← Book details Love Circl Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 78

Sashe 32

Love Circl Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💫❤Love cycle❤ (10)✨ *Not edited* Daddy yace "yaya I missed you so much kun gujeni without knowing halin da zan shiga" Abie ya dago dan uwan nasa yana share masa hawaye "we are srry lil bro muma munshiga halin rashin ka for so many years".. Daddy ya share hawayen sa yace "ina baffa na" Alh. Ahmad yy murmushi.. "Baffan ka yafi kowa damuwa da rashin ka tsawon 19yrs da be ganka ba yanacikin tsanin damuwa ynx ma besan mun taho ba da tare dashi zamu taho"...cike da farinki yace "ynx baffa yana son ganina Ina mamana ina umma da sauran yan uwana".. Daga ganin yanda yake magana kasan yana cikin farinciki da kewa Alh. Aminu yace "eyee is that how you miss us shine ka barmu".. Dan langwabar da kai daddy yy kamar yanda ya saba masu kasancewar sa karamin su yace "I don't think zaku sake kewa ta sbd yanda har nayi 4yrs na koma amma baku bukatar gani na.. I thought sona ya fita a ranku.. I thought kun barni har abada bazaku sake yafemun ba"..yafada a raunane Alh. Ahmad yace "common bro we loves you kasani kawai de lokacin idanmu ya rufe ganin yanda ran baffa ya bace but kafimu gskiya".. Abie ya shafa kansa yace "se bayan ka tafi muka fahimci cewa kafi mu gsky liman ya samu baffa yamasa nashiha ya nuna masa abinda kayi daidai ne.. baffa ya shiga damuwa tun yana saka ran zaka dawo har ya cire but kullum yana maka Adduar gamawa da duniya lpy.. Kullum kaine mafarkin sa ... Kuma be taba cire ran zaka dawo ba duk kyautar dayamana har da kai".. Daddy da farin ciki ya ishesa se juyawa yy ina matarsa da yaran sa suke.. "Halimatu. Mamana kunga yan uwana sun dawo hisam zo".. Duk tahowa sukayi kowa idonsa na zubar da hawaye... Abie na kallon fannah yace "masha Allah yarinya ta ta girma".. Murmushi tayi kanta kasa.. Alh Aminu yace "come to ur parents we really miss you".. Suka rungume hisam ita kuma suka shafa kanta.. Daddy is so excited he can't believe ranar nan zata zo... He can't wait yaga mahaifinsa sa ji yake kamar yy tsalle ya gansa a Nigeria yaga mammansa da sauran yan uwansa.... Bayan komai ya lafa aka gabatar masu da abinci sun roki kafarar mummy da shi kanshi daddyn har fannah da take jin kunyar su sun roki tata kafarar kuma duk sun yafe mata.. Daddy ya shige cikin yan uwansa se fira suke yana tambayar yan uwansa da yaransa.. Aka kira haj. Maimuna da Alh. Rabiu bade a kira su sa'adatu ba sbd suna son surprising dinsu amma sauran ya gaisa dasu a waya kuma yaji kalar farin cikin da suke.. Se daddy yaji duk be kyauta ba dama ya koma da be zauna cikin kadeci na shekaru ba.. Fannah kau se kallon daddyn take ganin yanda ya sake da yan uwansa kamar bashi ba dan is hardly ya sake da jama'a inhar basu ba.. Ynx ko koyanayin maganar sa ya chanza se yar shagwaba yake masu dade kagani kasan dama shine karamin su kuma dan gata... Fannah kasa sakewa taci abinci tayi sbd yanda idanuwan sultan da Farouq ke yawo akanta.. Kara daga ido tayi suka hada idanu da Farouq.. Ta ware masa idanu shi kuma ya sakar mata murmushi tare da kashe mata ido daya.. Ta dauke kai tana murmushi.. Suka hada ido da Alh. Ahmad.. Da sauri tayi kasa da kai dan hakanan taji tanaji matsanaiciyar kunyar sa fiye da kowa a wajen... Wayar Alh. Ahmad ne tayi kara yana dubawa ya kalli daddy yace "danka ne kekira" "me sunan baffa".. Daddy ya fada yana murmushi... Alh. Ahmad ya dauki wayar bayan sun danyi magana kadan ya mikawa daddy suka gaisa snn mummy.. Daga nan ta mikawa Alh. Ahmad se yace "ga kanwar ka ku gaisa toh"... Shru yy kafin can yace "ohk to Allah ya kaimu ya bada sa'a".... Ya kashe yana kallon fannah "wai dan uwan naki busy yake but idan ya zama free ze kira ku gaisa"... Gyada kai fannah tayi kawai a ranta tace "wato shine kade baze gaisa da ita ba bayan kowa dokin yake abasa ita su gaisa yaji yanda ta girma.. Amma shi busy yake...." ... A ranar su abie sun dade kafin suce yaushe ze koma.. Daddy ji yayi kamar ya bisu but yace "gobe inshaallah kasata zata amshi bakuncina nida iyalina"... fannah couldn't find it but smile... Jin cewa gobe zataje Nigeria abun kamar a mafarki.. Kowa se kallon juna suke suna murmushi sun kasa magana.. Alh. Aminu ne yy karfin halin fadin "lallai gobe munada manyan baki lallai gobe ilahirin family din Radda suna cike da farin cikin dawowar dan uwansu bayan tsawon shekaru".. Duk murmushi sukayi Farouq yace "su wata za'a bar kauye aje birni".. Fannah ta tsuke fuska tana hararan Farouq sultan yace "Allah yasa karta mana kauyanci dukda nasan ma wnn aje take".... Abie yace "rabu dasu daughter ne ai sune yan kauye keke birni bakiga idan zasuzo bude ido nan suke zuwa ba".... A hakade sukai ta wasa da dariya daddy ya zagaya dasu cikin gidan sa ya fada masa nasarori da arzikin da ya samu bayan barinsa gida.. Sun jinjina masa kuma sun saka masa albarka... Gabadaya tare suka rakasu airport fannah kamar ta bisu haka take ji dan gani take kwana dayan nan kamar shekara daya ne.. Ganin yanda jikin ta yy sanyi yada sultan kamo hannun ta yace "lil sis are you ohk?"...kamar zatayi kuka tace "I just can't wait jinake kamar na biku"... Yy murmushi "see you inde Nigeria ce seta isheki"... Itama murmushi tayi ya kashe mata idanu.. "Keep smiling cutie you look more beautiful".. Kasa tayi da kanta ganin yanda ya zuba mata manyan idanu.... Kiran su da aka farayi ne yasa bama fannah kade ba hatta daddy seda jikinsa yy sanyi dan gani yake kamar baze kara ganin su ba ya rungume su.. Fannah ta kalli Farouq dake kallon ta ya girgiza mata kai alamar kartayi kuka.. Itama seta gyada masa kai tana masa murmushi.. Ya kashe mata idanu... Yanda yayi din seya mata kama da Amah... Suka daga masu hannu suna gani har suka shige snn suka juyo... Fannah ta dubi daddy dake driving tace "daddy ynx Nigeria zamu koma".. Yace "sure daughter gobe zakiga baffa ba da mamana da umma and other of ur relatives" farin ciki kamar me.... Suna komawa gida suka fara shirye shirye daddy yace ba wasu kaya dayawa zasu dauka ba idan sunje duk zasu siya nacan Nigeria.. Ranar suka gyara gidan komai aka ajesa a inda ya dace wanda ze lalace suka bayar dashi daddy ya masu booking flight.. Kafin dare sun gama shirya komai .... Ranar ma duk basuyi wani baccin kirki ba daddy hankalin sa gaba daya ya koma kan iyayen sa.. He just can't wait ya gansa tare da mahaifinsa mamansa da sauran kannensa... Fannah ma murna da farinciki da dauki ya hanata bacci.. Ta rungume pillow tana tsara yanda zatayi surprising maryam.. She wish ace ta hadu da Amah acan tasan zeyi mmki..A haka de bacci ya dauke ta... Washe gari jirgin su ya daga zuwa Nigeria.. Fannah tana cike da doki daddy kau da mummy tunanin su daya ne babu wanda ya manta last tym da suka hau jirgin Nigeria shekara 19 knn lokacin fannah na jaririya.. Gaban mummy se faduwa yake musamman ma da tasan itace silar komai fahimtar hakan da daddy yy ne yasa ya kamo hannun ta.. Ta kalle sa ya girgiza mata kai kafin yace "inshaallah komai yaxo karshe".. Ta gyada masa kai.. Ya juya ga Fannah da tayi bacci with smiling face... Yace "kinga diyarmu bacci take cikin farin ciki.. Wancan tym din da muka baro da ita bata san komai ba.. But now she's happy"... Mummyn ta kalli diyar tata cike daso da kauna tana murmushi.. "Inason yarana yaya iyayen mu sukaji da suka rasa mu"... Daddy ya kwantar da ita a shoulder dinsa yana dan buda bayan ta..... *⭐⭐NIGERIA⭐⭐⭐* Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja... A hankali fannah ta lumshe idanu tana shakar iskar kasar tata wani irin farin ciki yana lullubeta she can't believe itace tayi stepping in a Nigeria.. Iskar yammacin tana dan kadawa a hankali taitabin jama'ar wajen da kallo inda take ganin kamar mafarki take... daga inda sultan yake yana hango su tunda suka fito sunyi wani kyau da kagansu kasan suna cikin hutu .. Ya sauke idanun sa akan fannah.. Tayi matukar yi masa kyau acikin arebian dressing dinna ta seta fito sak balarabia kyawunta is unique ta hada komai sede abinda ba'a rasa ba.. Fannah a bangaren kyau babu macen da bazata iya gogawa da ita.. Gashi kallo daya zaka mata ta shiga ranka... Sultan yadan lumshe idanu yana kara jin son fannah acikin ransa wanda tun randa ya fara ganin ta yakejin sonta... A hankali ya bude motar ya fita yakarasa inda suke... Hisam ne ya fara ganin sa yaje ya rumgumesa... Duk su daddy suka juya gare su... Ya gaisar da su dady snn ya dubi Fannah tana murmushi ta gaisar dashi... Yace "eyee muje gida"... Daga haka suka shiga.... .. Fannah ta zage se kallon hanya take kamar wata bakauya ko ina yana mata kyau wai ynx nan zataga yan uwanta.. Sultan ya kalle ta.. Yace "kalle kallen fa ko tafi UK".. Murmushi kawai tayi dan tasan babuma hadi... Kusan 26mnts suka iso cikin unguwar cikin silent unguwar tasu dake dauke da manya gine gine daka gani kasan anguwar ta manya ce .. Batayi mmki ganin inda sultan ya tsaya yana hon ba domin kau tasan arzikin kakan nasu ya wuce haka... Tasan daddy ta nada arziki iya arziki amma be kama kafan babansa ba... Daddy kau tunda ya suka shigo yake tabin ko ina da kallo ganin yanda aka kara kawata kasar tasa da kuma irin cigaban da suka samu... Lumshe idanu yy jin sun karaso kofar gate din gidan nasu har ynx suna nan inda suke but kamai ya canza kamar anrushe gidan an sake gina nazamani kuma an kara gine gine... Babban wajene me dauke da manyan duplexes na zamani ga shuke shuke da suka kara ma wajen kyau... Daka gani kasan naira ta zauna..
Chapter 32 · 0% Book details