar ynx Idan ya samu flight din Nigeria ze taho zuwa gobe se suje London din snn yace a a fadawa Alh Aminu da Alh Rabiu.. Bayan nan kar a fadawa kowa dan basa so Baffa yasan da maganar har se komai ya dedeta.... " kafin azahar su Alh Aminu da Alh Rabiu duk sun san da maganar kuma suna cikin farin ciki Rabiu da yake sudan yaso ya yanke aikin da yake ya taho amma Abie yace ya bari zasuje. Haka ya hakura dan yasan duk da shine suke uwa daya uba daya da Muhammad yasan baze nunawa sauran yan uwan nasa kaunar sa ba.. Dan dama tuni shi Muhammad kowa yafi sonsa a gidan sbd shi Allah yayi sa da sauki da hakuri ba kamar sauran ba... Hajiya.. Maimuna ma da take Lagos danta sultan ya kirata ya fada mata... Dan haka itama tuni ta kira Abie kuma ya sanar mata da inshaallah gobe zasu je.... ** Fannah shiryawa tayi ta tafi wajen maryam.. Bata fada mata komai game da ganin family din nata ba.. Ita kuma maryam ta dauka duk dan zata tafi ne da yake duk in zata tafi haka suke barin ma hutu me tsayi irin wnn.. Haka de taita lallashin ta... Karshe ma fannah kuka ta fashewa maryam dashi... Abubuwa da yawa sun mata gana Amah gana Family dinta ga kuma maryam ma Zata tafi.... Da kyar maryam ta lallaba ta dan itama seda ta sakata kukan .... Fannah ta rakata har airport din snn ta juyo ta dawo gida.. Mummy ta iske a parlor tayi shiru.. Zuwa tayi ta kwanta saman cinyar mummy kafin tace "mummy pls do something"... Shiru mummy tayi bata san dalilin daddy nayin haka ba but tasan cike yake da son ganin yan uwansa ita ynx hankalin ta duk a tashe yake sbd bata san wane hali yake ba a ynx.... Tashi fannah tayi ta koma daki.. Tana zuwa ta ciro sakon da Amah ya barmata ta karanta.. Tana hawaye kafin a hankali ta furta I love you.. Pls come back to me"... Ranar gidan babu wanda yabi ta kan lunch har dinner ma seda mummy ta mata da gske snn tasakko kuma har lokacin daddy be dawo ba... Gaba daya hankalin su a tashe yake... Suna gamawa yana shigowa... Suka masa sannu da zuwa ya amsa ciki ciki snn ya haye Sama... Fannah kara fashewa da kuka tayi snn ra wuce dakin ta... A haka ranar suka kwana kowa da abunda yake damunsa a rai.. washe gari andade da gama breakfast amma babu wanda ya sakko yy har wajen 12... Da kyar mummy ta lallaba daddy yasakko snn ta kira fannah a waya... Har suka kusa gamawa fannah bata sakko ba.. Daddy ne na kansa ya dauki waya ya kirata... Tana dauka yace "I want to see in lessthan 2mnts" daga haka ya kashe wayar... Ai kau se gata dakaga idanun ta kasan tayi kuka.. Abubawa da yawa sun mata yawa to... A hankali ta zauna tare da gaisar da iyayen nata mummy ce kawai ta amsa amma daddy sede kallon ta yy ya basar... Har cikin har sa bayason yanda ya ganta... Kodaya bayason ganin ta a damuwa... Itace babban farin cikin sa a duniya shiyasa a duk lokacin da yaganta cikin damuwa zuciyar sa take karaya... Juya abincin kawai take har lokacin ta kasa kai ko tea bakin ta... Ganin abinda take ne yasa daddy fadin.. "Kar ki bari na gama break ba tare da kin cinye abinda ke gabanki ba you better behave ur self" gyada masa kai kawai tayi tana tura abincin tana hawaye.. Suna cikin haka ne sukaji an danna bell.. Daddy ya umurci maid dinsu akan ta bude... Tana budewa.. Farouq ya shigo da sallama cikin shiga hausawa wacce ta fito da anahin kyaunsa.. Sultan ma ya shigo cikin shiga irn ta Farouq sunyi matukar kyau da kagansu kaga kyawawan asali.... Da sauri fannah ta mike cike da farin cikin ganin yan uwan nata.. Sede kafin tayi step daya.. Idanun ta ya sauka akan wani kyakkawan dattijoh cikin shiga ta alfarma kamannin sa da daddyn ta sun bayyana haka kuma suna tsananin kama da Farouq... Wanda ya shigo daga bayan sa seda gabanta ya fadin ganin shima kamannin sa da daddy sun fito a fuzge kuwa da Dr. Amah dinta yake kama.. Next ma wani ne ya sake shigowa kammanin sa sak da daddy... Ai ba ita kade ba harta Daddy da mummy seda suka mike..... Gaba daya daddy jiyayi jijiyoyin