Sashe 40
Love Circl Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
dear yaya sultan ze kawo ni".. Fareeda ta langwabar da kai "promise" da sauri Fannah tace inshaallah... Koda fareeda ta fita seta koma baccin ta.. Se 11 ta tashi tayi wanka ta dauki atamfan ta da aka dinka mata ta saka ta iya saka kayan hausawa bata son sune sbd nauyi suke mata da kuma can England bawani saka su ake ba..kayan sunyi matukar yi mata kyau tadan yi ture kaga tsiya taga anayi.. Snn ta yafa mayafi.. Sosai tayi kyau kamar ka sace.. Breakfast batayi ba tayiwa mummy sallama ta tafi part din baffa.. Tayi dan sallama ta shiga parlourn sultan ne zaune yana breakfast jin kamshin turaren ta ya daga kai yana kallon ta seda yy da gske snn ya gane ita .. Wara idanu yy "wow lil sis are you" Murmushi tayi wanda ya kara fito da kyawunta yace "kinyi kyau" tayi kasa da kanta tana wasa da ring din da Amah ya bata.. Kafin tace "yaya inaso naje sch dinsu fareeda pls can we go together"... Cike da farin ciki tace "why not give me some minutes" daga haka ya shiga dakin sa. Ita kuma da wuce part din mama.. Bata wani dade a can ba ta tafi wajen umma dan sunfi dasawa kodon fareeda oho... " Suna gama yin parking wajen department dinsu fareeda wayan Fannah ta fara ringing duk suka kalli wayar a tare idanun sultan ya sauka akan best bro.. Wani abu yaji ya soki zuciyar sa.. Ita kam fannah murmushi tayi ta dauki wayar tare da fadin "yayana"... Tuni sultan ya gane wa take nufi kodaga ganin yanda suke waya kade ya isa ya nuna tsananin shakuwar dake tsakanin su.. Yasan kuwa duk lokacin daya nuna yana sonta baze sha wahala ba zata karbe sa.... Tace "yaya Farouq bana gida fa muna sch din su farida".. Yace "iye keda wa kikaje".. Karban wayan sultan yy ya kara a kunne "hey mr muna tare . ita kade kk kira knn bnda mu"... Farouq yace "kai bros yne".. "No babu wani bros Dubai tayi dadi ka manta dani Fannah kade kasani".. Dariya Farouq yy "kai bazaka gane ba ina Fannah bani ita... Sultan yace "nooo sede anjima" daga haka ya kashe wayar ya rike a hannun sa ya dubi Fannah muje.. Dan tura baki tayi tace "shine ka kashe".. Budewa yy ya fita itama ta bude ta fita tayi wani rau da idanu.. Ta zagayo suka jera... Yace "see kinyi kyau a haka".. Tsayawa tayi kamar zatayi kuka.. Ya ware idanu "oh sbd na hanaki waya da best bro shine kk fushi.. Sbd kin fi sonsa a kaina"... Da sauri tace "lahhh aa fa" yana Hararan ta yace "uhm to yane" murmushi tayi ta fara tafiya.... Tace "duka ina sonku"... Girgiza kai yy yana murmushi itama murmushin tayi tana dariya... Tunda sukayi parking fareeda ta gansu.. Yanda suka fito suka jera suna tafiya da maganar da suke ne kamar wasu masoya.... Slow ta farayi tana tafiya zuwa inda suke.. Jikin ta duk a sanyaye dan gani take kamar sultan son Fannah yake.. Sede bata fatan hakan... Tana karasowa inda suke ta rungume Fannah.. Tana kallon yanda atamfar ta mata wani kyau sosai.. Sultan yy ta kallon ta ganin yanda duk tayi wani irin yace "you look somehow.. Anything wrong".. Ta langwabar da ka "yaya duk nagaji wlh daga zuwa yunwa nake ji"..tayi masa karya... Yace "lets go and get something".. Ta gyada masa kai suka juya zuwa mota.. Fannah tace "yaya my phone".. Yace "am not giving you".. Tace kila fa ze kira".. Yace "to ya kira mana".. Ta dubi fareeda.. "Kinga wai don yaya Farouq ya kira shine ya amsa fa"... Sosai gaban fareeda ya fadi.. "Why will he collect her phone dan Farouq ya kira inde babu wani abu"... yace "to fareeda ta kwatar maki.".. Fareeda tayi yake "yaya ai kasan munfi ka yawa ko" yy dariya "kuma sarkin yawa yafi sarkin karfi ko".. Duk dariya sukayi... Basu tsaya cikin sch dinba waje suka je wani babban eatry ya siya masu abinci ... Yanda hankalin sa gaba daya yake kam fannah yasa hankalin fareeda kara tashi.. Tama kasa natsuwa taci abinci... Taji duk ma ya fita ranta.. Haka de taita daurewa tana yake har suka dawo sch suka aje ta.. Sukuma suka shiga cikin gari.. Sosai Fannah ta sake da sultan . Wanda hakan ya masa dadi... Kusan fareeda ta dawo basu dawo ba seta kasa natsuwa jidda da hafsat sukazo amma ta kasa natsuwa cikin su suyi lvri koda suka tambayeta lpy se cewa tayi kanta ke ciwo..... ... Satin su Fannah biyu amma kai kace sunyi shekara da family din nasu sun sake cikin su suna komai tare baka taba cewa daga baya suka saba...Fannah batada wata damuwa seta Aliyu da batajin akwai ranar de zebar zuciyar ta... Yayinda kusanci me tsananin ya shiga tsakanin su da sultan.. Sosai ta sake dashi har ynx farouq be dawo ba amma koda yaushe suna tare a waya hakan kau Ba karamin kusanci yake kara masu ba.. Wanda shine kesa hankalin sultan yana tashi.. Tabbas ya samu kusanci da Fannah amma yasan har ynx kusancin dake tsakanin Fannah da farouq ba kadan bane... Hakan yasa duk lokacin da farouq ya kira seya amsa sun gaisa.. Kuma yanayin hakanne dan ya kular da farouq yasan cewa yana sonta kuma suna tare idan ma shi farouq din yana sonta... Aikam kuma yaci riba domin sosai abin ke kaisa bango baya nunawa ne kawai amma har ransa yakejin haushin abinda sultan yake masa.. Kamar yanda sultan ke bukatar yasan yana sonta ya fahimta kuma ya fahimci da gangan yake masa sbd inde har akwai son Fannah a ransa zeji haushi.. Kuma yaji yes yaji.. Because he loves Fannah since from day one.. Shi idan sultan na sonta ba damuwar sa bane.. Abinda yake masa da ganganne is getting him.. Idan yana sonta why can't him try and capture her heart ba tare daya kuntata masa ba.. Amma inde hakane "sultan this just the beginning mucigaba da wasan"... Farouq ya fada yana duban kansa ta cikin mirror din dakin hotel din da yake a dubai.... Fareeda kam tun tana yaudarar kanta cewa sultan ba son Fannah yake ba harta dena dan ynx duk wani alamu na soyayyar fannah ta gani wajen sultan.. Sosai hakan ke damun ta tanade kokarin dannewa ne kawai .... Ko ynx haka duk suna part din baffa tunda safe jidda ce keta kiran Amoon amma yaki yin pinking kamar zatayi kuka ta dubi su Fannah tace "yaki dauka tunda na zo Abuja sau biyu ya dauki wayana... Fannah ta kalle ta cike da tausaya wa fareeda kam tabe baki tayi...ita duk son da take ma sultan bazata taba zubda class dinta a kansa ba komi halin da zata shiga akansa zata iya jurewa... Ta dubi Fannah tace "muje idan ynx zaki wuce"... Fannah ta tashi suka fita jiddah kam bama tasu take ba... Suna fitowa compound din sultan ya karaso inda suke... Yana kallon Fannah "shine har zaki tafi baki nemeni ba ko". Ta langwabar da kai... "I thought baka nan".. Fareeda ta gaisar dashi ya amsa yana kallon ta.. Snn ya dubi Fannah "and you should have check on me ai" tace "srry bro" yy Murmushi.. Fareeda de batace komai ba bnd kirjin ta dake bugawa babu abinda take.. Suna fitowa bakin gate din gidan baffa mota ya gama parking.. Seda ya gama kare masu kallo ta cikin motar.. Kafin ya bude ya fito.. Duk suka bisa da kallon mamaki.. Yana sanye cikin manyan kayan da suka matukar yi masa kyau.. Kyawunsa ya kara fitowa.. Ware idanu fannah tayi....