← Book details Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 6 OF 59

Sashe 6

Life Partner Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ranar Friday da yamma Rafi'a na zaune a dakinta tana tilawa Abdul ya shigo rike da phone dinsa ya na "Mummy want to talk to u" ta kar6a wayar ta kara a kunne hade da sallama, Mummy ta ce "I don't really know the essence of ur phone Fatima, why is it always off? Haka saurayinkin yake kiranki yaji ko yaushe a kashe" Abdul ya sheke da dariya harda kwanciya, turo baki kawai tayi kafin ta ce "Ni Islamiyya zan tafi ai mun gaisa" Mummy ta ce "Kika kashemin waya wallahi sai ranki ya 6aci, daga tambaya zaki taramin mutane wani wai islamiyya, Allah yasa Madina zaki taho" Qur'an din ta ajiye gefen bed side drawer ta mike tsaye, Mummy ta ce "To dama next week zan dawo, nace bari na fada da wuri dan ranar dana sauka dake zan wuce gidana" kallan wayar kawai Rafi'ah take with confusion ta ce "I will just go and see u Mummy, Abba ya hanani barin gida" Mummy taja tsaki ta ce "Sai na gani ai, na ta6a jin yadda ake hana diya taje wajen yayar uwarta, shekara nawa ina naci ya bani ke baiban ba na hakura, sai dan kwana uku zuwa hudun da zakimin zai hana, da anyi magana yace ba lafiya kike dashi ba, ai yanzu kam we have to drop a very big thank to God, Zainab tacemin bai fiye tashi ba yanzu ko?" daga mata kai tayi kamar tana gabanta sannnan ta mikawa Abdul wayarsa ta ce "To Allah ya kawoki lpy" Mummy ta ce "Alright sai anjima" daga haka tayi hanging wayar.
Dai dai lokacin Ummi ta bude kofar dakin, ta dinga kallan Rafi'ah dako uniform din boko bata cire ba, gashi har ana shirin islamiyya, Ummi ta ce "Why haven't u remove ur uniform Fatima?" A hankali ta ce"I slept off bayan na dawo, yanzu zanyi shirin islamiyya" Ummi ta ce"Hope u are not sick?" Girgiza mata kai tayi ta ce "Noo, stress ya sani bacci Ummi" ta ce "Ohk, Abba yana hanya fa" tayi wani tsalle hade da kara ta ce "Are u serious Ummi?" Ta daga mata kai ta ce "Sure, ya kiraki bai sameki ba" gaba daya she can't hide her happiness, ta rungume Ummi cike da shagwa6a ta ce "Almost 2 months fa banga Abba ba Ummi, amma dai muma 2 months zai mana ko?" Ummi ta zameta a jikinta ta ce "I don't know" Rafi'ah ta zauna gefen gado ta ce "Is he alone?" Ummi ta dalla mata harara ta ce "U can call him and ask" turo baki tayi ta tashi ta fara cire uniform dinta ta ce "Ai nasan waccen matar saita biyoshi" Ummi dai bata kula taba ta kalli Abdul dake kwance kan gadon Rafi'ah ta ce "Kai ba zaka je islamiyyan bane?" Ya mike yana kallanta ya ce "Zanje Ummi" ta ce "Oya do fast is after 4 now" daga haka ta fice a dakin yabi bayanta shima. Har Abdul ya shiya ya dinga jiran Rafi'ah a mota bata fito ba, ya kalli Mustapha dake kallan film din india a wayarsa ya ce "Let me check on her" daga haka ya koma cikin gida, a parlor ya samu Ummi tana tasa turaren wuta, ta juyo tana kallansa ta ce "Baku tafi bane, karfe 4 da rabi fa" ya tsaya yana kallanta ya ce "Anty isn't out fa Ummi" ta ajiye kwaskon hannunta ta nufi stairs ta ce "The only thing Rafi'ah can do fast is to sleep, in dai bacci ne tana kwanciya bata kara minti daya" tana bude kofar dakinta ta sameta a gaban mirror tana ta fama da trouser dinta ta kasa daure tazuge, dama mostly Ummi ke daura mata ko Abdul, itama ta koya amma yau gaba daya ta rasa kan abin ta masa kulli yafi hudu, dago kanta tayi tana kallan Ummi kamar zatai kuka ta ce "Help me pls Ummi, i can't do it, tin dazu yaki zama, my neck is even aching" Ummi taja tsaki ta karasa gabanta ta durkusa tana gyara mata ta ce "Keep shut now before i give u a dirty slap, when was the last time na koya maki daura abin nan" kamar zata fashe da kuka ta ce "Ummi ni kasawa nayi, I'm just trying my best but na kasa daurawa" mikewa Ummi tayi bayan ta gama daura mata ta ce "Wear your hijab and come out now" ta dauka zulelen hijab dinta har kasa ta saka sannan ta lankaya side bag dinta da qur'an ke ciki ta biyo bayan Ummi, bayan sun sauko ta bata light hug ta ce "Pls Ummi kiyi ma Abba hug dina kafin na dawo na mishi wani" Ummi ta dalla mata harara ta wuce kitchen, murmushi tayi ta fita a parlo'n ta wuce parking lot, bayan ta shiga motar Abdul ma ya shiga, Mustapha ya juyo yana kallanta ya ce "Wani film din india nake kalla Hajiya Rafi'ah, yarinyar yadda kikasan ke, komai naki take, ita fa har takalmin makaranta mahaifiyarta take saka mata" dalla masa harara Rafi'ah tayi ta shiga turo baki, hakan yasa yayi shiru yaci gaba da tukinsa, dan yasan yau babu me ta6a Rafi'ah tinda Abba yake hanya, in kwa aka ta6a ta har abinda aka mata tin tafiyarsa saita juye masa, shima Abdul shiru yayi ganin irin 6ata ran da tayi, bayan few minutes ta ce"Ai duk kaika fada mishi" Abdul ya zaro ido ya ce "I'm not the one sis, have u forgotten he said... " toshe kunnuwanta biyu tayi, cikin tsawa ta ce "I don't want to hear anything pls" shiru yayi ya juya kansa gefe, yasan by this time kam sunyi late kuma ana duka, shi kuwa tinda ta masa shouting bazai kar6a mata duka ba yau.
Mustapha na parking suka fita yaja mota ya barsu a wajen, Abdul ya nufi gate din ya tura, zaro ido tayi ganin students a compound ana ta dukan lattee, Abdul ya danyi murmushi ya shige ciki tabi bayansa, duk gaba daya ta gama tsorata sai numfashi take saukewa daki daki, ga idanuwanta da suka fito alaman tsoro, bayan an yiwa kowa Abdul ya mika hannunsa aka masa guda hudu ya wuce, Rafi'ah da duk ta rude ta ce "Pls don't leave me Abdul, pls help me kaji dan Allah" ko ya juyo ya kalleta ya shige ciki abinsa, Malamin ya daure fuska yana kallanta ya ce "Kawo hannunki" ta ce "Ai Abbana yazo ya fadawa Malam Ahmad kar ana dukana, bani da lafiya wallahi" wani kallan rashin mutunci ya mata ya ce "Ai kowa ma ba lafiya ce dashi ba, ki kawo hannunki na dakeki ki wuce aji an fara kar6an hadda" ta dukunkune one side ta ce "Pls let me go, i promise not to come late again, dan Allah kamin hakuri" Tinkarota malamin yayi ta fasa kara jikinta ya hau rawa, har idanta ya cika da kwalla ta dago tana kallansa ta ce "For God sake na roke ka". Muryar wani malami sukaji yana cewa "Wannan ai mahaifinta yazo tin shigarsu islamiyya ya sami headmaster, ai ba'a dukanta Malam Umar" ko kallansa Malam Umar baiyi ba ya ce "Su sauran 'ya'yan da aka daka ba mutane bane, dan meyasa zaku ware ta ace baza a ta6a taba, ni ba ruwana da ubanta koshi waye dukanta zanyi wallahi" Malam Sadeeq ya ce "Ba batun 'yar wani bace Malam, indan haka za'a bi ai rabi da quarter ba dukansu za'ai ba, ina maka bayani ne akan akwai dalilin da yasa ba'a dukanta" ganin ko kallansa baiyi ba yasa ya wuce ya barsu a wajen, sai lokacin hawayen idanta suka gangaro kasa, ya daka mata tsawa ya ce "Bani hannunki kona miki a jiki ki wuce" girgiza masa kai ta hau yi ta saita kofar gate ta fita a dari da sittin.
Cikin saurin ya taka birki yana fadin innalillahi, itama gaba daya ta tsoruta jira kawai take taji an kade ta, jin shiru yasa ta bude hijabinta a hankali tana kallan gabanta, sai kuma ta sunkuyar da kai ta kasa magana, Yusuf ya fito a motar sanye da lab court, daga gani yanzu ya tashi a clinic, ya dinga kallan Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "U again" ta dago da sauri jin muryarsa, suna hada ido ta saukar da kanta kasa, ya matso kusa da ita ya ce "U haven't forgot the other incident right?" Ta girgiza kai a hankali ta ce"It isn't my fault that time, shine yazo ya bigeni without me knowing and baiyi horn ba" ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Yau fa?" ya karashe magana yana shafa beard dinsa, ta kara sunkuyar da kai ta ce "I'm sorry it wasn't intentional, and dukana za'ai" Yusuf ya dan zaro ido ya ce "Who?" Ta ce "Malam Umar" ya kalli gate din islmiyyar sannan ya kalleta ya ce "Why?" Kamar zata fashe da kuka ta ce "Is because i'm late" ya ce "And why did u came late?" Sai lokacin ta dago kanta tana kallansa ta ce "Na kasa daura tazugen wandona shin... " zaro ido tayi da sauri taja baya, sai a lokacin ta lura saam bai dace ta fada masa haka ba, ya danne dariyar dake cinsa ya ce "Then what?" Ta fara kame kame ta ce "Noo i slept off.... Yes i slept and... And i woke up very late..Very late i swear"
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_7~8_
Chapter 6 · 0% Book details